JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Mom da Hamida ke jinyarta tsayin kwanakin biyar batasan waye akanta ba Kareem ya canza mata asibiti yakai uku qarshe Asibitin Mal Aminu Kano ya mayar da ita acanne suka samu ta fara motsa gabbanta sai lkcn ya samu nutsuwar tunawa da iyalinsa har zuciyarsa nutsuwarsa ta rabasa da tunanin komai sai lfyr Meenah babban tashin hankalinsa da likita yace masa zuciyarta ce take barazanar daina aiki saboda ta cunkusa mata damuwar da tafi qarfinta tunaninsa ta yanda zai fara nasa aikin ya goge mata duk wata damuwa dake buwayar rayuwarta ya sanyata farin ciki kamar yanda ya shirya yi a farko Allah bai amince masa ba burinsa bai wucce Meenah ba cikin duniyarsa gata ya sameta Amma Kuma wasu abubuwan sun danni soyayyarta gareshi tsabar qin da takeyi masa ne yasata shiga wannan yanayin dajin cewa shine matsayin mijinta ko meye dalili?
Wadannan tunane²n sune suka sanyashi ramewa cikin kwanaki biyar din.

Ranar kwana biyar din ranar ta kama sunan Matarsa hakanan ya nufi Katsinan bashi da wani kuzari dake yasan dama ba taron sunan akeyi ba har zuwa lkcn Zainab sunan yarinyar kenan sunan mahaifiyarsa yasa mata tana asibiti ciwon gendis yayi mata kamun gaske anyi mata juyen jini Amma duk da haka taqi lfy inda likitoci suka tabbatar da a cikin mahaifiyarta ta samu matsala Amma su sun dauki alhakin ciwon kacokan sun dorawa Meenah musamman su Dada Hanne da dangin Zahrah da sukayi tsalle suka dire suka dauke yarsu cewa bazata zauna da Meenah ba shidai daya yakabo yaje ta qare masa,
Bai damu ba koda yaje gdan nasa ya tarar dashi a kulle domin ya riga ya shiryawa zuwan wannan Rana a baqin kishi irin na Zahrah ba Meenah data tsans fiye da kowa a duniya ba ko wacce mace ya auro sai anyi wannan rikicin shiyasa baisa abin a ransa ba taje tayita zamanta a gdannasu idan ta gaji ta dawo. Kwanan Meenah bakwai a Kano ta bude idanunta tana kallon kowa daidai a lkcn tunaninta bai dawo ba bama kowa take ganewa ba hakanan ta rinqa rarraba ido kan mutane.

Mom sai sannu take jera mata tana binta da kallo da la’asar Kareem ya iso asibitin shida Ya’isha tun daga harabar asibitin ya hadu da Lado drivern Mai Martaba yayi masa albishir din Juhud wani farin ciki da murna daya dade baiyi irinsu ba suka cika zuciyarsa har gudun motarsa ya qara don ya isa gareta yayi parking baikai ga rufe motar ba ya nufi ciki sai Ya’isha ce ta rufe masa motar cikin tausayinsa ko lkcn da Meenah take matsayin matar Rasheed Kareem baya zama cikin nutsuwa muddin tana guri Allah ya jarabceshi da qaunarta gashi Kuma yanzu tasan ba qaramin rikici ya saukowa kansa ba don tabbas Meenan da ba itace yanzu ba batajin zai samu kanta da sauqi duk wannan rawar qafar da yakeyi akanta ba gani zatayi ba tunda bashine a zuciyarta ba hasali ma ita a lissafinta ma Babu aure.
Yana shiga bai saurari kowa ba ya nufi gadon da take kwance idanunta a lumshe yaja wata ajiyar zuciya tare da binta da kallo me nuna tsantsar qauna da kulawa yace “Aminatuh” jin saukar muryarsa tayi kamar muryar Rasheed ta kuwa juyo da sauri tare da bude idanunta ta saukesu akansa yanayi mata gizo cancanzawa yakeyi daga Kareem ya koma Rasheed ta kasa gane taqamaiman waye a gabanta.

Tun farkawarta bata iyayin furuci ba sai yanzu da bakinta ya bude da furta “Abdulrasheed…..” Daga haka ta sake lumshe idanunta ta kwantar da kanta a pillow kuka me ciwo ya qwace mata daya Sanya Mom dake shigowa nufota da sauri tace “Subhanallahi waike yanzu Aminatuh bazaki daina Sanya damuwar nan a ranki ba kenan kullum ke kenan cikin jinya” wata ajiyar zuciya me qarfi Kareem ya sauke ya nemi guri ya zauna gumi na karyo masa Yana sharcewa Ya’isha dake shigowa tace “ya Kareem motar taka baka rufeta ba ka barota” shafa sumarsa yayi yace “wlh hankali nane baa jikina ba ince kin rufe” dagansa kai tayi ta nufi gadon da Meenah ke kwance ta riqo hannunta tace “amaryar Ya Kareem sunqi Allah yaso meye yayi zafi da doguwar jinya haka?” Zame hannunta tayi a na Ya’isha ta sake gyara kwanciyarta taci gaba da jan zuciya abubuwan da suka sabbaba mata ciwon suna dawo mata a fili tace “Aure, Ni Mai Martaba Ya Kareem Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Allahumma ajirni fih musibati wlh banaso don Allah ku taimakeni ku rabani dash………

Nasani wannan page din ba kowa zatayima dadi ba so Amma a babin qaddara wannan daidai ne shi ubangiji Yana zartar da hukuncin da yake daidai batare da la’akari da abinda Wanda ya zartar da hukuncin akansa zai nazartawa zuciyarsa ba kada ku manta matar mutum kabarinsa Kuma shi rabo ajali ne yakanyi kisa ma idan qarfinsa yakai.
So kada kuga laifin alqalamina haka abin yake kamar yanda kuka ganshi a rubuce kada ki manta 50% is true life story.

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/6, 9:00 PM] Oum Hairan: 0030 Miqewa Kareem yayi ya fice daga dakin ya koma waje ya rafsa tagumi jikinsa sai tsuma yakeyi Yana tausayin kansa Amma yafi tausayin Meenah saboda tafisa shiga damuwa ya jima zaune a gurin kafin likitan ya iso suka shiga tare likitan ya dubata ya sake bata kulawa ya fice daga dakin ya dubi Juhud datake zaune take shan tea yace mata “sannu” bata ko dubesa ba ya nemi guri ya zauna Suna taba hira lkc zuwa lkc suna taba hira da Ya’isha Mom tana Sanya musu baki itako ko kallo bai isheta ba hasali ma tunda ya zauna takejin wani qunci aranta ji takeyi kamar ta fice daga dakin bata son ganinsa.
Kwanciya tayi taci gaba da saqa da warwara a ranta sai yamma Ya’isha tace zata tafi mijinta yazo daukanta sukayi sallama suka tafi Mom ta tafi rakasu ya taso ya matso jikin gadon yace “duk da nasan ni mai laifine a gurinki Meenah Allah ya sani inasonki tun kafin yanzu Amma bantaba yimiki fatan ki dawo gareni ba Allah shine ya tsara hakan saboda haka na karba Kuma nayi masa gdy kema inaso ki karba kiyi masa gdy……” Miqewa tayi zaune zuciyarta na tafasa tace “akanme zanyi gdy akan abinda ba zabina ba bankuma nema ba? Why da zakace dole saina karbeka? Kareem da zaka manta dani ka fice cikin rayuwata da mun taimaki kanmu wlh banyi farin ciki da samunka matsayin miji ba kada kaji a ranka na karbeka bazan taba karbarka ba Rasheed shine zabina shine rayuwata……”

Hannunsa ya dora bakinta yace “stop Meenah ya isheki don Allah kada ki fasamin zuciya da kalamanki kiji a ranki wannan bayin kaina bane yin Allah ne….. Wayarsa ce tayi ring ya zaro a aljihunsa number Zahrah ce yayi kamar ya kashe saidai zuciyarsa ta raya masa ya daga qila wani abune Important yasata kiransa danna wayar yayi ya Kara a kunnensa ta cikin wayar Meenah take jiyo gunjin kukanta tana cewa “Allah ya isa tsakanina dakai Kareem ka cutar dani kaine wlh kaine sila tunda kaine ka rakitomin ita cikin rayuwata harta cutar dani, na dauki ciki watanni tara na Haifa matarka ta kashemin yata wlh bazan yarda ba kaji na rantse maka wayyoh Allah na Zainab ta mutu Aminah ta lashemin yata……”
Qit ya kashe wayar idanunsa ya ciko da hawaye ya dubi Juhud data zubawa TV idanu a zahirinta ba TV take kallo ba kalaman na Zahrah ne sukeyi mata yawo a kwanya yace “kinji sauqi likita yace zaki iya komawa gida zanyiwa Mom mgn ta shirya mu tafi Zainab ce ta rasu….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button