WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

A kalla sai da muka dauki wata goma sha biyar bamu fito ba daga hal din shekara daya da wata uku, shi hall din idan nace babu abin da babu ina nufin akwai kome, mu rai bakwai aka kawo mu, kuma abu daya aka koya mana, sai dai kowacce akwai inda ta kware, ni na zaɓi computer domin tun a gidan Mss Jessica Simpson ita tace min kar na sake na zabi wani abu bayan shi, shi yasa na zabi bangaren computer. Kuma ina fahimta sosai da sosai. Matsalar da aka samu shine, babu damar kayi kutse sai da izini.

Sannan a gefe guda akwai, Mr James, shi din hadadden gaye ne, irin na fita kunya, an kawo mana shi ne yana koya mana yadda zamu iya jure karfin sha’awan mu, kuma ba wai yana mana kome ba ne, a’a yadda zamu iya shanye duk wata mu’amalar da zamu yi da wasu mazan ne, haka yasa muke iya jure duk wani abinda yake mana, kuma ana bamu maganin da aka tabbatar ba zai mana illa ba, sabida a cikin gidan ake kome.

**
2018
Lagos.

Idan ka ga yadda Ammyn ke kuka sai ta baka tausayi, domin a cikin shekaru hudu, zuwa biyar ita kadai tasan halin da zuciyarta take ciki,ga rashin Rabi’ah, ga kuma rashin mijinta.

“Mr Jones Brinda wannan itace Babbar Yar shi, Jamilah, wannan ne shekaranta na karshe a Jam’i a, sai kanwarta tana Abuja tana karantar likitanci, shekaran ta hudu kenan, wannan kuma tana shekara na uku a jami’a ita, karamar su kuma ta rasu bayan ta b’ata.” Cire madubin idanun shi yayi yana share kwalla, sakamakon bashi labarin da aka yi na mutuwar Abban su Jamilah.

“Kuyi hakuri ku yafe min, ban tafi da kayan shi É—an na ci ba, haka ta faru ne sakamakon mutuwar da mata na tayi da cikin jikinta, naso matuka na dawo, toh ga halin da mahaifiyata take ciki, haka yasa na hakura, amma ina niman yafiyar ku, domin na zalunce ku. Tunda sanadin haka kome ya tarwatsa muku” ya fada yana kuka.

Shiru Alhaji Muhammad Lawal Dambatta yayi, dake Aaman yana zaune a wurin shiru yayi yana kallon yadda Ammyn take kuka, wanda zuwa yanzu likitoci suka tabbatar tana gab da rasa Idanunta saboda yawan kukan da take na rashin Rabi’ah, dauke kai yayi yana kallon Jamilah da take wani irin fushi, dan ita bata ga dalilin da zai saka Ammyn kuka har yanxun ba, tunda tasan Matsalarta likita ya hanata kuka aosai, sai idanun su samu matsala. Mr Jones Brinda ya Basu hakuri tare da gaya musu abinda ya sani na dukiyar Alhaji Ishaq sannan ya basu wasu takardu, haka ba karamin sake suka kowa farin ciki ba yayi.  Domin basu zata ba, bayan ya basu hakkin su ne, ya bukaci su bishi su ga yawan kadarorin shi.

     A take Ammyn ta ce musu.
“Aaman shi yafi dace da zuwa ya ga kome.”
“A’a Kema zaki iya tafiya ki je ki gani,”
Ammyn bata so ba, domin duk wani yarda da aminci ta basu, bata kaunar abinda zai iya cire Yardan da ta musu, a bangaren Jamilah akan fuskarta bata so ace tafiyar da Aaman ba, wanda ba kome ya janyo haka ba, sai dan yadda suke wata irin rayuwa da Namir Adamu Abbas Jikamshi, tsakani da Allah ya fahimci ba zai yiwu gidan su Namir su barshi ya auri  Jamilah ba,.dan yasan yadda gidan su yake da daraja ba zasu bar shi ya auri Jamilah ba. Toh yayi kokarin fahimtar da ita amma baki É—aya taki fahimtar shi karshe ma sai rashin kunyar da ta mishi yasa shi alkawarin babu abinda zai kuma had’a su, dan haka aka bari nan da sati biyu masu zuwa zasu zo inshallah.

  **
Rome.

Kowani rayuwa yana da me kyau ko mara kyau, sannan ƙaddara kullum zagaye take da rayuwar mu. Dan haka bana tunanin yau zata iya zame min rana me cike da tarihi, bayan an gama koya mana yadda zamu yi harbi da duk kowani rana ana kara koya mana yadda zamu kare kan mu, bayan mun gama aka tura ni office din Mr Andrew Cuomo.

      Tsayawa nayi daga bakin kofa sakamakon hango Priyanna tana kan shi, shi kuma yana saman kujerar shi, sauke tayi tana kallona,. cikin gatse ta ce min.
“Kema kin zo ayi dake ne?” Karamin murmushi nayi na dauke kai, bayan sun gama ta tashi ta fita, wannan ba wani abu bane a cikin gidan. Tana fita ya mike tare da gyara zaman wandon shi. Takowa yayi gabana.
“Kin san kin gama samun horon ki, saura nawa horon” murmushi nayi domin ya bani dariya, na ce mishi.
“Har yanzun ba a haifi namijin da zan bashi kai ba, dan haka na dauke ka ne a matsayin Uba, karka bari raina ya b’aci”

Ta shi yayi tare da dauke ni da mari, sai da na zube a kasa, bina yayi da kafa yana naushi na, dakyar na iya tare shi ina girgiza mishi kai. Tashi nayi tare da cewa.
“My Virgin ba kyautar kowa bane, na wanda ya isa.”

Ganin yadda na kafe shima kuma ta shiga dukana, dakyar Allah ya bani sa’a na buga mishi wani Æ™arfe na buga mishi a kokon gwiwar shi, ina ta shi na dauki karfen na buga mishi a gaban shi, kafin na fita gidan baki daya. Na nufi bus stop.

Anan na samu motar Tivilo, cikin abinda bai kai minti goma sha biyar ba, na isa ina sauka, na nufi kauyen da gudu, domin nasan zasu biyo ni, ina isa na samu gidan Mss Jessica Simpson yana ci da wuta, daidai wata mata ta soka mata wuka a bayan ta, sai da ya fito ta gaban ta….

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:57 – Nuriyyat: 45
“Maamahhhhh!” Na kura sunanta da karfi, bayan na rasa kome a rayuwata daga ita sai Steven da Aunty Blessing suka tallafi rayuwata, wace ce ni? Ban sani ba, daga ina na fito ban sani ba, amma qaddara ta had’ani da mutanen kirki da suka tallafi rayuwata kamar tasu.
“Me yasa kika zo?” Ta tambaye ni, hawaye na zuba daga Idanunta, domin tasan tabbas ta kare mata, da rarrafe na isa gabanta, ina kallon lokacin da matar ta kai kafa tare da kwallo ta ita, da sauri na isa ina kuka, tare da rungume ta.
“Maama tashi mu gudu”
“A’a Rebecca kai yi aiki domin kasarka, laifi ne dan na bada rayuwata domin kasata? Ƙarki manta da sakona,  kiyi fada domin Yanci ba domin a biya ki ba, ga wannan makulin zaki same su a milan,maza ki tafi zan dakatar da.”

     Girgiza mata kai nayi tare da cewa.
“A’a, ba zan iya ba tashi mu gudu” ina d’agata, tare da rikota, wani irin numfashi ta ja, tare da zubewa ba jikina. Wani abu naji ya tsaya min a kirjina, hawaye ya xubo min  a hankali ta zube a kasa, wani irin ihu na fasa tare. Binta ina kuka jijjigata nake hannunta ya tafi can gefe, d’ago kai nayi tare da kura mata idanu.

    “Kinyi kuskuren, idan gobe wani ya ce Miki ga abinda zai yi, ke zaki ce mishi kul karka fara aikin da wani zai karasa maka. Meye Maama tayi miki?”  Na tambaye ta da karfi, kafin na dauki wukar ta soki Maama da shi, ina zuwa gabanta, ban yi wata wata ba na yanke ta, da shi dai da ta yarfe hannun ta, sake kai mata yankar nayi, kawai naji kamar an buga min abu a kaina sai da nayi wani irin sauti na daban. Zubewa nayi a wurin.

BAYAN AWA GOMA cif

        Jife ni cikin wani abu a ka yi na ji ƙaran sauƙata da kuma afkawa cikin wasu halittun da ban rarrabe da su ba. Sai dai lambar da ke zane a jikinsu ta tabbatar min da abu guda ne ya haɗa zama na da su.
    ‘Ina ne nan? Me ya kawo ni nan? Su waye mutanen nan?’ Na watsawa kaina tambayar da nasan ba zan taÉ“a samun amsarta ba. Hakan ya sa na duÆ™a a kan Æ™afafuwana ina fashewa da sabon kuka, kukan da na ke da tabbacin na fara yinsa ba tare da samun wadda zai share hawaye na ba. Sake bude idanu nayi tare da sauke kwalla me zafi, tabbas rayuwa Æ™addara ce kowa da irin tasa. Shi yasa wannan kaddaran take walagigi dani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button