JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Wani gwauron numfashi Meenah ta saki tace “idan har kace saika Bari ta gane da kanta to kuwa da jan aiki a gabanka Baffa’am idan Irina ce me qarancin fasaha wajen gane abubuwa hannunka Mai sanda bazai wadatar wajen fallasa mata sirrin zuciyarka ba misali kamar ni duk da har yanzun ban karbi tayin qaunar Ya Kareem ba, Ganin nidin bame ganewa bace yasa ya fito ya sanar dani abinda ke ransa ko banza nasan zai samu sauqi game da ciwon dake cin zuciya balle ma ni……”
Dagowa tayi ta dubesa tsoro ya kamata ganin yanda lkc daya ya hargitse yanayinsa ya canza daga na walwala zuwa matsananciyar damuwa, da sauri ta miqe tace “kayi hqr don Allah Baffa’am kaine kace duk wani abu dake damuna na rinqa sanar dakai kafin na sanar da kowa……” “Shut-up Meenah!” Abinda ya fada da qaraji kenan ya miqe jikinsa na rawa zuciyarsa na motsawa da qarfin gaske maqwallatonsa kamar zai faso maqogwaransa tsabar bala’in dake cinsa suka fara zagaya dakin cikin tashin hankali ganin guri ya qure matane ta zame a qasa kawai ta saki kuka me sauti tace.
“Na shiga uku ni Aminatuh Baffa’am meye laifina ne don naso Ya Kareem wlh ko zaka kasheni saina fada maka inasonsa saboda yanada cikar Kamala da nagartar da tayi qarancin a samarin zamanin nan inasonsa saboda zuciyata tana fadamin shine ya dace da maraici na Baffa’am Ya Kareem baitaba sani dole ba baitaba hanani dole ba saidai akan aya da hadisin ma’aiki (S.A.W) baitaba takuramin akan nasoshi ba saidai ya roqi alfarmata duk da kasancewar banida alfarmar shine yake da ita domin a cikin da’irar arziqinsu nake rayuwa, Ya Kareem baitaba nuna yanason jikina ba hasali ma yaqi yakeyi da duk abinda zai tarwatsa mutumcina Kuma, Ya Kareem ya fadamin cewa Allah Yana maraba da bayinsa da sukayi soyayya dominsa wannan dalilin yasa naji inasonsa domin Allah Kuma zan rayu das……”

Bata iya qarasa kalamin nata ba saboda wani gigitaccen mari daya sanyata kifawa ya nunata da yatsa zuciyarsa na tuquqi yanason yayi mgn Amma harshensa ya sarqe a hankali ya janye ya koma ya zauna yana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji’un” ya maimata ta takai sau goma kafin yaji nutsuwa ta fara saukar masa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur kamar garwashi bakinsa da jikinsa har yanzu rawa yakeyi yace “kina sonsa ko Meenah?” Dagowa tayi idanunta shabe² da hawaye yace “bakiyi qarya ba duk gdannan babu wanda ya tara wadannan suffofin da kika lissafa sai Kareem nima shaida ne saboda haka ya cancanci kisoshi tabbas Amma Kuma yanzu ya zakiyi da wanda ya daukoki tun baki cika mutum ba yajaki jikinsa ya mayar dake mutum ya bata darensa da ranarsa dominki ya Hana kansa farin ciki sai yaganki cikin farin ciki yake shiga damuwa da damuwarki koda kuwa bakwa tare motsinki ya zama nasa lfyrki tasa ciwonki nasa Aminah ya zakiyi dashi wanne halacci zakiyi masa da zaiji a ransa kin saka masa da kwatankwacin tausayinsa da qaunarsa gareki?”

Tunda ya fara mgnr ta kafesa da idanunta da yake tsiyayar da hawayen tashin hankali tasowa yayi ya matso gabanta ya miqar da ita yace “idan ya kasance kin kasa saka wancan Alkhairin da abu mafi daraja wato qaunar da wannan mutumin yake nema a gurinki to tabbas ke ba yar halak bace domin dan halak shine yake jiran gabar saka Alkhairi da komansa koda kuwa gurin bai cancanci sakayya ba shidai burinsa yaji a ransa babu bashi tsakaninsa da wannan mutumin”
Sakinta yayi ya juya zai shiga bathroom har ya bude ya juyo yayi mata murmushi yace “kije kiyi tunani akan kalamai na” a mugum kasalce ta bude qofar ta fito ta nufi cikin gdan zuciyarta na kai kawo akan kalamansa tana shiga dakinsu ta zube a bakin qofar tana mayar da numfashi Amrah dake fitowa daga bathroom taja ta tsaya sake da baki ganin yanda ta cure jikinta tanata rera kuka takaici yasa Ya’isha miqewa tace “dallah malama ke baki rabo da kukane meye Kuma akayi miki” dagowa tayi ta kwantar da kanta jikin Amrah tace “nikam Ina ganin rayuwa Amrah don Allah meye wadannan kalaman suke nufi……”
Zayyane musu komai tayi ta qarashe da cewa “bansan meye yasa qwaqwalwata bata gane abubuwa ba” numfashi Amrah da Ya’isha suka saki tare Amrah tace “kan ubancan lallai akwai qura a gdannan Juhud bafa wani abu Big Cele yake nufi ba kece yakeso kece Aminan da yake baki lbr ke kadai ce me wannan siffar daya suffanta” Ya’isha ce tayi murmushi tace “ke saiyau kika fahimta ai dake da Aminah dukkanku kallonku nakeyi Amma wlh batun yanzu ba na fahimci Big Cele son Juhud yakeyi tsabar miskilanci ne da girman kai ya hanashi bayyanawa yake wani bada fadi da hura hanci kamar kyankyaso aikin banza na dade da gano damuwarsa kekam ta bakin naki kina ganin rayuwa ga Mai Martaba yayima Ya Kareem alqawarin aurenki” cikin mutuwar jiki ta dago tace “nikam ya zanyi wlh da gaske bantaba daukar wannan gundumemen lamarin zai fadomin ba banyi masa muhalli a bangarena ba bantabajin Baffa’am zaice yanasona ba kai bama abinda yake nufi ba kenan babu abinda zaiyi dani”

Dariya sukayi dukkansu ta zubansu idanu Amrah tace “waima to shi ya gani wlh yarinya tun wuri ki takansa birki inba hakaba zakisha wahala Big Cele bashida mutumci gashi da ganinsa zaiyi wuta babban tashin hankalin ma mgnr aurensa da Zulaihat tayi mugun nisa harma fah ankai kudin tambaya sa rana kawai zaayi anasa rana Kuma raqashewa zamuyi Kinga kenan bakida gurbi kawai batankin gomanki zaiyi dayanki bata gyaru ba”
Tagaji dajin wadannan kalaman hakanne yasata miqewa ta shiga bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta fito taji ana kiran magrib ta dauki dabino ta tauna ta fita ta dauko ruwa tana dawowa Amrah ta miqa mata waya ta Amsa ganin number Kareem ta Kara a kunnenta tace “nasha ruwa lfy Habiby kaifa?” Murmushi yayi yace “yanda kikasha Luv ya exams?” Kwanciya tayi tana lumshe ido tace “inajin dadin exams din da taimakonka” hirarsu sukaci gaba dayi tama manta da batun Shan ruwa saida yace “kije kisha ruwanki zan kiraki anjima” ta aje wayar ta tayar da sallah tayi buda bakin.

Tun daga wannan ranar salon rayuwar gdan ta canza musamman tsakanin Juhud da Rasheed duk inda tasan zasu hadu gujewa gurin takeyi saboda ita har cikin zuciyarta bataji a ranta zata iya soyayya dashi ba bayan haka ma sannu a hankali Kareem ya gama siye zuciyarta da salon qaunarsa me tsayawa a rai da wuyar gogewa kullum idan sunyi waya kalmarsa daya itace don Allah Aminah ki kulamin da kanki nayi miki tanadin kaina na tsare kaina tsayin shekaru burina ya kasance a halali na na fara shuka inason gonata tayi kyakkyawan yadon da yabanyarta zata burge kowa idan amfanin ya nuna ya isa moro ya morawa duniya baki daya Aminah samawa yayana uwa ta qwarai shine abinda na dade Ina addu’a nasani bazan taba danasani ba idan kin kasance mata a gurina zaki bani farin cikin da zanyi alfahari dake a duniyata da lahirata”
Idan ya fada mata haka Yana kashenta jiki matuqa takanji kamar ya daureta da jijiyarta ne duk saitaji wani shauqin qaunarsa Yana qara mamaye ruhinta wannan dalilin yasa ta qara qaimi wajen tsare kanta tunda me bata kariyar bayanan gashi ya Daura mata nauyi Mai girma na amanarkai.

Kwanci tashi lkc ya rinqa tafiya cike da matsaltsalu Rasheed mugun miskili da baa gane matsalarsa Amma yanzu kusan kowa ya fahimci yanada damuwa gashi da baqin zurfin ciki ya kasa furtawa kowa damuwarsa saidai yaje Garden yayi tagumi ko ya tusa waya a gaba yayita kallo. Ranar da sukayi Candy suka hada qwarya²r party a gidan sarautar Juhud batada qawaye su Ya’isha ne suka gayyato samarinsu da qawayensu Mai Martaba shine ya daure gindin partyn harda dauko musu Dan Hausa yazo don qarawa abin armashi qarfe hudu suka fara caskalewa samarinsu duk sunzo itace kadai saurayinta baizo ba baya qasar ma Amma yayi mata fatan Alkhairi sun dauki wanka na tashin hankali sunyi kyau na bam mamaki dama dukkansu ba baya ba wajen kyau Amma sukansu Saida suka sallamawa Juhud tayi kyau kamar wata amarya suka fito daga gdan ana take musu baya suka fara hotuna anyi mata hoto yafi kati dari da shiga daban² ta karbi wayar Ya’isha ta zagaya baya ta Kira layin Ya Kareem bugu daya ya daga tayi ajiyar zuciya tace “rayuwata tana cike da kewar masoyi banajin komai yana tafiyar min daidai” dariya yayi yace “kinajin abinda nakeji kuwa Aminah nifa inajin kamar zanyiwa Mai Martaba mgn ne zanzo hutun azumi kawai a hada bikinmu dana Big Cele ayi a bani ke mu taho nan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button