WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin gajiya da shirme ya ce mun.
“Muje” fita muka yi bayan ya kwashe kome, muka bar asibitin.

“Ba dai an sallame ni ba?” Na tambaye shi ina tsalle da juyi, girgiza kai yayi. Sannan ya ce min.
“Koma ki tambaye su”
“Ina ba bukata, ina farin cikin na fito daga jahannama ka mai dani, ai yau kwanan gidan mun ya kama ni”

Tsaki yayi tare da da yin gaba,da gudu ba sha gaban shi,  ina dariya na bude baki xan yi magana sai gani nayi ta watsar da……🔥🤔 What is going on….

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/8/22, 08:24 – My Mtn Number: 63

Wani irin fisgo ni yayi na fada kirjin shi jikina yana rawa, da gudu motar ta wuce.

“Are you okay?” Ya tambaye ni, gyada mishi kai nayi, ya janye ni daga jikin shi yana kallon yadda jikina yake rawa, kwashe kayan yana kallona.
“Kin tuna abinda ya faru ko?” A raxane na Kalle shi.
“Ni kan ka kai ni gida”
“Toh zan kai ki” ya fada bayan ya tsare abun hawa, ina shiga motar na fashe da kuka.
“Ina son ka kaini gida”  bai ce min kome ba, har muka isa airport bamu huta ba, muka bar kasar ban san ina ne saka a kai mu ba, amma baki daya,  bakina ya mutu. Saka abu yayi a kunnen shi yana me lumshe idanun shi. Bayan awa biyar muka sauka a garin da ban san ko ina ne ba, muna fitowa a jirgin na shaki wani irin iska me masifar sanyi, har cikin kashin jikina nake jin iskar, ganin ina rawan sanyi yasa shi cire sweater coat din shi ya saka min sai lokacin na lura da ai iya mune a cikin jirgin tura baki nayi na ce mishi.
“Ina ka kawo ni?” Kallona yayi kafin ya cigaba da Tafiyar shi. Muna shiga cikin airport din, naga wasu kartin maza. Suka shiga gaida shi, sai bin shi nake. Ina kallon airport É—in.  Yana gaba suna take mana baya, har waje.

Motar da ya shiga ya bude min na shiga, ina cewa.
“Nan China ka kawo ni?”
“A’a sayar da kanki Nazo yi idan aka yanke sai a cire min bakin ki sabida ya cika magana” wani kallon renin hankali na mishi na ce mishi.
“Tab’a ba zan yarda ba” share ni yayi, kallon shi nayi ma dauke glass din motar na ce mishi.
“Gaskiya garin ku a kwai dad’i, sai dai sanyin su”  na fada ina kallon shi,  tab’e baki yayi har muka isa da wani estate, kallon unguwar nayi. Rufe glass din motar yayi. Sannan ya ce min.
“Na lura bakin ki bai da birki, idan kika sake baki kama shi ba, sai na zane ki domin nan gidan mu ne”

“Toh idan akayi abin magana wallahi sai nayi” na fada kasa Æ™asa. Murde min kunnen yayi yana faÉ—in.
“Idan baki iya bakin ki ba zaki sha wahala a hannuna”  ya fada min lokacin ba muka fito daga motar.
“Allah sai ya saka min” babbar mace ce ta iso wurin mu tana gaida shi, ya ce mata.
“Ga bakuwa ki wuce da ita cikin gidan gani nan zan duba kaka ne” 
“Toh yallabai” ta nuna min hanya, bin bayan shi nayi da Idanu, sannan na bi bayan ta har cikin katon falon da yake gidan.
“Lim shin ina Oppa” suka tambaye ya baki daya.
“Yana can wurin babban mai gida.” Ta basu amsa.
“Wannan fa?”
Suka tambaye ta,
“Tare suka zo.”
“Barka da zuwa Rubi, zo nan Dota na. Duk wanda zai kare Gong Yoo kamar rayuwata ya kare. Zo nan”  na jima da kewar mahaifiya, dan haka na isa gare ta, rungume ni tayi tana cewa.
“Mun gode da sake taimakon Matar Faisal da cikin jikin ta.” Murmushi nayi na ce mata.
“Is my pleasure” na fada mata,

       “Allah yayi Miki albarka”
..
A waje kuwa kallon kakan shi yayi tare da cewa.
“Gani nan nazo”
“Yawwa Sannun kaji, wannan lokacin ana Niman dan takara ne nace bari na maka magana.” Zama yayi tare da zuba ruwan zafi a kofi ya kurba, sannan ya cewa kakan shi.
“Ga Park Yun me zanyi kuma? Can ma ana bukata na, shima jikanka ne zai iya abinda ba zan iya ba, sannan kuma zai kasance jinin kasar Mutanen busan ba zasu guje shi ba, Ni kuwa dayawa zasu kalubalenci mahaifina ba dan kasar bane ka fahimta.”

  Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Ka gama magana, jeka zan yi magana da kawun ka shi zai wakilta ba dan shi ba.”
“Nagode kaka”
“Ka samo Yarinyar?”
“Eh na samu wacce ta taimaka min da nayi hatsari amma wancan ta Paris ban same ta ba”

” Kayi hakuri zaka same ta kaji”
“Toh kaka” ya fada tare da mikewa ya nufi cikin gidan.

Yana shiga ya samu ana Umma tana ta ina ina da ni.
Tabe baki yayi yana faÉ—in a ran shi.
Kuna ta damun kan ku akan magananniya

Sai da ya zauna suka gaisa, ni kuma na koma kamar mutuniyar kirki, sai wani sunkuyar da kai nake irin babu ruwa na din da wata Uwar harara ya wurga  min, sannan ya cewa Matar.

“Ummin ta koma ko?”
“Eh ka shiga ciki ka huta. Itama NaNa kaita dakin baki ta huta sai tazo ta ci abinci” kallon shi nayi na d’age mishi gira, dauke kai yayi yana kallon ta kusa da shi sa take bashi labari.
“Oppa baka tambayi Mimih ba tana school”  kallona yayi tare da harara na, har muka kusan kullewa na juyo na mishi gwalo.

   “Mahaukaciya”
“Me?”
“A’a bari na huta”

    Tun daga nan ban kuma jin zuriyar shi ba sai dare, shima naga da wata Black Beauty budurwa suke hira, zan ce ita ce take hiran shi kan hankalin shi na kan abincin da yake ci, ina zuwa table din na zauna a kujeran da yake kallon shi. D’ago kai yayi zai magana na kashe mishi ido daya, kafana na daura akan gwiwar shi. Ina d’aga mishi gira. Kwarewa yayi, da sauri na daura shiga shafa kafar shi, kura min ido yayi duk da sun bashi ruwa amma, naji dadin abinda nake mishi.
“Sorry” nafada ina rike kunne na,
“A ina ka samu mahaukaciya haka?”
“A garin mahaukata” ya bata amsa, kallon ta nayi, sannan nace mata.
“Yar me kyau na zata baki ita Hausa bane sai Yaren nan, toh ai ta baki amsa Meye na kallona kuma” 

   Kallon Maman shi nayi, na ce mata.
“Mama. Abincin nan yayi dad’i Allah ya riko hannun ki”
“Amin Rebecca” mikewa nayi na fito waje, ina kallon yadda sararin samaniya tayi kyau.
“Ban gane ba? Kana nufin ma’aikaciyarka ce ka dauko ta har nan? Oppa wallahi babu zancen ma’aikaciyarka sai dai masoyiyarka”

Wuce ta yayi tare da inda nake. Kallon shi nayi, yana zuwa ya kame kunne na ya Murda.
“Zaki sake? Wai ma shekarun ki nawa?”
Cikin yardar hannu nace mishi.
“Goma sha shida da watanin shida”
“Shine kike min abu kamar wacce ta san kan bariki? Idan kika kuma sai na zane ki kawai mara jin magana”. Ya sake min kunne, sai da na bari ya juya zai tafi na yanka a guje na É—anne bayan shi ina cewa.
“Wayyo Allah na rama nima na rama” na rufe mishi idanu, kamar zai yi Hauka haka na manna mishi ita kuwa tana kallon mu ta kasa yarda ma’aikaciyar shi ce ko yar reno ce domin abin ya fi kama da renon yarinyar yake.

Fisgo yayi sai da kashin hannu na yayi kara, kura mishi ido nayi sabida zafi da radaddin da ya ziyarce ni, amma ban yi ko ihu ba, wani abu na daban nake hangowa a cikin idanun shi. A hankali ya sake hannun sakamakon kwallar da ya zubo daga cikin idanuna, goge min yayi tare da riko daya hannun muka fita parking lot muka nufa da kan shi ya ja motar har wani babban asibiti aka duba hannun. Kamar Ya cire ciwon ya mai da jikinsa.

“Sannun da zafi ko?” Gyada mishi kai nayi ina wani irin tsayar da kwallar da zata kuma gigita shi, ai kuwa kamar abinda yake son gani kenan sai gashi yana rikicewa har yana gaya musu su yi a hankali kar su ji min ciwo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button