WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Nan ma waya suka yi.
*
Abuja

Office din Jakadar Nijar.

Ministan harkokin waje da Hanan, ne a zaune.
“Kayan mu suna iyakar Nijar da Benin, jama’arku sun hana a shiga da shi meye haka bayan kasan akwai yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin mu”

Shiru Jakadar Nijar yayi kafin ya ce.
“Kasan cewar Æ™asar mu akwai tsaro da kuma bin doka, dan haka zamu bari a wuce da su, amma abisa kafada da kafada, domin akwai mutanen mu da suke son shiga Libiya.” Kallon hammad Harissu Hannah tayi kafin tace Mishi.
“Zamu baku damar haka, sai dai bamu da tabbacin zasu samu wadataccen wurin zama, amma babu damuwa” daga haka ta mike tana gyara zaman jakarta.
“Zauna mana ranki shi dade, an gama magana”
A take aka kira shugaban tsaron nijar aka yi magana da shi, shi kuma ya tura zancen zuwa ga ministan harkokin waje, shi kuma ya tura ga ministan tsaron, take aja basu samar shiga nijar.

Wannan shine tsarin shiga da fita idan aka dibo mutanen da zasu shiga ta wata ƙasa, sannan suna da kyakkyawar connection ga kowata kasa, idan har baku amince da kudi ba, sai su ma su bada mutanen su, a shiga dasu wata ƙasa. Abin sai ya koma kasuwanci. A cikin tafiyar har da yan tawayen da zasu shiga wata kasa, akwai masu Safaran kwayoyi, da  bindigogi ana smug din din su zuwa wata nahiyar da bata da yawan su.

..
Niger Republic
Sun samu shiga garin nijar, can wani gari me suna Tahua, anan suka sauka a tashar.

   Motar JF Transportation, suka bude kowa ya fita bayan an huta sannan suka fara kokarin bawa kowa abinci, sai da suka ci kafin aka fara tattara masu passport.

Muna gefe ni da Aunty Blessing, ta kalle ni sannan ta ce min.
“Yanzun kuma zamu fara tafiyar da hatsarin ta kadan ne, sai dai kuma idan muka yi dace mu shiga nan da sati biyu mu.tsallaka Libya idan kuma  motar bata sauri mu shiga nan da sati Uku zuwa hudu.”

   Shiru nayi ina kallon ta, kafin na ce mata.
“Yanzu baki É—aya idan aka hada tafiyar mun yi tafiyar wata daya kenan?”  Gyada min kai tayi tana kallona.
“Kin gaji ko?” Girgiza kai nayi sannan nace mata.
“Naga dayawan mu kamar basu san da tafiyar ba” girgiza kai tayi tare da cewa.
“Eh toh wasu sun san da tafiyar, wasu kuma sun san da tafiyar, kamar mazan nan su niman kudi zasu, sai da suka biya kudin su, ku kuma dama can tafiyar ku a shirye take”

“Kamar Ya?” Girgiza min kai tayi tana kallon yadda nayi tsuru tsuru,
“Ƙarki ji tsoro!”. Ta fada bayan ta mike, riko hannuna tayi muka shiga zaga cikin tashar, muna cikin tafiya wasu mota guda goma sha tara suka shigo kiran Hilux 4×4, suka shigo.

**
Abuja

STEVEN

Yau kwana biyu kenan hankalin shi baya kwance, saukar shi daga jirgi ya kalli Obinna da yake dauke kan shi.
“Ban gane ba sai dauke kai kake?”
“Babu” inji Obinna,
Karban jakar Steven yayi suka nufi cikin arrive yake, suka fita baki daya jikin su dukkan su a mace yake.

   Sai zaman ya gundure shi har suka isa gida, tun daga kofar gida yake rana idanun shi ko zai ga Rebecca amma bai ganta ba, har ya shiga cikin gidan.

   “Mama na dawo” fitowa tayi tana kallon shi ta fashe da kuka, ta zauna a hankali tana cewa.
“Steven mun rasa Rebecca ta b’ata”  ta gaya mishi, da tasan abinda haka zai janyo mata da ko a mafarki ba zata gaya mishi ba,.kawai kura mata ido yayi kafin ta kuma bude baki tayi magana sai ganin shi suka yi ya zube a kasa babu numfashi.

Haka Obinna suka kwashe shi sai Asibiti, dake cikin unguwar su,aikuwa likitoci suka rufa mishi tare da kokarin ceto rayuwar shi.

**
Daƙayyawa .
Wata motar Bus ce ta isa gidan me gari, bayan ya tsaya. Driver ya fito suka gaisa da jama’ar me gari,
“Malam daga ina kake?” Malam Nasiru ya tambaye shi.
“Daga Kano nake, an bani aika ne na kawo garin nan gasu nan a cikin”

        Mikewa yayi ya bude motar a hankali kayan yaran su da aka tura birni aikatau ne, wasu babu labarin su. Ya ajiye musu tare da cewa.
“Gashi wannan kuma wasikar daga mutumin da ya bani aikan ne”
Karba aka yi, sannan ya wuce abin shi.

  Duba sunayen Yaran ake har aka samu na Rabi’atu.
“Allah ya taimaki me gari gana Rabi’atu mun samu”
“Ku buÉ—e muji Meye yake ciki.”

“Toh”
Ba wani labari bane mai dadi! Kawai zamu sanar muku ne Rabi’atu ta mutu sakamakon gobaran da gidan aikin ta suka yi sauran Yaran kuma zasu dawo idan lokacin haka ya tabbata

Shiru wurin ya dauka, kowa da abinda yake damun shi, dan haka aka fara kokarin niman na sauran Yaran, abin tausayi wasu babu labarin su har abada, sakon Rabi’atu ne kawai aka samu labarin mutuwar ta, a take wasu suka nufi gidan Badamasi aka gaya mishi abinda ya faru, shi kuma ya tafi ya sanarwa yan sanda, aka kira Aaman aka sanar mishi.

**
Lagos

Alhaji Muhammad Lawal Dambatta da kan shi ya shiga gidan da Iyalin shi, suka gaida Ammyn, sannan suka yi shiru kafin ya gyara murya.

“Hajiya Harirah, ina me baki hakuri akan abinda ya faru, da kuma wanda zan baki labarin faruwar shi.” Yayi shiru kafin ya ce mata.
“Kuyi hakuri Allah yayiwa Rabi’atu rasuwa sakamakon hatsarin gobaran da ya kama gidan da suke”  shiru tayi kanta a sunkuye tana jan casbin hannunta, kafin ta d’ago kai ta ce musu.
“Alhamdulillahi! Innalillahi wa inna alaihil raji’un allahumma ajirni fii musibati wa’akhlifni khairan minha. Allah ya gafarta mata yasa ta huta” ta fadi haka ne kawai amma zuciyarta bata yarda Yarta ta mutu ba, jikinta bai bata Yar ta mutu ba,babu laifi idan aka ce ta b’ata amma mutuwa,hmm bata yarda da ba, sai dai ba zata iya musanta musu ba, domin sun mata kome.  Haka suka yi ta rarrashin ta, cikin juriya da hakuri ta ce musu.
“Babu kome” sannan suka mata sallama, tare da barin gidan. Jamilah ce ta fito a daki, tashinta Kenan daga barci, Rahmah da Wasilah, sun tafi islamiyyar da take babban masallacin unguwar.
“Ammyn mu lafiya” ta tambaye ta, bayan ta zauna. Hawaye ne ya xubo daga idanun Ammyn ta ce mata.
“Allah yayiwa Rabi’atu rasuwa ne, sakamakon gobaran da ta tashi a gidan aikin ta.”

Wani irin kuka ne ya kwace mata, sai da tayi sosai har su Wasilah suka dawo aka gaya musu, suma sun sha kuka tare da kewar Yar uwar su.

    Baki daya sai suka zama abin tausayi da rashin son magana a tsakanin su, idan ma zasu yi akan Rabi’atu ne.
*
Abuja

Sai da ya kwana ya wuni kafin ta buÉ—e idanun shi, ya sauke akan Maman shi.
“Rebecca ba zata iya fita ko ta gudu ba, domin nace ta jirani ina kuka kai min ita?” Ya fada da Æ™arfi bayan ya tashi daga kan gadon yana cire abubuwan da suke daure a jikin shi.
“Please ka kwanta baka da lafiya, don Allah kar ka ce zaka tashi”
“Da kin damu da halin da nake ciki ba zaki na cutar da Yarinyar ba, Mama ina Rebecca?”
“Kayi hakuri karka ce zaka tashi” ta fada kamar zata yi kuka,
“Ina kuka kai ta? Dama kin shirya tafiya ta ce dan ku dauke ta? Ki gaya min ina kuka kaita”

   Jikinta a matukar sanyayye bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba ta ce mishi.
“Mun sayar da ita ne dubu dari bakwai da hamsin” kura mata ido yayi. Bai san lokacin da hawaye ya zubo mishi ba,ya kura mata ido.
“Mama kika sayar da dan Mutum dubu dari bakwai da hamsin?  Baki daya babu imani da tausayi ina za akaita? Waye ya saye ta.” Cikin shashekar kuka bata ce.
“Idan aka sayar da su Italia za a tafi da su, a can zasu” kasa magana tayi tana kallon shi, sabida yadda ya rintsa idanun shi yana me dakatar da abinda zata fada.
“Thank you Mama,da Kinsan me yasa na damu da Yarinyar ba zaki tab’a aikata haka ba, da kin san me yasa nake son zama da ita ba zaki kashe ni ba, shine kuka sayarwa yan trafficking Yar mutane, ina kaifinku mai da ita inda kuka dauko ta,.shine gatar da zaku min amma ki sani na rabu dake kenan Har abada, sabida Yarinyar itace farin cikina,ba wai ina son ta bane amma ina jin farin cikin idan ina tare da ita, shine kuka sayar da ita,.Mama idan kika ce min kar nq tafi da ita xan iya hakura amma lokaci guda ku kashe min rayuwa….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button