JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

A wannan rana akayi komai aka gama Batare da sanin Aminatu ba kwanaki uku tsakani Aka shirya masu kayansu da tarin shanayenta garke guda suka dunguma suka nufi Chad tafiya yau kwana anan tashi anan haka Mahaifina da yar’uwarsa da mijinta sukeyinta har Suka isa Chad. Sarkin yankin na wannan lkc amini ne ga Baffa Doda hakan yasa saida aka fara saukar amarya Aminatu a gidansa akayi biki sannan ta tare a rugarsu.
Lkcn da akayi wannan aure Aminatu bata wucce 14 ba hakan yasa sukayita wasan buya da Wandu har tsayin shekaru inda zama yaqi dadi tsakanin Aminatu da Gwaggo Lami, ita Gwaggo Lami batada shanu saita tatsi na mijinsu sannan takai kasuwa ta siyar ta samu na cefane ita kuma Aminatu yawan shanunta yasa bata fita tallen nono yarane da ita da suke dauka mata suke saidawa su kawo mata kudin.

Wannan abu yana ciwa Gwaggo Lami tuwo aqwarya gashi ta rasa yanda zatayi da Aminatu ga wata kulawa da Maddibo Wandu ke bawa Aminatu ta musamman kinsan abinka da lamarin maza idan suka auro yarinya wannan abu ya taru ya hadu ya haifarwa da Aminatu baqin a gabadaya rugar domin kowa Bayan Lami yakebi sai ya kasance shikuma Moddibo ya koma bayan Aminatu, kwatsam ana haka sai aminatu ta fara rashin lafiya ana shawara ce basir ne ashe cikine da Aminatu a haka dai ba tare da kowa ya ankara ba har cikin Aminatu ya isa haihuwa cikin dare ciwo ya turnuketa gashi Maddibo bayanan a lkcn ya tafi Nigeria sawo wasu shanaye.
Gwaggo Lami tanajin Aminatu tanata nishin ciwo amma taqi ko leqota saida Buba ya fito fitsari yajiyo ya nufi dakin da sauri ya isheta cikin mawuyacin hali a lkcn ta gama jigata kan da ya sawo kai amma yaqi qarasa fitowa aikuwa ya ruga da gudu yaje ya taso wata dattijuwa me suna Suwai suka taho tare kafin kace wannan dakin Aminatu ya cika da mutane amma ko qeyar Gwaggo Lami Cikin ikon Allah ana kiran Assalatu aka samu Aka ciro yaron daqyar Amma Aminatu batasan wake akanta ba gashi jini yaqi tsayawa Suwai tayi iyakar qoqarinta zamani bana asibiti ba amma ina saida ubangiji yayi ikonsa Aminatu bata ko kalli fuskar danta ba Allah ya karbi rayuwarta………

Mutuwar Aminatu ta girgiza duk wani mutum dake rayuwa a wannan ruga hakana aka tashi Manzo ya tafi Senegal ya sanarwa da iyayenta suka taso suka taho tare, tabbas Baffa Dodah ya tausayawa Moddibo matuqa da irin halin dimuwar daya riskeshi a ciki daqyar da qarfin Addu’a ya dawo daidai amma duk da haka daya kalli Jaririn da Aminatu ta tafi tabar masa sai ya kama hawaye kwana sittin da haihuwar jaririn aka rada masa Suna Haruna su Baffa Doda sunso tafiya da Haruna amma Moddibo yaqi yasa musu kuka yana roqonsu idan sun barshi zaike dauke masa kewar Aminatu.
Badon ransu naso ba suka tafi sukabar masa wannan jariri hakanan Wannan yaro yaci gaba da rayuwa tun yana tsumman goyo cikin rashin kulawa da qyara indai kinga anyiwa Haro wanka to Dattijuwa Suwai ce ta daukeshi a qarshe ma dole Maddibo barmata shi yayi itake kula dashi da komansa duk da cewa kwana Saba’in da rasuwar Aminatu Gwaggo Lami ta haihu hakan baisa taji tausayin maraici ta bawa wannan yaro nono ba watsin da tayi da wannan jariri yasa shikuma Maddibo ya dauki qaunar duniya ya dora masa komai ya samo na Haro ne Buba dake yarone me hankali kuma ya dan fara tasawa bai damuwa da wannan fifikon hasali ma tausayin Haro yakeji inda Bangel ya taso da qiyayyar haro shima Rubado daya tashi qarami da wannan aqida da uwarsu ta koya musu ya tashi Haro ba mutunne me hayaniya ba wannan tasa ko fita sukayi kiwo sai su kamashi su zaneshi da zarar sunga Buba ya kauce haka zai dawo gda yanata kuka Suwai da Moddibo suyita rarrashinsa.

Rayuwa tayita tafiya a haka har suka tasa sukakai munzalin girma Al’adarmu ta fulani yaro yana kaiwa sha takwas akeyi masa aure suyita tsalle tsallensu da matarsa har hankali ya iso musu su rungumi junansu wannan ce ta faru da Buba da Bangel buba yanada Sha tara bangel yanada Sha bakwai akayi musu aure Buba aka aura masa Jumme shikuma Bangel Asubi Jumme mace ce me kawaici da hqr itakam Asubi irin mijinta ce sai ya kasance Haro ya tare a gdan Buba komansu tare sukeyi ko shawara buba zaiyi baya shawara da yan uwansa da suke ciki daya saidai Haro saboda nutsuwarsa tasa tunanin manya yakeyi.
Rayuwar ta farayi mawa Haro dadi ya saki jiki da Jumme sosai duk abinda ya samo daga Jumme sai Suwai lkcn da shekarunsu suka kai ne aka daura masu aure Lariya itace matar da aka bawa Rubado shikuma Haro aka aura masa ni nima kamar yanda aka dauko Aminatu daga Senegal haka nima aka daukoni aka kawoni jumme ce tayi murna da zuwana ita da Suwai sune suka karbenu hannu biyu surukarmu kam ko kallo ban isheta ba mijina kuma dan’uwana dan qanwar mahaifina Haro ya qaunace ya nunamin kulawa dayake dama ba qarama sosai aka kawoni banyi wannan bambadancin da amare sukeyi ba muka zauna lafiya da mijina a hakanne Jumme ta Haihu haihuwar farko ta haifi Abdullahi wanda kuke kira da Hammah Audi shekaru biyu kuma Asubi ta haifi Rubado basa jana nima bana shiga cikinsu daga asubi har lariya Jumme ce kawai muke mutunci matuqa ana haka na samu cikina na farko nasha wahala sosai da yakai haihuwa Na haifi namiji Umaru ya fara girma sosai yakai kusan shekara uku ya kama qyanda wannan qyanda bata barshi ba saida ta tafi dashi munji mutuwar yaron sosai, bayan rasuwarsa ne harin barayin shanu ya addabi Lardin Wandu babu shiri Moddibo ya debo halwarsa muka dungumo Niger daga niger muka tsallako Nigeria muka samu matsugunni a Wannan guri da ya zama sabuwar Wandunmu”

Bamu jima da dawowa ba ciwon Ajali ya kama Moddibo ansha jinya sosai a lkcn da ajalinsa ya rigaya ne yasa aka kira masa yayansa yayi musu nasiha akan zumunci sannan ne ya ware wani kaso me yawa a cikin shanunsa yace wadannan na gadon mahaifiyarsa ne Aminatu daya rinqa kula masa dasu sune sukayi yawa haka, nanfah Bangel da Rubado suka kalli juna sukayi qwafa suka tashi suka fice daga dakin bayan fitarsu ne yake sanar dashi cewa akwai wasu shanun da ya bayar aka tafi dasu kudu kiwo da Buba da Haro ne sukaci gaba da jinyar mahaifinsu har kwana ya qare ya tafi yabar baya da qura qurar da itane kema kikazo kika tadda burbushinta.
Maitar da suke iqirari ta fara ne daga lkcn da nake haihuwa yarana suna mutuwa Asubi ce ta fara cewa wai ni nake cinye kayana saida na haifi yara takwas duk suna mutuwa sannan ne Allah ya bamu ke kika tsaya wai ashe duk yaran dana rinqa haifa maza suna mutuwa Ubayenku ne suka sanya hannu kawai saboda tunanin idan Haro ya mutu yanada da Namiji bazasu samu komai ba kedin ma sunso hallakaki Allah yaqi basu dama kika rayu da tsangwamarsu saboda kyawun da ubangiji yayi miki tun kina qanqanuwa dumurmur dake kamar kazar gidan gona saurin girmanki yafi komai bawa mutane mamaki Hasiya da Adama da Baraka duk sa’anninki ne amma duk kinfisu girma ko tallan nono muka tafi kafin akulasu an kulaki sau dari wannan tasa uwayensu sukejin hasaadar hakan akwai wani furuci da Gwaggo Lami tayi kafin mutuwarta watarana mun dawo daga tallen Nono wani Alhajin birni yabaki kyautar Yar dolin wasa (yar tsana) kinzo gda kuka fara fada da yan uwanki akanta har kika fasawa Baraka baki, ina daki ta kamaki ta zaneki sannan tace indai su baraka jininta ne to saita lalataki sai kinyi abin kunya a rayuwarki ko tana raye ko bata raye, badai kyaune yasa kowa yake nannan dake ba to kyawun saiya zame miki fitinar da zata addabi rayuwarki………….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button