JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Oum Hairan
[7/19, 9:16 AM] Oum Hairan: JH012 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki

Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566

Wata irin zabura tayi ta miqe a hargitse tana waige² kamar ance ta daga kanta sama ta hango Baffa’am dinta tseye shima ya zubanta ido fuskarsa babu alamun haske ko annuri mamaki ya cikata a tace “yaushe ya dawo?” Baita samu amsar abinda take nema ba Kareem yasha gabanta ya tsugunna yace “malaminki yana neman taimakonki Aminatu don Allah kada ki wofintar dani nasan har yanzu babu kowa cikin zuciyarki shiyasa nayi gaggawa wajen furta miki abinda Raina ya qunsa”
Sake kallon inda Rasheed yake tsaye tayi har yanzu ita yake kallo ta janye hannunta daga riqon da Kareem yayi mata ta nufi step din upstairs din da sauri zuciyarta na bugawa da qarfi kafin ta qarasa taga ya juya ya shige dakinsa ya danno qofar da qarfi daidai lkcn ta qarasa ta shiga qwanqwasa qofar tana cewa “yau nafi kowacce ya saa Baffa’am ashe idan mutum Yana mafarki gani yakayi wayyoh dadi baffana ya dawo gareni, please budemin na kwashi tabarraki kasamin albarka My lovely Dad……”
Yana tsaye jikin qofar yanajinta qirjinsa na harbawa da qarfin dashi kansa baisan dalilinsa ba so yake ya bude mata ya kasa saboda wani tuquqi da zuciyarsa takeyi masa yayi danasanin fitowa a daidai wannan lkcn duk da baisan meye Kareem ya fada mata ba Amma yanayinsu ya nuna wani sashine me muhimmaci sukeson wanzarwa.

Zama yayi saman gadonsa jikinsa Yana wata irin rawa a hankali ya furzar da iska me zafi yace “meye yake fada miki Meenah?” Miqewa yayi zunbur ya bude qofar har ta hqr ta juya jikinta a sanyaye abinka da me qoramar hawaye ta fara fitar da qwallah taji ya bude qofar ta juya da sauri ta nufesa a guje ya bude mata hannu me Kuma ta tuna saitayi turus a gabansa idanunsu na sarqe cikin na juna hakanan taji sautin bugun zuciyarta yana nunkuwa ta kama hannunsa ta tsugunna saita rushe da kuka abinda ya qara tashin hankalinsa yasa hannu biyu ya dagota yasa yatsansa Yana share mata hawayen har zuwa lkcn zuciyarsa tafasa takeyi burinsa kawai yaji meye Kareem yake fada mata harta bashi attention haka data kasa jin kiransa ta kasa ganinsa?
A kasalce ya hadata da jikinsa qirjinta ya tokare nasa yaja wata ajiyar zuciya me qarfi yanajin wata nutsuwa na saukar masa yace “miss ur My Meenah” dagowa tayi hawaye nabin kuncinta tayi murmushi ta sake saqale bayansa tace “shine Saida ks batamin farin cikina Baffa’am kasan irin wahalar da nasha kafin na saba da rashinka kuwa meye yasa ka ja zuciyata a qasa harna fara tunanin ko na bataran haskena?”
Inda kalamanta suka nufa daban inda yakaisu daban janyeta yayi ya zauna a qasa itama ta zauna yace “meye Kareem yake fada miki me dadi haka da har ya dauke miki hankali kusan 30 minutes Ina tsaye akanku Amma baku sani ba?” Rufe fuskarta tayi tana dariya sokuwar tace “nifa Baffa’am bansan meye yake nufi ba wai Yana sona kuma son aure hakams Saleem yace da Ya’isha nikam bana kulasu ma cewa nakeyi suje su sami Baffa’am dina namasan bazakayimin aure ba ko………”

Wani ihu yayi daya ja hankalin mutanen dake falon qasan gabadaya ya miqe ya shaqeta jikinsa na tsuma ya kasa mgn sai wani turiri da bakinsa yakeyi haqoransa suna haduwa da gudu Mom ta nufo saman ta riqeshi tana cewa “na shiga uku ni Aishatu Abdulrasheed meye Kuma yarinyar nan tayi maka daga dawowarka ko hutawa bakayi ba….” Da ihu yace “So Momy sonta fah yace yanayi Kuma har take iya fadamin wai yanasonta Nawa take Mom irin riqon amanar taku kenan har damar soyayya kuka bata injiwa? Waye yabaku wannan damar?” Daqyar suka bambare Juhud daga hannunsa yayi watsi da ita baijira cewar kowa ba ya fada dakinsa ya doko qofar da qarfi hada kansa da bango duk wata qofa ta gashi a jikinsa ta miqe idanunsa ya kada yayi jawur zuciyarsa kuwa kamar ta faso qirjinsa haka yakeji.

Mom ce ta dagota idanunta gabadaya sunyo waje saboda ba shaqar cigaba da rayuwa yayi mata ba so yayi ya aikata lahira sauka sukayi Addah Abulle ta karbeta hannun Mom tajata dakinta ta zaunar da ita Ya’isha ta matso tace “kay yau Ina ganin masifa towaishi Big Cele meye yake nufi dan ance anasonki ya nemi aikaki barzahu?” Iska Addah Abulle ta furzar tace “Lamarin Rasheed wuyar sha’ani garesa ni yaran nan sun fara gwaramin kai wlh yanzun Kareem ya fita harda hawayensa wai in taimakeshi ta yarda tanasonsa kafin ya tafi karatu ayi komai a gama a hada aurensu da Rasheed sai tayi karatunta acan shine nace yaje ya samu Mai Martaba ya fada masa shikuma wannan kurman yazo Yana neman kasheta kawai don ance anasonta ko ubanme yake nufi oho”
Shiruce ta ratsa na dan lkc Amrah ta miqe tace “Allah ya kyauta saiki tashi kisa uniform dinki mu fita ai” tunda suka shigo tana kwance jikin Addah tana aikin kuka daqyar Addah ta rarrasheta ta miqe tasa uniform din suka fita driver yajasu suka tafi mkrnta duk abinda akeyi akan idon Muntaz yayi qwafa ya fito ya shiga cikin gidan sukayi clear da Kareem suka harari juna kowa ya wucce.

Tunda suka fito har sukaje mkrntar kuka takeyi har suka isa kai tsaye office din principal suka nufa suka gaisheta tare da gabatar mata da Aminah Haroona Moddibo a matsayin sabuwar dalibar da aka dade dayi mata bayaninta, tambayoyi tayi mata ta bata Amsa duk da batada nutsuwa Madam Khairat ta Yaba da qwazon yarinyar a mstsayinta na wacce batayi karatu ba.
Bayan ta gama mata Interview din tabasu izinin su tafi domin Mai Martaba yace kada a raba masa yaya abarsu tare, hakance ta faru har aka tashi batada walwala, Muntaz ne yazo daukarsu baiga fuska a gurinta ba dole yasha jinin jikinsa maimakon ya tafi dasu gda wani park yakaisu waisu huta tukunna kafin lkcn islamiyya, Ya’isha da Amrah suka tafi harkokinsu itakuma ta nemi guri ta zauna har yanzu idan ta tuna ta batawa Baffa’am dinta rai sai taji hawaye ya zubo mata.
Ji tayi an kama hannunta ta dago tana sauke ajiyar zuciya ganin Muntaz da wani fure a hannunsa yasata zubansa ido ya miqo mata yace “yau ranar masoya ce ta duniya shiyasa na zabeta matsayin ranar da zan fara fayyace miki sirrin zuciyata, kafin hakan ki karbi wannan furen ki shaqi qamshinsa nasan zaiyi miki dadi” hannu tasa ta karbi furen tayi jifa dashi tace “na shiga ukuna ni Aminatuh don Allah Ya Muntaz kar kace kanasona wlh Baffa’am kasheni zaiyi dazun saboda Ya Kareem yace yanasona daqyar aka kwaceni a hannunsa….” Batayi aune ba taji ya banqarata baya ya hade bakinsa da nata numfashinta ya dauke ta rintse idanunta ta hada qarfinta ta tureshi daqyar ta miqe tana rarraba idanu yayi murmushi Yana shafa sumarsa yace “nop Ni ba irin baqauyiyar soyayyar nan zamuyi ba sai kinso kosu Ya’isha zasusan halin da muke ciki kawai zan baki damane mu rinqa ware guri muna haduwa har zuwa lkcn da Mai Martaba zaibamu damar yin aure Kinga saimu bayyana kanmu matsayin masoya lkcn babu abinda Big Cele ya isa yayi, to waima da kike wani tsoronsa shidin ubanki ne naga shima aure yake Shirin yi kekuma saiya hanaki jin dadinki akan me?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button