WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   Sai dare Faisal ya bar asibitin, ya kira shi a waya.
“Bilal na manta ban gaya maka ba, yarinyar nan ya kamata gidan da take su sani”
“Ok bani address din su” koda ya tura mishi, ya koma wurin da take kwance ya tab’a kanta. Sannan ya fita,  ya nufi gidan Ammyn ya dauki Rahmah har zuwa lokacin fushi yake da ita, daga nan suka wuce gida.

**
A madadin ya tafi gidan su ya gaya musu halin da take ciki, sai ya nufi asibitin ya zauna.  Domin baya jin zai d’agawa iyayen ta hankali. Dan haka ya zauna bayan ya dauko laptop din shi ya shiga aiki da shi.

        … A can gidan marayu kuwa hankalin su ya tashi gashi ko sun kira wayar ta baya shiga domin a kashe yake. Har zuwa dare babu ita babu labarin ta.

Haka suka hakura idan gari ya waye su tafi har kamfanin nimanta,
..
Har kusan karfe biyu yana aikin shi, tashi yayi ya nufi ban daki yayi mika, sannan ya nufi ban daki yayi uzirin shi, sannan ya fita ya zaune  a gaban gadonta. Daura kafar shi yai a kusa da hannunta, ya kwanta haka a kuntacce, domin wannan ne karon farko da ya kwanta a cikin mugun yanayi.  

     Asuban fari ya bar asibitin,  sai karfe tara na safe na farka, inda naga Faisal da matan nan da na taimaka.
“Sannu kin tashi?”
“Eh yallabai Faisal” na kalli matar shi da kamar mu ta b’aci, a hankali na kalli har an zare rovar jinin, sai cannular.

   Ban daki na fara kokarin ganin na shiga tazo tana faɗin.
“Kiyi a hankali, sabida ciwon jikin ki”
“Ba kome “na fada ina kallon shi, gyada min kai yayi, da taimakon ta nawanke bakina.
Nayi duk abinda xan yi a ban dakin na fito, abin karyawa ya shirya min, ina fita na sake yar dariya..
“Kasan me?  Yarinyar nan kamar mu ta b’aci” zungure mata goshi yayi yana faÉ—in.
“Da na gaya Miki ai baki yarda ba, gani kike kamar budurwa ta ce ko Rubi?”
“Rubi?? Meye sunanki?” Ta tambaye ni.
Kallon shi nayi, lumshe idanun shi yayi na Kalle ta kafin nace mata.
“Rebecca”
“Ayya” ta fada tana kallon shi, zuba min abincin suka yi na dan ci kafin na ce musu.
“An gayawa Gidan mu?”

“Eh an gaya musu”
Sannan na cigaba da cin abincin, wadannan masoya zasu saka ka cikin wani irin yanayi, shigowar Nurse ya dakatar da su,  magani sai bani, sannan ta gwada jinina, ban san me ta gani ba, ta min allura sannan ta fita can sai gasu sun kuma dawowa, daukar takardun da kuma sabon text din da aka rubuta min matar Yallabai Faisal.
“Jinin da aka saka mata yaki dauke jinin ta, shine ya haifar mata da karamin zazzaÉ“i. Kina jin zazzaÉ“i ne?”

“A’a bana jin kome sai ciwon kai”
“Kwanta maza” haka na kwanta, allura aka min kafin suka zuba min ido.

Bayan kamar minti talatin wani mugun zazzaɓi ya rufe ni, jijjiyar da nake har gadon yana amsawa. Sai da suka min allura tare da zuba wasu alluran a cikin drip din, sannan na daina. A lokacin yazo shima,

      “Faisal meke faruwa?”
“An duba kwayoyin halittar ka kafin a saka mata jinin?” Kallon shi yayi, kafin ya kuma magana Faisal ya daki bango.
“An samu a cikin jinin da aka saka mata akwai kwayoyin guba a cikin shi , ba mamaki kai ka rayu ne sabida Allah yana tare da kai ita kuma meye laifinta da ta shigo cikin lamarin ka? Gubar ta mata karfi wanda ya haifar mata da wannan yanayin.”  Kallon shi kawai yake kamar wani kurma yana kallon yadda Faisal yake magana.

“A tadda jirgi.” Ya shiga dakin ya dauko ta, zai fita da Ita.
“Ina zaka kai ta?”
“Hakkina ne na nima mata lafiya! Dole ne na nima mata lafiya tunda a sanadina take cikin wannan yanayin.”  Ya fita da ita, bai tsaya ba sai wurin motar shi, babu b’ata lokaci Khalil ta bude kofar motar ya sakata,sannan ga koma cikin asibitin aka bashi takardan shedan barin asibitin.

A ranar suka bar kasar linjeriya, bai zame ko ina ba, sai london. Anan ya kaita aka fara bincike tare da musu bayanin kome, shima kwantar da shi, suka yi dole ya kira Faisal bayan ya sauya layin shi ya gaya mishi.

Wasa wasa sai gashi an shawo kan nashi matsalar, ita kan Rubi kamar ba zata tashi ba, dan al’amarin ya wuce yadda ake tsammanin,sannan a iya binciken da aka yi an ga babu wani abu da yake ci ko yake sha. Sai da aka kwashe sati biyar kafin na farka.

Ranar wata Laraba, yana zaune na bude idanuna, ina saukewa a kan shi na kuma rufe idanun.
“Ban son gulma idan kin tashi na taimaka miki”  sake budewa nayi na ganshi tsaye a kaina.
Danna wata yar karamar abu yayi sai ga nurse da likita sun shigo dakin aka shiga min bincikar ko na samu lafiya.

“Kome nata lafiya sai dai zamu kara mata wani an jima yanzu bari a Turie nurse su taimaka mata”
“A’a no need” ya fada tare da kallona, har zan bude baki nayi magana nurse din da Dr suka fita. Tura baki nayi ina cewa.
“An ce maka zan yarda ka min wanka ne?”
“Toh waye ya gaya miki wanda zan miki?”
“Ga ka nan”
“Ke ban son shirme”
“Ka hadu da shi ai” na fada ina kunkuni.
“Wato zagina kike?” Ya tambaye ni a fusace,
“Kuma ba halin nayi yar magana da kaina”
“Zaki sani”
” Zaka sani dai”
Kama kunne na yayi sai da nayi kara.
Cikin shagwab’a, na ce Mishi.
“Allah zai saka min”
Bude min baki yayi na saka Mishi kuka har ina ture kayan da nake lullube da shi. Yadda nake abin ba karamin al’amari bane dauke kai yayi ta nufi ban daki ya haÉ—a min ruwa nahei nayi wanka.

A kullum rana ta duniya kamar wani bawa na, haka yake min hidima ni kuwa nayi ta mishi rashin daraja, tun yana jin haushi ya murde min kunnen ko ya buge bakina, har ya daina. Kallon kayan asibitin nayi na ajiye a kan gado daga Ni sai towel.shigowa dakin Yayi yana kallon yadda na ajiye kayan.
“Iskancin yau kike ji?”
“Guguwanci nake ji, yau ba zan kwana asibitin ba bari na gwada maka ciwona ya warke.”. Kawai na mike zan bude towel din, sai ji nayi ya wani irin hadani da bango.  Ashe yaji za’a bude kofar dakin ne.
“Sorry mara lafiya ce fa”
“Eh dan fita na sake ta.” Ya fadawa Nurse. Sake ni yayi tare da mangare goshina.
“Wallahi idan baki saka kayan ba, sai ba zane ki” ya fita. Tsaki nayi tare da cewa.
“To ai kwai boxes da haf vest a jikina, an ce maka nayi araha ne da zan bude maka jikina dan renin hankali” na fada ina bin kofar da harara.

     Fuskar shi a sake ya shigo abinci ya tura min da wata jaka, bude jakar nayi naga gown ce abaya da gyale. Sai flat shoe.
“Ba zan saka ba” na tura mishi kayan shi ina bori.  A ran shi ta ce.
Wannan yarinyar zata kashe mutum matukar ban wuce da ita gida akan lokaci ba zata ja min na fara matse ta
Harara ya zabga min tare da daka min tsawa.
“Saka kafin na miki shegen duka” daukar kayan nayi, tare da nufar ban daki can na saka na fito,raba hannuna nayi cikin style na ce mishi.
“Nayi kyau?”
“Ko daya” ya fada.
Zuwa nayi na tsaya a gefen shi, ina kokarin kallon idanun shi har da wani lekawae, shi kuwa sai kauda kai yake.
“Gaya min gaskiya nayi kyau ko ban yi ba?”
“Ko daya baki yi ba”
“Sai ka gaya min nayi kyau ko ban yi ba?”
“Ko É—aya” ya fada yana murmushi sabida yadda na dage sai na leka idanun shi, dariya na saka ina tafa hannu na ce Mishi.
“Fuskar ka ta gaya min nayi kyau kawai kishi kake kar ace ba fika kyau, kasan ku yan China baku son kome ba sai chan chai Chaga chu Chau choo” rufe min baki yayi da hannun shi.
“Ni ba China bane, ni Korean ne”
“Ina ban yarda ba, sai ka rantse min, baka ga idanun ka mitsi-mitsi bane?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button