WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

     “Rufe min baki, bana son munafunci salon a dauka ana Miki wani abu ne” ta fada tare da wurga idanunta, a cikin dakin tana niman abin karyawa.
“Baku yi abin karyawa bane, matsiyaciya ina kayan abincin da aka kawo muku?”

      “Yaya Badamasi ya kwashe tun ana gobe addu’ar bakwai” Ammin su Rabi’atu ta fada tare da sunkuyar da kanta kasa.
“Ah…ah!” Inji Gwaggo Lami, tana kallon Ammin su, tace mata.
“Dama an gaya min baki da aiki sai na kulluwa mutane sharri dama haka kike? Dama haka mugun halin ki yake? Toh Insha Allah sai na gayawa Badamasi”

Da sauri Harirah ta kalle ta, cike da al’ajabi. Toh meye ta fada? Meye mai muni a cikin halinta, kawai daga fadar gaskiya sai ya zama kuskure? Dan haka ya sunkuyar da kanta kasa, tana jin dumin kwalla na zuba mata.
“Toh Allah ya taimaka miki wurin kulla munafunci Allah yana tare da Ammin mu!” Inji Wasilah da ta shigo dakin tana kallon su, dan dama ita tafisu yanayin budewar kai, tana da zafi amma bata da fara’a a fuskarta.

   Mikewa suka yi dukkan su, tare da kallon yar yarinyar da ta gaya musu magana son ranta. Mikewa Gwaggo Lami tayi tare da rufe Wasilah da duka, yarinyar nan bata fasa gaya musu magana ba, domin bakinta yaki mutuwa. Sai da suka mata mugun duka Gwaggo Lami da Yaran ta, suka tafi suka barta gidan tare da janyowa Harirah jafa’in da zai same.

   Suna fita yan uwan suka rufa mata, tare da d’ago.
“Sannun kinji, Karki kuma babu kyau” inji Rahmah,
“Toh haka zamu tsaya muna kallon su suna saka Ammin mu kuka?” Ta tambaye su, tare da ware idanun ta, akan su.
“A’a idan na kuma jin haka sai na sab’a Miki” sake baki tayi tare da kallon Ammin su, cikin tsananin damuwa ta ce mata.
“Kina kuka sannan kin ce kar na kuma magana, matukar baki son nayi magana toh ke ki daina kuka.” Ta fada cikin shashekar kuka, tare da matsawa wurin mahaifiyar su, suka zagaye ta, suna kuka. Kallon su Rabi’atu tayi tana me komawa gefe ta zauna, a kowani dakika sake jin kewar su take ji, gani take kamar zata mutu ne ta bar Ammin su.

     Dan haka ta ware kanta tana kallon su, har suka gama kuka su, sannan suka fara kokarin niman abin da zasu karya, kitchen suka shiga tare da duba sauran gasarar kokon da aka yi kafin addu’ar bakwai, Rahmah ta haÉ—a bakin wuta, ta daura  tukunyar da ruwan da zasu dama kokon, Wasilah da Rabi’atu suka kama wanke wanke, da sauran ruwan da ya rage musu.

      Jamilah ta dauki bokiti domin dibo ruwa.. dake kofar gidan su akwai dan dakali, tana kawo ruwan a kofar gidan tayi kicibis da Yaya Haliru, wanda suke kira Baba. Jikinta ne ya dauki rawa, har ta kusan shigowa zauren gidan, yayi maza ya shiga cikin zauren gidan. Idanun ta ne ya cika da kwalla, jikinta da ya jima da daukar rawa, sai da yayi effect din bokitin ruwan, ya shiga zuwa tana shiga zauren, ya sha gabanta yana wani b’ata rai, yadda jikinta yake rawa yasa shi sauke mata bokitin kan ta.
“Ba…ba… Ha…” Wata sharbebiyar wuka ya ciro, tare da zare mata idanu, sai da ta sake fitsari a jikinta, ilahirin jikinta ya dauki rawa, takowa yayi tare da turata bayan kofar, kuka da tsoro suka hadu a wuri guda, ga jikinta da yake daukar masifar rawa, hannun shi ta ji a cikin rigar ta, tare da matse boons dinta, wanda sanadin zafin da ta ji da ya ratsa ta ne yasata fasa ihu, kifa mata mari yayi, tare da kwashe mata kafa, ta zube ya shiga dukarta, yana fada.
“Shegiya mu zaki lalatawa suna, mu zaki janyowa magana? Ki rasa abinda zaki sakawa dan uwana da shi, sai lalacewa, shegiya me mugun hali.” Ihun Jamilah da kuka ya saka Ammin su ga fito daga cikin dakin ta, tana kallon shi, ya dauki takalmin shi yana dukarta da shi, abin tausayi babu wanda yayi magana har ya gama ya saka kai ya fita, yan uwan suka kawo mata dauki, haka suka dauke ta zuwa dakin su, karshe haka suka kara ruwa akan ruwan zafin kan wuta, bayan an dama kunun. sauran sauran suka juyewa Jamilah tayi wanka da shi. Tunda abin ya faru, Ammin su bata mata magana ba, sai da ta fito daga wanka ta zauna tana shafa mai.
“Ammin mu baki ce min kome ba sai kallona kike, ki min magana wallahi shirun yana jefani cikin tashin hankali”

         Goge kwallar fuskarta tayi tare da dauke kanta, bata san meye nufin Yaya Haliru ba, amma Allah yana gani kuma yana jin su, ba zai tab’a bashi damar cutar da su ba.
“Wallahi Ammin mu, nan aikata kome ba, na rantse da Allah ban yi kome ba” dauke kai ta kuma, suma Yan uwanta da suka ga halin da Yayarsu take ciki ya sa su, komawa gefe suka cure wuri guda suna kuka. Yadda suke kukan shi ya kara d’aga hankalinta.
“Zaku min shiru?” Ta daka musu tsawa, hadiye kukan suka yi tare da mannewa jikin juna,  bata saba ba, ba halinta bane. Sai dai bata da yadda ta iya, Yaranta mata idan bata basu kariya ba, meye amfanin rayuwarta? Idan bata kare su ba meye amfanin rayuwar ta?  Kallon su take cikin matsanancin damuwa. Ta rasa meke mata dadi, ta rasa meye zata yi domin fadawa wata rayuwa da Yaranta, shin zata fita da kanta ne diban ruwa ko kuma zata zauna ne domin kallon su, suna fita wasu munanan abubuwa na faruwa da su?

     Taya zata yi dasu? Me zata iyayi domin kare su? D’ago kai tayi tare da kallon yaranta cikin tsananin damuwa sama da na farko ta yafito su da hannu, da sauri suka nufeta. Tare da rungume ta, suna kuka kamar ran su zai fita,  kasa kuka tai tare da jin kamar zuciyarta yana ci da wuta, wani irin tausayin kan su, da zuciyarsu, take yaushe zata fita daga wannan yanayin, yaushe zasu daina kuka, kukan su ba zai kare ba ne? A hankali tayi ta sumbatar goshin so, tana jin wani irin kuka yana zuba mata, tabbas Yaranta sune kashin bayan cigaban ta, ba zata iya sake da rayuwar su ba, zata bada rayuwar ta domin tasu ta mike gaba.

      Haka suka shafe awa guda, suna kuka kafin ta yi karfin halin cewa.
“Ku tashi mu karya” ta janye Rabi’atu da take barci domin tafi su mugun son jiki, kamar wata Yar baby haka take da zaran taji dumin jikin Ammin su, shi kenan sai barci haka take. Wani irin kaunar Yaranta take ji domin babu abinda take so sama da Yaranta, amma Rabi’atu daban take a duniyarta,  kodan yarinyar tayi karama ne a cikin yan uwanta, ko dan  bata cika walwala bane yasa take kaunar Yarinyar ohho amma tana kaunar ta sama da sauran Yaran, babban burinta shine ta boye kaunar da take mata, domin bata son haka ta shafi rayuwar yan uwanta, bata so ta haifar da damuwa a cikin yaranta.

     Bayan sun karya, suka kuma zama jingum jingum, suna masu shiru kamar babu su a cikin gidan.
“Tunanin me kuka? Ba zaku iya karatun ku bane?” Kallonta suka yi, kafin suka mike zuwa dakin su, tare da dauko littafin islamiyyar,.da ace suna Yan lema ne, da bana Jamilah zata yi saukar Alqur’ani, amma kome ya koma baya ne sakamakon rasuwa mahaifin su da kuma kama shi da aka yi shi ya janyo musu kome na su ya koma baya.  Sunkuyar da kai tayi ganin yadda ita Jamilar take d’aga kannenta,.har suka jima ita kuma tana saka Alqur’anin domin karatu, sai kuka ne ya kwace mata. Kuka take tana kallon su. Kafin ta rarrafa jikin Ammin su.
“Ammin mu don Allah ki mai damu makaranta”  jikknta ne yayi kuma sanyi, a hankali ta d’aga karkashin katifar dakinta, ta zaro kudin da ta samu na sadakar da abokan marigayi suka had’a mata, ta kalli kudin sosai ta kirga kudi ne me yawan gaske,.dan haka tace musu.
“Idan Allah ya kai mu ranar Monday sai ku kira min Ammar yazo ya kai ku makarantar kota gwamnati ne zai fi zaman haka, islamiyyar kuma tunda akwai ana kusa sai ku shiga.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button