JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Oum Hairan
[8/6, 10:48 AM] Oum Hairan: 0029 A gdan Ya’isha suka shantake sunata fira Basu suka baro gdanba sai gefin magrib suna shiga gdan gaban Juhud ya fadi batare da tasan dalili ba suka nufi parlourn da sallamarsu a tsaitsaye suka tarar da Addah Abulle da Fadila Juhud na Shirin mgn taji an shaqeta ta baya batare da sanin waye ba suka rinqa kokawa daqyar Mom da Muntaz suka rabasu Fadila na huci ta nuna Juhud da ta zubanta ido tace “muguwa azzaluma Ni dama tunda akace kinje barka nasan ba Alkhairi ne yakaiki ba ace daga zuwanki jaririya ta kama cuta kwana uku da haihuwarta batayi ba sai yanzu da kikaje to wlh ki sakar Mana kurwar yarinya ko mu aikaki lahira shegiya baqar kadara”
Cafewa Addah Abulle tayi da cewa “to waima meye yakaita barkar waye yace Yana buqatar barkarta gsky nikam wannan lamarin na gdannan ya isheni Abu ya wucce kan wadanda suka jajuboki ya dawo kanmu shekara uku dayin auren nan baa haihu ba shine daga kinji an haihu zaki lashe musu ya tab wlh bazai yuwu ba dole ma Mai Martaba ya zaba a gdannan ko mu da muke dolensa ko Kuma ita da suka liqawa mutane” tunda suka fara mgn ta fahimci inda suka dosa jikinta yake rawa hawaye ya kasa tsayawa a idanunta mgn takeson yi Amma bakinta ya sarqe zuciyarta wani zafi takeyi hakanan takejin a ranta yau ko zata fita a kasheta sai tabar gidan lamarin ya fara wucce yanda zuciyarta zata dauka. Juyawa tayi ta shiga dakin da take taja akwatu ta fara hade takardunta tana wani irin kuka me ciwo itakam tagaji da wannan quntattaciyar rayuwar shekaru ashirin da biyar na rayuwarta ta qaresu a qunci shekaru tara Mom na hadiyar baqin ciki akanta meye yasa bazata gushe ba kota samu salama da sanyin ruhi suma masoyanta su samu?
Tanayi tana jan zuciya tana tunano yanzu hakanan zata fice tabar gudan jininta daya tal a duniya meye makomar rayuwar Sarki idan ta tafi ta barsa? Dagowa tayi bayan ta gama hada kayan ta zuge ZIP din trolley din ta miqe ta dauki hijjab dinta ta zura taja akwatin takai hannunta zata bude qofar Mom ta bude ta shigo idanunta na tsiyayar da hawaye tace “duk wani abu daya kamata nayi miki Meenah nayi miki domin Allah meye yasa qaramin Abu yakesaki jin tafiya kibarni shine mafita? Me kikeso nacewa Rasheed idan Allah ya bayyanashi yaji abinda kika aikata? Haba Meenah nidai Ina ganin indai kika yanke barina to tabbas baki biyani haqqina ba Kuma kin basu damar yimin dariya ne…….”

Wani kuka ta saki me ciwo tare da durqushewa ta kifa kanta jikin akwatin tanayinsa babu furuci kalma batada ita a bakinta da zata iya furtawa zama Mom tayi tana bata baki tana rarrashinta Amma kamar tana zugata, aka bude qofar aka shigo Mai Martaba ne ya shigo fuskarsa Babu alamun wasa yace “ke Aisha tashi ki bani guri inason mgn da ita” miqewa Mom tayi ta fita tana kallon Meenah data dunqule tanata aikin kuka ta girgiza kai ta fice daga dakin ya nemi guri ya zauna Yana nazarin yarinyar da yanda duk jikinta ke rawa jikinsa yayi sanyi shi kansa yanajin kunyar kansa irin biyayyar da yarinyar takeyi masa bata cancanci haka daga gareshi ba ta daukeshi kamar mahaifi tanayi masa biyayya fiye da yanda yayan daya Haifa sukeyi masa to waima meye yasa yake yarda da jita jita akanta ne?”
Gyaran murya yayi yace “ina kike Shirin tafiya yanzu?” Cikin kuka tace “inda ubangiji ya kaini don girman Allah karka hanani Mai Martaba na gaji wlh na gaji da qaddarorin nan masu wahalar dauka inaji a jikina banida wani rabo na farin ciki a rayuwata Mai Martaba idan ka hanani zan rasa kaina zuciyata zata buga…..” Jinjina kai yayi cike da tausayawa yace “meye yasa kika yanke wannan hukuncin?” Dagowa tayi idanunta akansa bakinta ba rawa tace “Baffa’am shine mutum na farko dayayimin gata ya zabi farin cikina akan komansa Mom ta dora sunci baqin ciki akaina sunama kan ci wlh koda bana tare da mijina inaji a jikina duk inda yake hankalinsa yana gareni Mai Martaba bazan zama silar bacewar da na zama silar macewar uwa ba idan naci gaba da zama da Mom baqin cikin abinda ke faruwa Dani zai iya taba tata rayuwar nikam na riga na zaba na yankewa kauna da samun wani jin dadin rayuwa kubarni naje na rayuwa ni kadai abinda kukayi a baya na gde…..”

Daganta hannu yayi yaja zuciya yace “naji Meenah ki cire wannan tunanin a ranki Babu inda zakije kinanan” miqewa yayi ya fita daga dakin yana fita ta koma ta kwantar da kanta jikin gado tana wani kuka me ciwo, tana jiyo hayaniya da fadan Mai Martaba a falo saidai bata fahimtar meye yake cewa sama sama taji yana cewa “ni na haifi Rasheed na haifi Kareem dukkansu ikona ne duk da qaddara tasa Meenah bata zama mallakin Kareem a farko ba hakan bazai zama hujja ta cin mutumcinta ba wlh tallahi Zainab duk ranar da wani abu makamancin wannan ya Kuma faruwa zakisha mamaki na Kuma babu wanda ya isa hanani zartar da abinda nayi niyyah a gobe juma’a zan yanke abinda nayi niyyah kai nama fasa yau dinnan idan da Wanda ya isa ya Hana”
Bata fahimci komai ba Amma sosai taji wata faduwar gaba ta darsar mata ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta damuwa tasa zazzabinta na qa’ida ya dirar mata wanda likitoci sukayi ittifaqin zai iya haifar mata da ciwon zuciya saboda Yana yawan kumbura zuciyar tata.
Bacci ne ya dan dauketa sama sama kasantuwar ba sallah zatayi ba tanaji ana Kiran sallar Isha a masallacin Fada ta sake gyara kwanciyarta bacci me nauyi ya dauketa batasan meye yake faruwa ba sai ji tayi ana yiwa qofar bugu na hauka ta miqe zunbur tana son tantance dalilin bugun taji muryar Addah Abulle tana cewa “billahil lazi la’ilaha illahuwa indai nice na haifi Kareem bazai taba zama da wannan tsinanniyar yarinyar ba matsayin mata wlh Allah saidai idan na kasheta nima a kasheni”

Muryar Mai Martaba taji Yana cewa “bazama takai ga kisan ba kizo ke ki fita a gdannan ki tafi gdan naki uban aure ne na daurashi Babu dalilin fasashi” bude qofar taji anyi ta sake zabura ta zubawa me shigowar ido Kareem ne ya shigo idanunsa akanta itanma shi take kallo ido cikin ido ya mayar da qofar ya rufe ya nufota taja baya da sauri yaja ya tsaya Yana kallonta ya dan saki fuskarsa batare data tsammata ba taga wasu hawaye sun kwaranyo daga idanunsa ya daga hannu sama yace “Alhmdllh Meenah duk da banyi tsammanin zuwan wannan lkc da wuri ba Ina tayamu murnar samun kanmu a sabuwar rayuwa matsayin da naso samunsa a farko ubangiji bai amince ba wato ma’aurata……….”
Ai bai rufe bakinsa ba ya tsinceta a qasa warwas yayi kukan kura ya isa gareta Yana jijjigata Addah Abulle ta danno qofar tayo kansu da wuqa tsirara a hannunta ya miqe da sauri ya tareta Mai Martaba da Muntaz suka tayashi riqeta ya damqe kaifin wuqar da hannunsa tana wani kuka me cin zuciya tana cewa “wlh saina kasheta mayya cikin zuri’a ta bazan taba lamunta ba……”

Abinda Mai Martaba baitaba yiba yau shine yayi mata allurar yan maza ta motsa abinka da tsohon soja baisan sanda ya saketa ba yayi bal da ita taje ta daki gini ta dawo qasa tana qoqarin tashi ya sake nufarta Kareem da hannunsa keta zubar jini saboda riqon da yayima wuqar ya nufeshi da sauri shida Muntaz suka riqeshi daidai lkcn da Arman ya shigo shima yayi kan Mai Martaba Mom ce da Salman sukayi ta Juhud suka kimkimeta Kareem ya saki Mai Martaba har yanzu kuka yakeyi yace “don Allah Mai Martaba kada kayi abinda kayi niyya ka qyaleta tayi duk abinda da tayi niyya aurena da Meenah ne Allah ya riga ya daurashi babu abinda zai kwanceshi saidai mutuwa ko qaddarar data raba auren Rasheed da ita”
Fita yayi da sauri ya shiga motarsa yabi bayan tasu Mom suka nufi asibiti sukayi emergency da ita likitoci suka rufu akanta numfashinta suketa qoqarin saqalowa abin ya gagara faduwar da tayi taja mata shiga doguwar suma, ranar daga Kareem harsu mom Babu Wanda ya koma gda anan suka kwana gurinta gabadaya ya rude hankalinsa yaqi kwanciya Yama manta da lissafin yar jaririyar yarsa da take asibitin itama ta Juhud din kawai yakeyi Muntaz ya tafi gda suka dawo da Hamida da Mai Martaba Addah Abulle bata gdan hankali ma baya kanta balle asan Ina ta nufa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button