RAUDHA Page 21 to 30

Farida ita ke tausar sa akan yaci gaba da hakuri sannan yakula da ƙanwar sa wajen ceto rayuwan ta, tana nuna masa hanyan da zai bi don nuna ma RAUDHA kuskuren ta, amma duk hanyar da tanuna masa baya jin zai iya bi, abu ɗaya yaɗauka shine yin mata nasiha, yakan zaunar da ita yay ta mata nasiha wani lokacin har da hawayen sa, amma RAUDHA ko kaɗan bata taɓa jin sa ba, a ganin ta rayuwan ta ne kuma hakan tazaɓar ma kanta, babu wanda ya’isa yahana ta yanda take so tatafiyar da rayuwan ta, wani lokacin ma idan yamatsa mata wani irin fushi take yi dashi wanda ada ko kaɗan idan zata yi fushi dashi bata yin hakan, kamar wata mara hankali haka take koma wa, idan tasoma musu hauka sai abun yabasu mamaki matuƙa, har zagin Suhaib ɗin take yi idan fushin ta yayi ƙololuwar tashi, sai takoma tamkar ba ita ba, abun fa yay mugun ɗaga musu hankali ganin yanda RAUDHA tasauya lokaci ɗaya, baza ka taɓa gane bata da hankali ba sai idan ka shiga rayuwan ta, wannan dalilin ne yasaka daga shi har Farida suka shafa ma kansu lafiya tunda RAUDHA bata sauraron su.
Yanzu RAUDHA da Rash tare dasu Zen sun jone matuƙa, duk inda zaka gansu tare suke, RAUDHA ta saki jikin ta sosai dasu, yawon su da ko ina ma tare suke zuwa
Karatun ta yanzu bata cika maida hankali ba tunda bata da lokacin yi, sai dai abu ɗaya tamaida hankali yanzu idan har suna da Lecture bata zuwa ko ina sai ta gama, duk nacin da zasu yi tazo su tafi bata bin su sai ta saurari Lecture ɗin ta, idan kuma suka tafi yawon su time ɗin Lecture na cika duk inda suke sai ta matsa musu sun dawo
Wani lokacin Rash tana biye mata su shiga Lectures tare, wani lokacin kuma taƙi bin ta tazauna wajen su Maan har sai idan ta fito sannan su shiga motan Zen subar makarantar, basa kuma dawowa sai idan time ɗin Lecture yayi, idan kuma aka tashi RAUDHA bin su take yi wani lokacin su tafi gantali
A zaman da tayi dasu RAUDHA ta fahimci halin su gaba ɗaya, yanda Rash take bin mazaje da yanda su Zen suke bin mata hakan baya mata daɗi sosai, tunda suka nuna mata rayuwan tanuna musu ita kuma sam bata so ko kaɗan, ko idan Zen yana riƙe ta tare da rungume ta ta rinƙa faɗa kenan har fushi take yi dasu, sai idan sun lallaɓa ta gaba ɗayan su sannan take dawowa su haɗe tare.
Sai dai abinda bata sani na su Zen ba sun bata lokaci ne yanda zata ƙara sakin jiki dasu ta yanda zasu ƙara nuna mata abunda suke so a wajen ta, idan kuma taƙi suna da hanyoyin da zasu bi don cin ma burin su akan ta, ahankali-ahankali zasu ci gaba da jan ta, musamman ma Zen shine yake shige mata kuma sosai tasaki jiki dashi, shi kaɗai ne take iya bari yana riƙe ta, shima ɗin don taga ba addinin su ɗaya bane, sannan ma ita ko kaɗan hakan ba wai burge ta yake yi ba shiyasa tun farko bata yi kuma bata soyayya tunda ba wai tasan addini bane bare tasan an hana, sha’awar hakan ne bata dashi ko kaɗan, duk idan namiji yaraɓe ta tana jin tamkar zata haukace ne sabida tsananin baƙin ciki da ƙuncin dake ziyartan ta.
????????????
Yau ma kamar ko yaushe daga school suka fito yawon shaƙatawa, suna zaune a haɗaɗɗen wajen huta wa inda akwai ƙoramu a wajen wanda aka ƙawata su sosai, da irin su soomun pool da abubuwan more rayuwa
Daga can gefe Rash ne da Maan zaune akan fararen kujeru tsakiyan an saka musu glassess table, sai abubuwan sha da aka ajiye musu, hira suke yi suna dariya cike da nishaɗi
RAUDHA da Zen kuma suna zaune bakin ruwa, ita RAUDHA ta saka ƙafafun ta ciki tana wasa da ruwan sai jan wandon ta take yi don kar yajiƙe tana murmusawa cike da nishaɗi, sosai irin wajen nan yake mata daɗi tare da faran ta ranta
Ɗago hannun ta tayi takalli agogo kafin tajuya tana kallon Zen dake zaune kusa da ita yana latsa waya tace
“Zen I want to go time ɗin Lectures yayi”.
Ɗago kai yayi yatsira mata idanu, ji yake yi tamkar yarungume ta yay ta tsotson bakin nan nata da yafi komi burge sa a jikin ta, shi dai yarinyan tayi masa ya gaji da jiran ranan da zai mallake ta akan gadon shi
Ganin kallon da yake mata ko ƙyafta idanu baya yi duk da kuwa ba yau yasa ba yin mata irin kallon ƙurilla ba, ita har mamakin sa take yi ko me yake kallo? Murmushi tayi tasaka hannu taɗana masa yatsan ta a saman fuska
Dasauri yayi firgigit yana sosa wajen
Hakan yasaka RAUDHA tasaki dariya tana kallon sa
Tunda yake be taɓa ganin dariyan RAUDHA ba, komin abu bata iya dariya sai murmushi, shiyasa sai yaga ta ƙara masa mugun kyawu musamman da yaga fararen haƙoran ta jere a waje
Sai da tayi dariyan ta son ranta kafin taturɓune fuska ganin dai kallon nasa yaƙi ƙare wa, miƙe wa tayi tana yamutsa fuska
Hakan yasa hankalin Zen yadawo jikin sa shima yamiƙe yana cewa “haba Babe muna tsaka da jindaɗin mu kike son tafiya? Please ki bar Lecture ɗin nan na yau ki zauna mu huta sosai”.
Kallon sa tayi sai tataɓe baki tana yin gaba batare da tayi masa magana ba, mota tashige wajen me zaman banza
Tunda tatashi su ma su Rash suka tashi suka nofo wajen Zen
Maan yace “har time yayi ne?”
Ɗage kafaɗa yayi batare da yayi magana ba
Maan hannu yaɗaura saman kafaɗan sa yace “ka dena damuwa yau komi zai wuce, mu je dai mu mayar da ita school ɗin”.
Dariya Rash tayi tace “babu ruwana Ni dai duk abinda yabiyo baya”.
“Dama wa yace da ruwan ki?”. Zen yafaɗa yana hararan ta kafin yayi gaba yanufi wajen motan
Taɓe baki tayi alamun ko ajikin ta, tashige jikin Maan tana faɗin “mu bar su don Allah su tafi Ni bana son mu bar nan”.
“Ko Babyna?” Maan yayi maganar yana shafa fuskar ta bayan ya ƙara matse ta a jikin sa
Zata yi magana suka ji ƙaran horn
“Mu je Babe kinsan halin Zen, kuma kinsan yau muna da shiri akan RAUDHA so dole mu zauna musan abun yi”.
Gyaɗa kanta tayi batare da tayi magana ba suka nufi wajen motan, baya suka shiga Zen yaja motan suka bar wajen
A cikin motan Rash da Maan suna manne da juna abun su yayinda suke ta romancing junan su ko gajiya basa yi
RAUDHA kuwa titi ta kafa ma idanu tana ta kallon gari
Kallon ta Zen yayi cikin ƙasa da murya yace “My dear Ina alƙawarin da kikai min?”
Kallon sa tayi tana waro manyan idanuwan ta akan sa batare da tace uffan ba
Murmusawa yayi yace “ko kin manta jiya kin ce min yau a gidana zaki kwana?”.
Sai kawai RAUDHA tasaki dariya tana kwantar da kanta jikin kujeran, cikin dishewar muryan ta me sanyi tace “uhmm bazan iya zuwa gidan ka in kwana ba, dama wasa nake maka don ka matsa min nafaɗa haka”.
Marairaice murya yayi yace “haba Babe meyasa Zaki yi min haka bayan kinsan Ni dagaske nake yi?”
Shiru ne yabiyo bayan maganar sa, don haka yasake cewa “shikenan to i know har yanzu baki yarda dani bane, kina ganin kamar zamu cuce ki tunda kinsan halin mu, but kinsan mu friend ne babu abinda zamu iya miki tunda yanzu mun zama ɗaya”.
Sai yayi shiru idanun sa kan titi yana ci gaba da tuƙin sa, kafin kuma yaci gaba da faɗin “any way yau zamu je birthday ɗin Abokina ina gayyatar ki”.