JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL
JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Ya jima bacci bai daukeshi ba sai juyi yakeyi da safe ya fiçe ya nufi cikin gdan Meenah bata tashi daga bacci ba a zahiri ba baccin takeyi ba kawai juyi takeyi, shiga yayi part din kumbo Hami suka gaisa ya wucce bangaren Alh Garbu suka gaisa yayi shiru na dogon lkc kamo hannunsa yayi yace “meye yake faruwa ne Dan Boko?” Qasa yayi da kainai Yana shafa sumarsa can Alh Garbu ya sake dubansa yace bai wucce kace kanason tafiya da matarka ba ko?” Jinjina kai yayi yace “hakane Alh inason jibi idan zan tafi mu tafi gabadaya saboda dawowa zatayimin wahala kusa” jinjina kai Alh Garbu yayi yace “shikenan zan fadawa kakar taku inyaso saisu fara Shirin abinne yazo Babu tsammani Amma fah akwai abinda bazan dauka ba cikin lamarin aurenku duk wani cin Kashi da akayi mawa Aminah a baya yanzu ko ita ta daukeshi ni bazan daukaba” ya jima yana kafa sharrudansa shidai Rasheed jinsa kawai yakeyi har ya gama ya tashi ya fice.
Lkcn da Kumbo Hami taji Shirin da Alh Garbu yayi taso tace aa Amma ya hanata katabus dole hakanan ta hqr tana jiran ranar zartaswa aikam ana samun Meenah da mgnr tayi tsalle ta dire tace batasan zance ba duk Wanda suke tunanin zai fada aji ya fada tayi kunnen uwar shegu Rasheed kam abokin gaba ya zama batako kallonsa bai wani damu ba saidai ya kalleta yayi murmushi ya barta tayi duk abinda yasan na dan lkc ne da lkcn ya wucce shikenan, ana gobe tafiyar da dare ya shiga har dakinta ya tarar da ita itada Aunty Kharimatu da Kumbo sai aikin rarrashinta sukeyi suna ganinsa suka miqe suka fita ya mayar da qofar ya rufe ya nufota ta miqe tsaye ya tsaya Yana murmushinsa na isa tare da zura hannunsa a aljihunsa ya harde qafarsa ya jingina jikin bango yace “banzo domin na baki hqr Kona rarrasheki ba saboda Ni nasan banyi miki laifi ba hasali ma nine nake tuhumarki so inada abinda yafi haka muhimmaci kin fadamin wata mgn ne da nakasa jureta shine nazo baki amsa Meenah yes na amince keda Kareem kuka Samar da Muneefah Amma kada ki manta kafin Kareem ya baki da nine na fara baki na farko kika zubarmin na biyu kika haifamin gashi ya zama saurayi so wannan kadai ya isa ya tabbatar miki ni na wucce kiyimin gatsali akan Muneefah Kuma ko kinaso ko bakiso dole kibarni da ita domin ba saboda ke nakejin yarinyar a Raina ba saboda mahaifinta yayimin kyautarta ne”
Shafa gemunsa yayi yayi murmushin gefen baki yace “shekarar Muneefah daya da rabi ki shirya karbar qaninta kowanne lkc daga yanzun ni bana wasa da dama amfani nakeyi da ita sosai” ficewa yayi daga dakin yabarta tsaye da zubar hawaye takaici kamar ya kasheta taja qwafa ta koma ta zauna.
Duk wani shiri da Kumbo Hami taso yi mata taqi bata hadin kai sai huci takeyi kamar ta kashe kowa haka takeji batasan meye yasa takejin haushin Rasheed ba ko ganinsa batason yi sauqinta daya dake tunda ta haihu Kumbo take hadata da magungunan da tasan bazasu cutar da itaba so data fahimci ba hadin kai zata bata ba saita tattara mata ta zuba mata cikin kayanta ta hade mata komai washegari kuwa da wuri suka dauki hanyar 9ja aikam anyi tafiyar kurame Babu me cewa wani qala garama shi da Khamil suna hira jefi² inda suka sauka ta tsaya tana kallo bata taba zuwa Lagos ba hakanan takejin to Ina ya kawosu?” Bai bata damar tunanin mafita ba motar office dinsa tazo ta daukesu suka nufi unguwar da yake da zama tasha mamakin gidan da aka kaisu ta tsaya tana qare mawa gidan kallo.
Plat ne me kyau sosai Rasheed akwai son qyale² ya qawata gidan tsaf ta tabe baki tajishi ya saqali hannun Muneefah ta sakar masa ita ya nuna mata dakunan yace gasunan keda yaranki duka sun isheku fatan nasara” dakinsa ya shige da Muneefah tabisa da kallon takaici ta gyada kai ta bude dakin kusa da ita ta shiga komai na dakin a tsare yake sosai abin gwanin birgewa gefe ga wasu manyan set na akwatuna guda 12 ta zubawa akwatunan idanu tana tunanin to na meyene?” Tabe baki tayi tace “nima dai da son wahalar da kaina kulle dakin tayi ta cire kayanta ta bude akwatun da ta taho da ita ta dauko wata qaramar riga Mara hannu ta shafanta turaruka ta nufi bayi tayi wanka ta fito ta shafa mai ta zura rigarta ta haye gado taja duvet tunda ba sallah zatayi ba nan take baccin gajiya yayi gaba da ita batasan sanda ya shigo ya kwantar mata da Muneefah ba sai wajen hudu ta farka taganta kwance ya cire mata riga daga ita sai Pampers tanata baccinta.
Yunwa ce ta fafareta ta miqe ta fito tana hamma ta nufi kitchen din taji qamshi na tashi ta qarasa da sauri ganinsa tayi dagashi sai boxes da headphones a kunnensa ya zage sai yankan alayyahu yakeyi ta juya zata tafi ashe ya ganta taji yace “kije ki huta idan na gama zan sammiki nasan cikinki ne Babu alert shiyasa kika fito
Yayi tsammanin zata kulashi yaga ta juya tayi tafiyarta ta koma dakinta yaci gaba da girkinsa Yana waqoqinsa bayan ya gama ya jera a dinning ya bude dakin ya isheta tana waya daga yanayin wayar yasan da Mom dinsa takeyi ya shafa kansa ya juya ya fice, koda ta idar bata nemesa ba har ya sake gajiya ya shigo ya tararta ta hade kai da gwiwa tanata jan zuciya ya matsa gabanta ya tsugunna yasa hannu ya dago kanta ta zame kannnata yayi mata murmushi yace “kinajin meye game dani?” Batace masa komai ba ta fara qoqarin tashi ta nufi parlourn yabi manyan bombom dinta da kallo yana lasar lips dinsa ya lumshe idonsa Yana tunano rayuwarsu ta baya da irin soyayyar da sukewa juna, zuciyarsa ce tayi baqi idanunsa ya kada yayi ja daya tuna Kuma fah irin abinda takeyi masa shine tayima Kareem shima ko?” Tuni hasken zuciyarsa ya disashe yaji wani qunci a ransa a fili da qarfi yace “Oh God meyesa hakan ta farune………..”
Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..
Oum Hairan
[8/28, 8:41 PM] Oum Hairan: Dafe kansa yayi ya koma ya zauna kalmar Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un tana kaiwa da komowa azuciyarsa shi kansa Yana jinjina baqin kishinsa baya iya jurewa abubuwa game da Meenah tun kafin takai haka, qwafa yayi ya miqe ya fito falon tana zaune Muneefah tana wasa ya nufi inda yarinyar take ya dauketa suka nufi dinning ya hadansu abinci yanaci Yana bata tanajan gemunsa Meenah na satar kallonsa har suka gama ya miqe suka fice ta Isa ga abincin ta diba daidai cikinta ta shige dakinta taci tasha yourghut dinta taje tayi brush ta sake kwanciya Basu suka shigo gidan ba sai Tara na dare tana kwance Muneefah ta shigo Yana biye da ita da qatuwar yar tsanarta ta fada jikinta ta miqe tana mata dariya tace “sarkin yawo kin sama abinda kikeso ko Ina kukaje”
Gwarancinta ta rinqayi ya nemi guri ya zauna batako kallai ba taci gaba da wasa da yarta shikuma Yana kallonsu ganin ba zai samu arziqin kulawa ba yasashi miqewa ya fice ya shiga dakinsa ta miqe tana murmushin mugunta ta nufi bathroom tayima yarinyar wanka tasa mata kayan bacci ta kwantar da ita ta kulle dakinta da key ta kwanta,. Ba wuyar bacci gareta ba nandanan bacci ya dauketa sai Kuma kashegari da safen ma shine ya tasheta ya shigo cikin shirinsa na tafiya office tunda ya shigo suka hada ido ta kawar dakai tare da lumshe idonta ya matsa kusa da Muneefah yayi kissing nata ya zubawa fuskar Meenah idanu yana ganin yanda take qifqifta idanu yaja fasali ya sauke bakinsa a kuncinta yace “kin tashi lfy” ajiyar zuciya ta saki wata kasala na saukar mata tace “normal” murmushi yayi yace “gud zanje office me kuke buqata”