JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Dukkannin kalaman Amrah babu Wanda ya daki zuciyar Juhud kamar Wanda tace Allah ne ya taimakesu Basu dauki Kara da kiyashi ba maita ai bala’i ce…..” Kashe wayar tayi cikin dimuwa tayi tagumi itadai tana ganin jarabawa Wai ya akayi ta zama mayya ne? Tana tsaka da tunanin nan Kiran Mom ya shigo ta daga a sanyaye cikin rawar murya tace “Mom…. Momy Ina yini” zuciya Mom taja tace “me Amrah tace miki?” Saita muryarta tayi cikin kuka tace “babu komai Mom” shiru Mom tayi sannan ta kashe wayarta ta miqe ta shige daki ta fada gado ta rushe da kuka yau ce Rana ta farko data fara jin shauqi da tunanin Ina zata Sami wani dazai zame mata abokin shawara dazai bata mafita cikin matsalarta maita? Maita?
Ta maimata yakai sau goma sannan ta iya miqewa ta shiga bathroom tayi wanka tayi magrib ta dauki qur’ani tana karantawa har akayi Isha tayi ta haye gado zazzabin dare ya aurenta ga kadaici hakanan tayita juyi da missing din Baffa’am dinta bacci ya fara daukarta taji wayarsa ta dauko ta gyara kwanciyarta ta Kara wayar a kunnenta tace “tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci zuciya biyu makusantan juna” numfashi ya sauke yace “Same to ur my Meenah meye ya hanaki bacci 11:40pm” kasa tayi da muryanta tace “kewa da tunanin mijina gami da missing lallausar fatarsa” dariya abin yabashi yace.
“Au haba dama kina jina a zuciyarki haka”

Murmushi tayi ta shafa saman kanta tace “komai na duniya hawa yake Yana sauka nikam sonka baitaba sauka a zuciyata ba Baffa’am tunda ya riga ya hauhawa don Allah ka riqemin amanar kanka kaji” qaramar ajiyar zuciya yayi yace “bakida matsala matata am dama mom ce tace tanason ki koma Daura a fara shirye shiryen biki dake Wai harda bikinmu zaa hada ayi” abinne ya bata dariya tace “biki Kuma Baffa’am nikam na yafe nawa su Bari su hada dana suna….” Duk da baa gabanta yakeba Saida ya zabura ya miqe yace “suna Meenah mun samu qaruwa be?” Jikinta ne yayi sanyi tace “hakane Baffa’am kwana hudu da lkcn period dina ya wucce……” Wani ihu ya saki Hadi da kabbara yace “wayyoh dadi Meenah shine baki fadamin ba na fara tanadi me zaki haifamin mace me kama dake ko?” Rufe idonta tayi tana share hawaye me hade da murmushi yace “amma kamar murnarki batakai ba my Meenah meye damuwar ne ko har yanzu fushinne?”
Girgiza kai tayi yace “talk me Mana” aa tace tare da cewa “bacci nakeji Baffa’am” da murnarsa yace “aikuwa zan fadawa Mom tabarki kada hayaniya ta damarmin ke ki huta kinji rayuwata” qit ya kashe wayar baa dauki 10 minutes ba saiga Kiran Mom tace mata “yayimin kwatancen gidanku gobe zanzo na daukoki gara ki dawo nan gidan ki zauna a bangarensa da zamanki anan Babu kowa bakisan kowa ba ga lalurar ciki Allah ya inganta ya rabaku lfy kinji me sunan yaya” a kunyace ta amsa suka Dan taba hira suka aje layin tana ajewa Kiran Ya’isha ya shigo tace mata “ke wlh banza ce daga zubar da wancan sai kika bude abu kika Kuma karbar wani nifa wlh banyi miki sha’awar haihuwa yanzu” shiru tayiwa Ya’isha jin hakan yasa ta gane yan iskan na kusa bazata kulata ba ta gimtse wayarta washegari kuwa 12:00pm a KD tayiwa mom da Muntaz tunda suka shigo yake binta da kallo yana hadiyar yawu a ransa yace “wow! Manyan kaya wannan guy chege ne yasan takan dadi dubi yanda wannan babyn take qara hauhawa abin kamar…..” Mom ce ta katse masa tunanin da cewa ai saika tashi ka Debi kayan mu tafi salmanu”

Zungi² ya miqe yabisu Mom na gaba Juhud na binta shikuma Yana qarewa halittar bayan Juhud kallo har suka isa mota ita da mom ne a baya shike driving har Daura suna tsayawa motar Mai Martaba tana tsayawa ya fito Mom ce tace da Juhud “kije ki gaisheshi” da faduwar gaba ta nufeshi ta rusuna ta kwashi gaisuwa Babu wata alama ta bacin rai ko damuwa ya Amsa mata tare da cewa “Meenah kawai saiji mukayi kinbi Wanda ya kawoki” da sauri tayi qasa da kanta saboda fitowar Kareem a part dinsa da yanda ya zubanta ido.
Tsayawa yayi cak Yana kallonta ta miqe tabi bayan Mom data nufi part din Rasheed tana cewa “wlh sakarcin Rasheed yawa gareshi Mai Martaba yabarta ita kadai a gda ga kadaici ga laulayi shine nace gara a dawo da ita nan kada dukan yayi mata yawa” tana tafe take mgnr suka gifta Kareem dake tsaye kamar dashe cikin sanyin yanayi tace “sannu Ya Kareem ya jikinka?” Wani yawu ya hadiye me daci ya juya yabar gurin gabadaya sai taji Babu dadi hakanan dai tabi Mom suka shiga abin mamaki bayine keta gyaran ɓarrayin fita mom tayi tace “bari na turo miki yan uwanki su tayaki shirya kayan”

Gdy tayi ta nufi ƙofar shiga dakin shima kamar falon an canza komai taja numfashi ta kulle qofar ta fada wanka ta fito daidai lkcn taji muryar Ya’isha ta bude mata suka rungume juna tace “wayyoh aure dadi gsky Big Cele Yana ban ruwa ke Kinga yanda kike wani glowing hajiyata fadamin meye sirrin 2 months kacal kamar kin shekara ana miki bayin ruwa” harararta tayi tace “kefa yar iskace meye Kuma bayin ruwa ana zamne qalau an fada miki Kuma kowa ma dan iskanne irinku ni zikiri kawai muke da karatun qur’ani da shaikh Baffa’am dina tunda ya saceni” dariya suka sheqe da ita Ya’isha tace “shegiya aifa dama Mana shiyasa naganki da sabon ciki ashe a ruwa ya baki kika kurba” gumtse dariya tayi tana cewa “hmmm yarinya kina wasa da mazan fama komansu na baiwa ne wato idan My Baff na bada darasi ji nakeyi kamar babu wani sauran gwani a duniya ke Bari fah kiji Allah Baffana akwai iya tsinko fure nakusa nayiwa kaina asar…..”
Shigowar jakadiya ne yasasu gimtsewa ta rusuna cikin ladabi tace “Allah ya taimakeki Mai Martaba ne yake kiran taron gaggawa a gidannan yace maza kizo kema tunda Allah ya dawo dake” Saida taji wata faduwar gaba ta dai dake tace “ok muna tafe” kallon Ya’isha tayi tace “meye ya janyo taron?” Miqewa Ya’isha tayi tace “akwai matsala ne kinsan fah Mai Martaba yasa Yaya Salman da Yaya Arman duk sun dawo da matansu gdannan wannan dalilin yasa Mom ta matsa kema ki dawo to tunda ya sauko ya amincewa dawowarki aketa tuka rigima da wadannan matan biyu Hajiya Bilki mahaifiyar su Aunty Zulaihat tana zugasu ita da Addah wai karsu yarda a kawo musu mayya tazo duk ta lashe musu kurwar yara a banza da mazan Basu daukar abinda muhimmaci Amma suma naga yanzu kamar maganganun sun fara tasiri ke harfa cewa sukayi wai kece kika lashe su Zulaihat da Ado driver saboda qudurinki na auren Big Cele”

Jikin Juhud Bari yakeyi dajin wannan sabon bala’in data fara karo dashi a wannan sabuwar rayuwa tata bata gama yanke abinyi ba Amrah ta shigo bakinta dauke da “la’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin” Saida ta tofa kusurwa hudu sannan tace “saqo daga Mai Martaba yace ku kadai ake jira” badon Juhud taso ba ta sanya hijjab dinta suka fito Ya’isha na qarfafa mata gwiwa suka Isa meeting hall din gdan kowa ya zubawa Juhud idanu harda Kareem ta sunkuyar da kanta tana neman gurin zama Mom ta riqo hannunta ta zaunar da ita kusa da Aliya matar ya Arman aikuwa tayi zunbur ta miqe tana qunquni itadai Juhud zama tayi Mai Martaba yayi gyaran murya ya fara bude taron da addu’a yace.
“Banso Kiran taro a daidai wannan lkcn ba so wata yar jumurda ce tasa dole na kiraku musamman akanki Aminatuh alal haqiqa a baya an zauna zaman gsky da rashin sani so yanzu abubuwa sun fasu Wanda mukayi qoqarin ganin mun kare zuri’a daga darsa zargi ko kokwanto Amma abin ya faskara wannan dalilin yasa na yanke shawarar kiranku nidai nasan iyakar zamanmu dake na shekara uku baki taba cutar da kowa ba duk da cewa akwai maganganun da naji suna yawo a bakin mata bamu daukesu seriously ba wannan tasa na Kira domin roqonki domin shi wannan abu a boye yake idan har da gaske hakanne mu bazamu qiki ba tunda mijinki yanasonki Amma kiyiwa Allah kici gaba da riqe kanki kada ki gwada Mana wannan mugum abu idan Kuma sharri ne to Allah ya saka miki sannan mgn ta qarshe banason qyara ko tsangwama a tsakanin ahlina wannan abu itama ba ita ta dorawa kanta ba gadar mata dashi akayi sannan alamu sun nuna batama da qarfi a jikinta Ina fatan kowa ya fahimta…..”
Tunda Mai Martaba ya fara mgnr ta rushe da wani kuka me gigita zuciyar me sauraro tana girgiza kai bakinta Yana rawa Mom ta riqota da sauri jikinta tana shafa bayanta cikin kuka tace “Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Allahumma ajirni fih musibati wlh tallahi billahil lazi la’ilaha illahuwa niba mayya bace sharrine kawai ku yarda dani nikam meye nayiwa rayuwa ne me nayiwa su Baffa Ribado suke bina har gidan aurena da wannan mugum sharrin meyesa kakata ta mutu da baqin cikin sharrin maita Innatu ta harta mutu tana maimata min basuda wata alaqa da maita kyaune yaja musu da hassada ake kiransu mayu nima Kuma saita tsallako kaina wayyoh Allah Baffa wayyoh Innatu wayyoh mijina don Allah ka dawo ka fada musu niba mayyah bace…..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button