WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR…!
{THE BEGINNING OF DESTINED}
BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM.
NA
Mai_Dambu
EWF
1/2/2022
Alhamdulillahi na dawo da sabon labari me tafiya da tunanin makarantar labaruna, wannan labarin ban yi dan cin zarafin kowa ba, idan aka ga wani abu saba’nin haka kayi hakuri, wannan labarin na kudi ne akwai pages har goma sha bakwai😱 hmm somin tab’i ango ya dafa amarya yace wai-wai akwai shagali!
SADAUKARWA GA RABI’ATUL ADAWIYYA MUHAMMAD YAKASAI, MY HAF SISTER
    ”’Albishir ku.. kuce min goro…ko kusan S.squar Fashion &More
Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa…
Turaren wuta na zamani.
Milk candy
Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¼Http://wa.me/+234 703 003 7697”’
<1>
Kaza da Ƴaƴan ta!
Jigawa State Nigeria.
Yan lema local Government
DAƘAYYAWA
“Toh kaza an maka uwar Ya’ya, yau kwana bakwai da Rasuwar ÆŠan Uwana, ki bar yaran nan a bawa waÉ—anda zasu rike su, kin kasa kin tsare ke nan uwar Yara, meke nufin ki? toh maza ki had’a kayan ki, ki bar mana gida akan wasu shegun Yara mata zaki saka mu a gaba” inji wani Dattijo da ba mamaki makusanci ne a wurin matar ko mamacin da ake magana a kan shi.
    D’ago kai tayi tare da kura mishi ido, idan ta ce zata fuskance su da rigima itace zata fadi babu nauyi dan haka, gwara ta fuskanci shi cikin lalluma,
” Don Allah ku bar min gidan da Yarana mana, ka duba ina zan kai su? Bayan ku basu da inda za a rike su, don Allah” ta fada cikin matsanancin kuka da tsoron abinda zai biyo baya yasa ta kuma roke bakinta, domin tasan ba imani ne da su ba, zubewa tayi a gaban shi, tare da cewa.
“Kuyi hakuri ku barni a cikin gidan nan Insha Allah ba zan nime kome daga gare ku ba, yanzun idan na tafi wallahi ba zan iya rayuwa cikin salama ba” ta fada cikin shashekar kuka, murmushi yayi yana kallon har yanzun Harirah tana da yarintarta, domin tana nan shar da ita, kamar ba ita ta haifi yaran ta nan ba.
  Lashe bakin shi yayi tare da mata kallon kasa kasa sannan ya ce.
“Shi kenan, karki damu ki zauna nan da wani lokaci zan dawo.” Ya fada tare da bin Jamilah da ido. wacce take dauke da bokitin ruwa, gashi ruwa ya zuba a jikin ta, ya jika gaban rigar ta, yan tender boons dinta sun fito shar har kana hango shatin nipples dinta da suka yi wani irin cur dasu, ganin irin kallon da yake bin Yarinyar dashi, yasa Harirah yin maza ta ture yarinyar da take sauke ruwa, kirjinta yana yana mugun bugawa.
     “Yaya Haliru, wadannan Yaran kaninka ne ciki daya ya haife su, idan har ka musu wannan kallon waye zai musu kallon Rahama, don Ka rufa min asiri”
Cikin borin kunya ya fara fada tare da cewa.
“Zaki min kazafi ne dan naji tausayin ki na ce ki zauna da Yaranki” bata iya magana ba, amma kuma zuciyarta yayi mugun nauyi, faram faram yasa kai ya fita, wani irin abu ya tokare mata kahon zuciyarta, ta zubawa Yara hudu da Allah ya bata dukkansu mata ne, Jamilah ita ce Babba, shekara goma sha biyar, Rahmah ita ce me bi mata shakara goma sha uku. Sai Wasilah shekara goma, Rabi’atul Adawiyya me shekara takwas. Yaran gwanin ban sha’awa. Gasu kan su a hade..dukkan su kuka suke sabida yadda mahaifiyar su take kuka da fuskarta challenge na rayuwa akan su.
Tun rasuwar mahaifin su, take kuka babu ranar da gari zai waye basu ga tears a saman fuskar ta ba.
  Harirah Bafilatana ce, yayin da Alhaji Ishaq canji ya kasance bahaushe gaba a baya, kasancewar Yan lema kowa yasan gari ne na Yan canji. Harirah Bafilatanar Jama’are ce. Fara ce sol kamar ka tab’a jikinta jini ya fita, Wasilah, Jamila,. Rahmah ita suka dauko, a hasken fata yayinda Rabi’atul Adawiyya ta kasance tayi wani irin yanayi, ita ba sakata a cikin farare ba,. Hakazalika ba ta cikin bakaken, bata kama da Mahaifiyar da Mahaifinta, wani irin yanayi ne da ita sai dai hancinta da bakinta wanda ake cewa bakin na mahaifiyarta ce, hancina kuma na mahaifinta.
   Dogo ne har baka,.giranta a had’e yake. Haka sajenta ya sauko kamar na da namiji, bata da kwaranniya. Ko hayaniya, tunda baban su ya rasa taga Iyarsu tana kuka ta koma gefe ta zauna har yau bata kuma magana da kowa ba,
  Jamila da Wasilah sun dan taso, sosai tare, duk da akwai ratan shekara biyu a tsakanin su. Sai dai yanayin mutuwar mahaifin su yana saka kome masu ya tsaya cak, dama dangin Uban mugaye ba kaunar Uwarsu suke ba.
…
Alhaji Ishaq Bilyaminu,
Babban matashin me kudi ne, kuma É—an canji, duk cikin gidan su shi daya ne yayi karatun boko me zurfi, Allah cikin ikon shi ya nime aiki bai samu ba,.sai gashi wani abokin shi ya dafa shi da barkan canji inda ya ja shi suka fara tafiya Lagos, a can suka kware da aikin canji. Allah ya buda mishi inda shima bai zama mugu ba, ya budewa yan uwan shi sai dai su din mugaye ne marasa tsoron Allah. Dan sau biyu yana biyawa Yaya Haliru kujeran aikin hajji.
  Alhaji Ishaq Bilyaminu canji, shine karami a cikin gidan su, Yaya Haliru shine Babba, sai Gwaggo Lami. Badamasi kafin Naira sai Alhaji Ishaq canji, Duk da Iyayensu basa raye, amma basu wani ja Ishaq a jikin su ba, dake Allah ya daura kishin kai shine ya maida hankali akan karatu, har zuwa matakin babban diploma.
 Koda ya hadu da Harirah basu yi na’am da ita ba, domin da ya turo akan su je niman mishi auren ta, kiri kiri suka nuna basu son ta, da yayi hakuri akwai yan mata a cikin Zuri’ar su, badamasi ya gaya musu, Gwaggo Lami itama bata boye mishi rashin jin dadin ta akan akwai yar kanwar mijinta, zata hada shi da ita. Amma ya tsallake, bakwai suna haka domin Allah bane kowanne su. Saboda ya tatsi arziki ne a jikin shi, sai dai Allah ya rigada yayi nashi tsarin, domin yana haduwa da Yar Fulanin Jama’are, Alhaji Ishaq ya sussuce.
  Kafin su tafi sai da ya biya su, domin basu fito sun nuna mishi haka ba, amma daga yadda suke mishi magana ya fahimci ba zasu mishi kome ba sai ya biya su. Dan haka ya basu kudi masu yawa, suka tafi Jama’are nima mishi auren Harirah, har zuwa lokacin auren, sun kwashi rabon su, a jikin shi. Amma haka bai dame shi ba.
  Bayan auren ne ya dauki matar shi da ta kasance mara yawan magana, duk abinda suka mata sai dai ya bata hakuri, domin shima ba yawan magana ne dashi ba, lokacin da ta haifi Jamilah sun matukar gigita mata lissafi, kamar zasu rabu da Alhaji Ishaq, amma Allah ya nufa suka cigaba da zama, a lokacin da ya ga tashin hankali yayi yawa ne ya mai da ta yan leman.
Inda yake zaune, ita kuwa da taga babu matsi balle takura ta shiga sana’a, Allah da ikon shi sai gashi Ubangijin ya dafa mata, shekarar Jamilah daya da rabi, suka tafi aikin hajji da Yarinyar da Yayun shi biyu Nairah da Gwaggo Lami. Wacce sunanta Halime.
A tafiyar ma sai da Harirah ta sha kuka, suka tsangwame su tare da yar ta, shi yana wurin maza bai san meke faruwa ba, har aka gama aikin hajji basu hadu ya kai sau uku ba, domin ko zuwa yayi duba Yar shi zasu shiga kananun magana, wai ya auri Yar bauchi ta mallake shi. Wannan abin yasa shi janye jikin shi. Har suka dawo gida, kafin suka samu sauki al’amarin.