WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   “Tab” ya fada yana kallon hanyar dakin shi yana shiga ya  fara lissafin baban giwa, yadda idan ya kama ta a hannun shi. Allah ka dai ya san yadda zai yi da ita, tabbas sai an taro jama’ar garin lagos su kawo mata É—auki.

    Haka ya shiga ban daki yayi wanka sannan ya shirya. Lokacin karfe daya na rana, masallaci ya fita.  Koda ta dawo suma suna cikin domin gabatar da sallah, zama yayi a Falon yana jiran fitowar ta, Rahmah ce ta fara fitowa. Kafin ta biyo ta dauke da Deedat, tana girgiza shi.

Ganin ta yayi ta saka abaya akan kayan, wani shegen kallo yake mata me cike da Masifar jaraba irin na shi, bata kula shi ba, sai ma tsoron da ya bata,  tunda ya shiga kitchen din taki fitowa, shine yabita kitchen din suka shiga hira da Rahmah. Idanun shi na kan motsin wasilah. Har suka gama aikin. Ganin zasu fito ya ce.
“Kin ga zuba min abinci ki kawo min dinning”

    Shiru tayi kafin ta mikawa Rahmah Deedat. Ta nufi warme din abincin ta zuba mishi,sannan ya kawo dinning table, ta ajiye kafin ta koma kitchen din ga kawo mishi ruwa da kome ta ajiye zata tafi.

“Zauna mana Barista!” Zama tayi tana kallon shi fuska a haÉ—e,
“Ko zamu cikin abincin tare.”
“Ina da wanda nake so! Kuma akwai maganar aure a tsakanin mu, so ina baka hakuri.” Ta mike zata bar wurin ya ce mata.
“Nima ina son ki, zan iya auren ki” nad’e hannun ta tayi a kirji sannan ta ce mishi.
“Really!…..
3/15/22, 22:14 – My Mtn Number: 82
“Kwarai! Nima aurenki zan yi” tab’e baki tayi tana me wucewa tashi yayi yana faÉ—in.
“Tafiyar tafi maganar jan hankali!” Juyawa tayi ta Kalle shi sannan ta ce mishi.
“Baka da matsala kana azumin Alhamis da Litinin zai rage maka damuwar ka.” Tayi tafiyar ta, ba so bane a tare da Alman, sha’awa ce da muradi da zai rage sha’awar shi ba zai kuma damuwa da ita ba.

   Shiryawa suka yi ya kai su Asibiti, sun wuni a can, sun leka dakin sauran marasa lafiyan. Kafin samu Bilal da Faisal suka dawo, anan aka bude hira,  suna cikin hiran Alkasim ya zo tare da wata yarinya. Kallon su Wasilah tayi kafin ta ajiye abin a ranta, tana kallon su har zasu fita ta Kalle shi.
“Ko zaki zo?” Kallon su Alman yai kafin ta dauke kai yana basarwa, domin baya jin akwai wani abun burgewa a tare da Alkasim. Bin shi tayi suka fita, tun kafin su yi nisa ta ce mishi.
“Ji mana!” Tsayawa suka yi.
“Yan mata ko zaki bamu wuri!” Kallon  wasilah tayi a wulakance ta ce mata.
“Kece wasilah Ishaq ko? Ai sami labarin ki, baby ba zan iya tafiya ni daya ba,  kayi maza kazo?”

    “Ok gani nan zuwa Aalimah” ya fada a dan kidime, kallon shi Wasilah tayi kafin ta ce mishi.
“Wacece ita?”
“Aalimah yar Boss dina ne”  ya fada yana kallon Yarinyar da bata wuce Rabi’ah ba.
“Ban gane ba yar ogan ka kenan? Koma me kasan yanzun zaman mu anan akwai matsala, ka tura DaÆ™ayyawa maganar mu”

“Gaggawan me kike yi? Idan kika yi hakuri ai abi kome a sannun ko, kawai idan na gama abinda nake zan Miki magana” kallon shi tayi kafin ta ce mishi.
“Kana nufin hmm! Ok” ta fada a hankali, gwanin ban tausayi.
“Idan baki manta ba, ai malam ta ce a cikin alamarin akwai matsala shine nake ganin ko zamu hakur…”

Wani irin murmushi tayi sannan ta kalli Yarinyar da suke tare ta cika fam, sai tsaki take.
“Ok thanks, Allah ya baku zaman lafiya” daga haka ta juya zata tafi Alman ta gani tsaye,  bai ce mata kome ba, dan ya ji abinda suke fada ya fito kamar yana waya ne.

   Tana shiga cikin dakin ya kalli Alkasim ya ce mishi.
“Ji mana!” Ya karasa gaban shi cikin wani irin taku, irin na Gayun da suka isa gayu.

“Wow! Kayi min abinda ya dace, da Kanwar naso, kasan Familyn mu muna kaunar abu me kyau shi yasa muke tattara su, kuma ko baka gaya mata ba, da nasan kai take so da tuni ba gaya mata ai kai kasa mu sadakayalla. So kayi min babban aiki bari ni kuma nayi sharan fagen” ya juya a hankali, ya koma dakin. Yana shiga ya dauki apple ya gutsira. Yana kallon ta.
“Ummyn na samu matar da nake so” .make shi tayi tana faÉ—in.
“Allah ya shirya min kai, amma baka jin magana”

     “Allah da gaske Ummyn wani ya jefar yace baya so ni kuma na dauka nace ina so sai na zama nayi laifi? Gata nan saurayin da take so yace ba yayin ta ni kuma na dauka ina yin ta my souvenir” kunya ce ta kama Wasilah ta shiga ban daki, ta bude ruwa, kallon kanta tayi a madubi, hawaye ne ya shiga zuba mata, shafa Fuskar ta tai tana jin wani irin daci a ranta.

    Tasan lokacin da ta fara karatu, alakar su tayi rauni. Amma ta dauki haka a matsayin daga shi har ita suna da abin yi ne, ba zasu yi wasa da damar su ba, ashe shi ran shi ba. Bata tab’a kawowa a ran ta zai wofatar da ita haka ba, kwalla ne ya zubo mata. Duk da haka basu da uba sama da Alhaji Muhammad a garin lagos dan shi ya bawa Bilal shawaran ya tafi da su,kuka take a hankali tana me dafe kanta, da ciwo a ce mutumin da kake so ya gaya maka baya son ka. Koda yake ai bai gaya mata ba, kawai ta bukaci su yi breakup ne kuma sun yi, yarinyar da ta gani bata kaita kyau da cikar halitta ba, kawai yana ganin tayi karama da ita ce hala.

Buga mata kofa aka yi, fitowa tayi tana goge fuskarta da mayafinta.
“Kuka kika yi? Ko Mazan duniya zasu  ki ni dai ina son ki kin ji yar abata me kayan dad’i”

          “Wannan ba abin wasa bane, abu ne na rayuwa da kuma daidaiton ra’ayi, don Allah ka rabu dani” ta fada tana me wucewa dani” ta fada tana jin kuka.
“Baki yi kama da wacce namiji zai saka kuka ba, me yasa zaki yi kuka yanzun? Karku yi kin ji ki ajiye kukan ki min daren mu na farko”
“Tir da halin ka” ta fada, tana barin wurin.

     Wato tun da Alman ya fahimci, Wasilah ba zata ba shi hadin kai ba sai ya shiga kunyatatta, da cikin jin dadi da nutsuwa, idan zasu fita sai ya kare mata kallo ya ce mata.
“Gaskiya na zaki fita a haka ba, kowa yayi ta kallon kirjina, bayan nawa ne da banza da wofi sun kare min kallo maza canza kaya domin wallahi idan aka yi auren mu hatta aikin nan barin shi zaki yi ki zauna kiyi reno na dan har yau ban fi karfin reno ba”

     Wani kallon banza take mishi ta ce mishi.
“Sai dai na saka ka a cikina. Na sake haihuwar ka.” Baki daya Wasilah ta gama rena Alman, gani take kamar ba wani abin arziki zai iya ba sai shegen cika baki. Kuma babban abinda yake kara daga mata hankali shine Alman akwai shi da farin jinin yan mata, wannan halin nashi ya kara sakawa taji baki daya baki daya ya fita mata a kai.

  Tun zuwan Bilal ya mika Junainah ga jirgin gombe, sannan ya kira Dr Hayat ya gaya mishi gata nan zuwa.

Alhamdulillahi Junainah ta isa gida lafiya cikin nutsuwa,

     **
Busan korea.

Kamar ba zan je Asibitin ba, na daure na shirya kallon kayan jikina nayi ina ji kamar kar na tafi, haka na daure na shirya na nufi waje na gayawa Umma zan tafi Rehab.

      Yoona ya kai ni, asibitin har muka isa. Koda na nufi dakin ta, murmushi nayi mata sannan na ja kujera na zauna ina kallon ta.
“Ya jikin?” Murmushi tayi sannan ta ce min.
“Da sauki yar akuya ya É—an tauren mu?” Murmushi nayi na Kalle ta daga dama har kasa, na tab’e baki ban bata amsa ba na ce mata.
“Da fatan kina jin dadin jikin ki?”
“Dan Ubanki da bana jin dadi zan ki ganni haka?
“Kuma haka ne tinkiya uwar tabele” na fada zan mike ta taso min dukar kafarta nayi, ta fadi zaune riko gashin kanta nayi tare da cewa.
“Don make me angry domin zan karya ki na zuba a kwandon shara lusara” na daket kanta nayi ficcewa ta, bin bayanta tayi da mugun kallo. Sai ta saka Rabi’ah kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button