WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

A yan kwanakin da suka biyo baya, raina yana yawan É“aci, amma haka nake daurewa wanda ba kowa yake haddasa min haka ba sai Yomi duk yadda naso kar na kulata sai da raina ya kai na mata shegen duka. Tare da targad’a mata hannu, ina rike da hannun ta ya shigo tun ranar da ya bani rigar shi, ban kuma ganin shi ba sai yau cikin masifa nace mata.
“Gaya min Meye nayi miki?”
“Sake mata hannun” cikin fushi na juya gare shi ina son zan bal-bale shi. Cika min ido yayi ture ta nayi, cikin fushi na bar wurin.

Kallon Hajiyar shagon mu yayi tare da cewa.
“Ki sallame ta, xan bata aiki tunda nan babu zaman lafiya, kuma fuska ce ta jama’a”

   “Amma ita din tafi su matsayi a nan domin Hajiyar Babba tace a kula da ita sosai” murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Nima karambanin nayi Kin san Biyu Bilal ba zai dauke ta aiki ba, kawai Æ™oÆ™arin ta da kuma yadda take kare kanta yasa zan bata koda goge goge a cikin kamfanin mu”

        “Toh Alhaji Faisal, an gama ya jikin shi Alhaji Bilal din, a gaishe shi.”
Fitowa nayi a fusace.
“Toh Yan mata zo muje yawo” kara bata rai nayi, sannan na fita biyo bayana yai ya bude min motar shi, kamar ba zan shiga ba, sai na shiga.

      “Kiyi wurin taron jama’a bai da ce ace kina fada ba, ko kina son wata rana a miki gorin fada ne?” Kallon shi nayi tare da dauke kai na ce mishi.
“Kuma dan na kwaci kaina sai a ce ina da faÉ—a?”
“A’a ai nima abinda na gaya musu kenan”  ya fada min, tare da bani hakuri.
“Ke Yar wani gari ne?”
“Ni yar garin nan ce mana” na fada mishi a takaice.
Shiru yayi yana ta tukin shi, park ya kai ni.
“Me zamu yi anan sai kace wata yarinya karama” na fada ina kallon shi,
“Have a fun” shiru nayi ina kallon shi, kafin na sunkuyar da kaina, zuwa yayi ya biya Bill din wurin tare da sayo min, ice cream da popcorn. Ya nuna min wani wuri muka shiga tare da niman wuri muka zauna.

  A hankali na fara cin popcorn din ina kallon yadda yara suke farin cikin su. Sai na tsinci kaina da ture abincin. Na mike batare da na ce kome ba.
“ina zaki?”

“Gida” na fada ina tafiya.
“Toh abincin ki fa?”
“Na koshi.”
“Akan me?”
Shiru yayi kafin nace masa.
“Duk yaran suna farin cikin, Kalle su da iyayen su suke farin cikin su, waye ya damu da Maraya yayi farin ciki? Waye yake son farin cikin Maraya? Su din ba mutane bane? Ko su din ba ansa da zaman su bane? Wallahi bana jin yunwa a duk lokacin da zan tuna akwai yaran da suke buÆ™atar cin abinda na ci”

“Ok toh muje ki zauna a mota ina zuwa”  kai ni wurin motar yayi ya bude min na shiga, kafin na ce mishi.
“Rigar ka na manta da shi a gida zan kawo maka gobe” murmushi yayi sannan ya koma cikin park din ya sayo abubuwan da ya saya min, sannan yazo ya zuba kafin ya koma ya amso wanda na fara ci.

         “Ina zan kai ki” murmushi nayi bayan na amshi kayan hannun shi.
“Gidan marayu mana” da sauri ya kalle ni.
“Ban yi kama da marayu bane? Ko nafi da cewa dama yar da take da iyaye ko? Duk abinda zaka yi tunani akan shi kawai kayi tunani akan me kyau.” Ya ja motar shi, haka muka isa har gidan da kwatancce, muna isa na kwashi kayan na shiga cikin gidan da shi.

   Da gudu yara suka zagaye ni, kan shimfida na kai kayan, na ajiye na kuma juyawa zan fita ya shigo da kayan, kallon yaran yayi na amshi kayan, na zauna a tsiyar su. Na shiga bude kayan ina cewa.
“Kunga ga uncle din da ya saya mana kayan dadi, dan haka kuyi mishi addu’a, ruhin shi ta zama me tsarki da salama”  tashi Nunu yayi yana lallube Yallabai Faisal.

      Kallon shi nayi tare da mishi magana da ido, karasowa yayi tare da kallon Yaron ya durkusa a gaban Yaron. Rike hannun shi Yallabai Faisal yayi. Yaron ya shiga jikin shi.
Kwantar da kan shi yayi a daidai zuciyar shi. Yayi shiru bani manta lokacin da nazo gidan sai da yayi min haka, sannan ya ce musu.
“Aunty ba zata cutar da kowa ba ita kamar sako ce a gare mu” murmushi nayi ina kallon su, d’aga kan shi yayi tare da niman wuri ya zauna.
“Alyuda kawo kai da Nunu ne”
“Aunty” Nunu ya kira suna na,
“Na’am Nunu” fuskar shi kamar zai yi kuka ya ce min.
“Aunty wannan uncle din zuciyar shi ta rufe da wata! Kawai yana miki kirki ne amma babu kome a cikin zuciyar shi sai wata” kallon Yallabai Faisal nayi, ina dariya.
“Kaji ba!, Nunu bai babu abinda yake tsakanin mu sai alkhairi karka damu .”  Haka na gama raba musu har da nawa ma.

Mikewa yayi zai tafi na bi bayan shi.
“Nagode sosai”
“Babu kome, kiyi hakuri ban gaya miki bane ina da mata da bamu jima da aure ba, kin ganta” ya bude min wayar shi.

A hankali nake kallon wayar kafin kafin na kalli hotunan su.
“Muna kama da ita”
“Shi yasa nake ta bin ki, kuna yanayi da mata ta tun ranar na gaya Miki ai”
“Eh yanxun kan na yarda” 
“Sai gobe ko”
“Dan tsaya mana” ba fada tare da shiga cikin gidan da gudu, can sai gani da kayan shi, mika mishi nayi.
“Da kin bar shi”
“A’a wallahi Nagode! Ba dan kai ba, ai da kimata ta zube a ranar”
“Nagode sosai nima” haka ya wuce shiga motar shi ya tafi.

Nan na shiga na samu yaran na kwanta a tsakiyar su,, suma  ni muka shiga hira, kamar ba gobe. Idan ina cikn su mantawa da kome nake.

Lokacin da ya bar gidan marayun, asibiti ya wuce wurin Bilal, amma bai shiga ba, sai da ya fara shiga wurin Ammyn.

“Assalamu alaikum, Ammyn ya jikin ki?”
“Da sauri sosai, an samu canji”  ta fada tana kallon Rahmah, da take ta dauke kanta daga shi.
“Baki ga mijin ki bane?” Tura baki tayi tare da cewa.
“Na gan shi Ammyn ya duba wayar shi miss call nawa na mishi?”
“Toh Allah ya baki hakuri, wallahi wayar tana silent ne”
“Ok” ta fada tare da nufar ban daki,

   “Kayi hakuri, kasan yarinya ce don Allah kar ka hukuntatta da halin ta” murmushi yayi tare da da cewa.
“Babu kome Ammyn”  shigowar Wasilah da Jamilah yasa shi kallon su, kafin ya wuce dakin Bilal.

Inda ya samu su Ummin aka bude hira, bayan fitar shi kuwa Ammyn ta saka Rahmah a gaba da fada da nasiha, har sai da ta tura mishi text message. Sannan ta bawa Ammyn hakuri.

“Auren kenan fa, shi yasa lokacin da aka hana mutum yake ganin kamar kashe mishi rayuwa aka yi nan kuwa yancin ake nima mishi”
“Ai tafi wasu matan da suke bin maza kamar jela, suna bin namiji yana wulakanta su. Sai kace jakuna” inji Wasilah.
“Ke ina wasa dake? Yar iska mara kunya” murmushi Wasilah tayi mata sannan ta ce mata.
“Bani da lokacin ki, domin baki daya baki san ciwon kan ki ba”

“Ya isa haka, zan saba muku.”

**
“Taya za a yi ace asibitin ma an samu wanda ya kare su?” Ya fada cikin matsanancin fushi da bori.
“Karka manta Bilal ba kanwa lasa bane, kuma ko harin da aka kai mishi ranar Sa’a aka samu akan shi. Dan haka kar a kuma na biyu, idanun duniya tana kan shi”

“Toh sai na ga karshen shi, Insha Allah”

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/5/22, 18:28 – Nuriyyat: 58

Washi gari

Wurin aiki da wuri, ina kokarin cire kayan jikina, Hajiyar mu ta ce.
“Ai na sallame ki.”
“Yaushe? Akan me? Meye nayi miki?” Duk lokaci guda na antayo mata da tambayoyin sai da ta kura min ido,kafin ta ce min.
“Kawai Bama bukatar ki ne a nan”
“Kiyi hakuri idan dan laifin da nayi ne ba zan kuma ba”
“Ya wuce amma ba zaki zauna a nan ba” ta fada min haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button