WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   Da suka gaya mishi labarin hauka yayi musu a gidan, sannan ya bi wasilah har wurin aikinta, ya tattaro ta suka fito. A mota ya watsar da kayan ta.
“Shiga kafin na nuna miki yadda nake!” Ya fada da mugun karfi, riga-kafin soja ya motsa, shiga tayi babu musu yana shiga ya fisgi motar a guje sai balai yake har suka isa kofar gidan shi, horn daya yayi aka bude mishi, yana shiga ya fito da sauri ya bude kofar ya fitar da ita, ya shiga janta har cikin gidan, yana shiga da ita ya cincibota yai dakin shi da ita, wani irin tsoro ne ya mata, lokacin da ya wurgata a gadon ya shiga cire kayan shi yana me fisge karamin hijab dinta, baki daya ya Haukace.
“Idan na miki haka zaki zama tawa har abada, idan ba haka ba mutuwa zan yi da sonki” bayan ya farke rigar jikinta ya hana kokarin hada jikin shi da nata, kifa mishi mari tayi sai da ya dauke wuta.

“Meye nufin ka?  An ce maka ni irin sauran matan da kake lalata musu tarbiyyar ne Alman, ai nasan waye kai shi yasa gwara na auri wancan da baya sona akan na aure ka kai da kawai sha’awata kake ji? Da zarar ka damu jikinka ya shiga jikina ks gama dani. Shi kuma yaso ni tun bani da boons tun kirjina babu kome ban ga laifin shi dan yace baya sona ba. Kana tsammani ni kamar Rahmah ce ta ta fada soyayyar dan uwanka lokaci guda? Baka tab’a burge ni ba asalima bana sonka tun daga lokacin da na samu labarin abinda kayiwa little sister na tsane ka har abada, sauka a jikina sakarai” ta fada cikin kwarin gwiwa. Janye jikin shi yayi, sannan ta sauka ta dauki rigarta ta kalla sannan ta . Saka kai zata fita ya ce mata.
“Kiyi hakuri ina son ki wallahi ina son ki”
Bude drower din shi tayi ta dauki wata shirt din shi ta saka sannan ta fita daga dakin, kamar ya fasa ihu haka yake ji, murmushi tayi sannan ta fita daga gidan baki daya, a karon farko na rayuwar ta da taga wanda ya yi Confess din love din shi akan ta. Haka ta isa gida, amma kuma idan ta tuna abinda yayi niyyar mata sai yaji kuka yazo mata, har ta shiga cikin gidan nan ta samu labarin da ya kuma kara mata kukan ta. Shi yasa yayi ƙoƙarin mata haka ashe abinda ya faru kenan.  Toh ya zata yi Alkasim take so tun bata san ciwon kanta.  Yau an wayi gari shi da kan shi yake cewa baya sonta.

    Bayan fitar ta shima fita yayi ya nufi gidan Alhaji Muhammad Lawal. Bayan ya gaishe ya zauna a gaban shi.
“Alhaji nazo ne akan maganar Wasilah. Alhaji ni namiji ne kaima namiji ne, karka manta yadda kiyayyar namiji yaÆ™e, Alhaji Muhammad ina son Wasilah, idan ka bani ita xan yi farin ciki kuma zan yi hakuri da kiyayyar ta, Alkasim baya sonta yana da wacce yake idan ka bani zan iya hakuri da kiyayyar ta, amma bai zama dole ka bani ba amma ina sonta.”

“Kayi hakuri bana magana biyu” inji Alhaji Muhammad Lawal Dambatta.
“Alhaji nayi maka alkawarin za a saka auren da Alkasim amma ni zan kasance a tare da ita har zuwa mutuwa ta, domin wallahi zan sace ta na tafi da ita inda xa a aura min ita” yana gama fadar haka ya fita, murmushi Alhaji Muhammad Lawal yayi domin yana son ganin mutum me matuÆ™ar kwarin gwiwa, bari ya gani me yaron zai yi.

   **
Bayan sati biyu.

Yau yake son bin jirgin dare zuwa Seoul, dakin Hajiya Humaida ya shiga ya zauna yana kallon ta yadda aka saka mata bututu a wuyarta, tun wancan satin aka sake Hajiya Turai, zama yayi yana kallon ta. Mika mishi hannun tayi cikin damuwa tace mishi.
“Don Allah ka auri Mimih zata samu kulawa sama da kome don Allah na baka ita tun ba yau ba”

    “Hmm! Ina da wcce nake so ba wai zan iya boye miki bane, amma ina da wacce nake so har an yi maganar mu da ita.” Kwalla ne ya zubo mata sannan ta ce.
“Don Allah Bilal” mikewa yayi tare da cewa.
“Ba zan cuci kaina ba” ya fada tare da barin dakin.

     Sai dai ta kudiri Aniyar sai ta aura mishi Mimih koda wancan matar da zau aura zata mutu, kamar yadda sauran suke mutuwa, dan Bilal na Mimih ce, shi yasa tayi ta kashe matan shi, ana zata Shuwa ce. Murmushin mugunta tayi, domin ta yanke hukunci, kuma ya kan ku.

   ..
Dakin Ummyn ya isa suma suna hada kayan su.
“Yau sai Korea?”
“Inshallah” ya fada yana taya Liyanah da take tattara kayan Faisal ya fita da su.
“Ban ga Alman ba?”
“Ka bar sakarai wai yana ta Rigima ne an ci amanar shi, an hada kai da a raba shi da Wasilah”

Dariya suka saka mishi.
“Ummyn da gaske yana sonta, domin ban tab’a ganin yayi magana yana son wata mace haka” inji Bilal,
“Eh nasan yana son ta, amma ita ai bata son shi, kuma idan na ce zan yi magana kamar ban mata adalci bane domin ita kamila ce, shi kuma kowa yasan Alman da maganar mata,.barta ta auri wanda zai rike ta.”
“Amma shi Yaron baya sonta!”
“Zai sota nagartaciyar yarinya ce.”
“Shikenan Ummyn”

Haka suka fito inda suka samu Alhaji Abubakar.
“Kin toh ya jikin naki?”
“Alhamdulillahi. Zamu raka Bilal ne airport”
“Allah sarki, ka gaida mahaifiyarka ka kuma rokon mana yafiyarta”
“Babu kome”

Yana fita ya samu Faisal yana son yayi mishi magana amma akwai Ummyn a wurin, sai da suka isa airport, nan suka kebe.
“Khalil ya bar gidan, kuma yaki zuwa kotu me zamu yi?”
“Kyale shi halin shi zai kashe shi” daga haka ya wuce abin shi
3/17/22, 09:10 – My Mtn Number: 84
“Bilal” Faisal ya kira sunan shi a hankali, juyowa yayi yana kallon Faisal.
“Don Allah ka kula da Rabi’atu wallahi ita ta dace da kai ba wasu ba, don Allah kayi hakuri da ita, kai kafin dacewa ki bata duk wani kulawa, kayi hakuri a matsayina na Mijin Yayarta nake magana kuma Ina ji kamar Kanwata ce ciki guda muka fito, don Allah tana buÆ™atar farin ciki kome kankantar shi.”

Kallon Faisal a karon farko a rayuwar shi da Faisal yayi mishi magana kamar babban mutum.
“Insha Allah surikina, sai dai kanwarka tana da zafi ne, idan aka cigaba da haka sai iya barna” ya fada yana murmushi.
“Karka damu nasan da haka, amma ai ba zaka iya cutar da ita ba, a lokacin da ya dace kayi baka yi ba, sai yamzun a rana tsaka? Kana da NaNa da Seyo Na ba zaka iya ba nasan Waye Bilal.”

Juyawa yayi yana faÉ—in.
“Ban da Rabi’ah, domin zafin ta yana yawa shi yasa zan kaita huso Women University ta fara karatu kafin na daidaita kome sai na dawo ayi maganar bikin mu, amma yanzun bana son ta sani”

     Takowa Faisal yayi yana faɗin.
“Na gargadi Rahmah da Wasilah, kuma nasan zasu iya shanyewa”  juyawa Bilal yayi suka kara musabaha, sannan ya wuce tare da nufar filin jirgin, Faisal yana bin shi da ido, wani irin kaunar Bilal yake kamar me, shi din kamar Zakin kariya ne ga Ahalin su baya Korea baya Nigeria. Idan yana abu kamar wani sarki he look like king not Prince. Domin shi yarima bai da ikon kare al’umma amma sarki fa? Murmushi yayi tare da cewa.
“Long life My King” har ya juya zai tafi sai ya kuma juyowa ya d’agawa Faisal hannun.

   Wannan kaunar su ta wuce yadda ake tsammani. Haka yasa shima Faisal ya d’aga mishi hannun. Har ya shiga cikin jirgi. Faisal yana tsaye har jirgin su ya tashi. Sai da yaga tashin jirgin sannan ya juya ya tafi. Yana barin cikin airport din Thomas ya kira shi.
“Barista mun kama Khalil”
“Ku kyale shi amma ku saka idanu akam kowani motsin shi, domin zai iya aikata wani shirme hukuma zasu kama shi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button