JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Bayan komai ya lafa yaso su koma Lagos ta kafe Saida tayi arba’in sannan suka koma da qarin me raino daya Ladi itama mutuniyar kirki sukaci gaba da rayuwarsu cikin gdyr Allah da amincewarsa Rasheed kullum likkafa ci gaba takeyi yau matsayin General Rasheed Gen Mahfuz yake amsawa inda makarantar Meenah kullum take qara habaka abin gwanin birgewa da hamdala shekara biyu Meenah ta qara haihuwar ya mace daga kanta tace ta gama abinka da yan bokon qarshen zamani suka fita India aka juyar da mahaifar gabadaya ta dawo taci gaba da kula da yaranta.
Sannu a hankali maqiyanta irinsu Fadila Dada Hanne Hajiya Bilki da wasunsu na boye sai gashi duk sun zama yan koranta idan taje Daura har zuwa sukeyi gaisheta musamman Fadila data zame mata kamar aminiya yanzu duk duniya bata da qawar data wucce Meenah hakan ya samo asali ne daga yanda Meenah ta shiga ta fita taga sun daidaita da mijinta ya mayar da ita dakinta cikin yayanta, itama Addah Abulle daqyar bayan auren datayi Mai Martaba ya dawo da ita dakinta inda ta dauki soyayyar duniya ta dorawa yaran Meenah guda biyu Muneefah da take yar danta da Kuma Kareem qarami da yaci sunan danta duk wani tanadinta nasune sauran jikokin gdan har tsiya sukeyi mata wai ita ta fiye son kai, itadai Meenah saidai tayi dariya tana mamakin yanda komai ya wucce kamar ma baayi ba idan tai tsai sai kawai taji hawayena tsiyaya a idanunta da zaran ta tuna yanzun muma duka wataran shudaddu ne gushewa zamuyi a manta da tarihinmu mu dusashe kamar baa haliccemu ba, a wannan ritsin tsoron Allah yake qara ziyartar ruhinta takanji duk duniya tayi mata zafi kullum addu’arta Allah kada ya jarabci yaranta da irin jarabtarta Allah ya Basu qaddara me sauqin dauka ya Sanya musu albarka cikin cinsu da shansu da motsinsu a kowanne yanayi yabawa mijinta qarfin gwiwar nemo halal a ko Ina take.

Tammat bi Hamdullah

Tabbas komai yayi farko zaiyi qarshe yau dai Juhud yazo qarshe Ina gdy ga ubangijin bayi me kowa me komai daya bani ikon farashi da kammalashi lafiya kamar yanda na tsara.
Kurakuran dake ciki ubangiji ya yafe Mana badon halinmu ba amfanin ciki Allah ya bamu ikon amfana baki daya.
Bazan rufe ba sai nayi gdy gareku masoya da baku qasa a gwiwa wajen qarfafamin gwiwa da kudadenku da lkcnku tabbas Ina alfahari daku Ina fatan ubangiji ya sadamu a dausayin zumunci na masuyin soyayya dominsa.

Kada ku manta next book dina YAFI ZAMAN AURE!_ yananan tafe da irin tasa rikita rikitar very soon insha Allahu.

Oum Hairan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button