WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta fada bawai dan tasan akwai abincin ba, kawai ta fadi haka ne domin ta kyale ta.
“Ina kuka je?” Rahmah ta tambaye ta,
“Gwaggo Lami ce ta tafi damu.”

“Alhamdulillahi, tunda akwai inda zaku zauna ba sai kun zauna da rana ba,  kawai kuna zuwa can kuna wuni zan yiwa Ammih bayani kun ga hankalin ta ba zai tashi ba sosai.” Shiru suka yi dan sun san haka ba me yiwa, domin sun san ba zasu tab’a samun soyayyar dangin mahaifin su ba, dan haka Rahmah ta ce mishi.
“Mun gode malam, sai da safe idan ka koma wurin Ammih ka gaida ita”

     Daga haka ta rike hannun Rabi’ah suka shige wasilah tana bin bayan su,  tunda suka shiga, Rabi’ah ta fara kukan yunwa take ji. Jin muryan su da Matar Ammar tayi ne ta kawo musu abincin da Aaman ya kawo musu dazun da basu nan,  jikin Rabi’ah na rawa ta zauna ta ci, ta koshi tana cire hannunta Wasilah da Rahmah su ma suka ci. Koda suka gama sai lokacin wasilah ta saka Rabi’ah a gaba suka yi sallah.

Bayan sun idar suka shiga dakin su, suka kwanta tare da rufe kofar sosai, sannan suka haura gadon, suka cure wuri guda, tare da lallube kan su da bargo.

*
Ikeja. Lagos

Gudu take a motar ta, tana juya bayan ta, gefe guda jinjirinta sai kuka yake. Sake juyawa tayi suna gab da cimma ta, ta kuma taka motar da mugun gudu, tana me kallon bayan ta. Ta mirror gaban motar,  sake daukar Wayarta tayi ta shiga kira, haka ya gama ringing ba dauka ba cikin shashekar kuka ta ce.
“Buddah nasan Gong Yoo, bai ji Imani da kai ba, Buddah ka kare rayuwar shi da ta Yoo. Amma nasan tabbas Abinda Aunty take gudu ne, ta faru…..” Ta fada tana kallon Yaron gefenta, farar fata ce. Dan ko ba a gaya maka ba, yanayin ta zai gaya maka yar Korea ce.

    Bata an kara ba, sai dukkan da wata motar kwasan yashi ta kai mata,  hantsilawa tayi tare da faduwa can gefe, abinka da Uwa dauke danta tayi ,  suna zuwa suka juyewa motar ya shi baki daya.  A hankali suka tura motar daga sama fly over suka wurgota kasa. Daga ita har Babyn suka mutu, a hankali jini yake zuba a motar yana malala a kasa. Fitowa suka yi fuskar shi rufe da mayafi, sannan suka tafa.

“An gama ka gayawa kowa an gama  me rabo  zai iya jan ragamar.” Inji dayan. Tsaki wanda aka gayawa yayi tare da cewa.
“Waye mai rabo? Waye ya gaya maka cewa wannan aikin hadin gwiwa ce? Kowa farauta ya fito nima na amsa ne Sabida tawa farautar.” Ya fada tare da saka madubin shi a idanun shi, ya koma wurin wata Audi CRV7 ya shiga a hankali bayan an bude mishi motar shi.

   …
A wani kyakkyawan hall wanda ya hadu sosai, dan haduwa ya hadu babu karya,.   zaune suke, manyan dattawa su biyar, maza uku mata hudu.

Mafi girma da manyanta a cikin su, Shine Mr Adamu Abbas Jikamshi, yana rike da wata sanda wacce yake taimaka mishi domin tafiya, a kala zai kai shekaru saba’in da takwas, dan ya ya manyanta. Gefen shi Dr Abubakar Abbas Jikamshi shine, zai kai shekaru sittin da wani abu,  gefen shi Ambassador Abdulkadir Abbas Jikamshi. Wanda shekarun shi ba zasu wuce Hamsin da Tara ba, gefen su can mata ne, Hajiya Turai Abbas Jikamshi ce, Mrs Ali Ruma, gefen ta Hajiya Atikah Abbas Jikamshi, Mrs Abdul Hadi Shema, sai Hajiya Humaidah Abbas Jikamshi, Mrs Muhammad Alfah. Gefen su kuwa wata Hamshaqiyar mace ce, wacce ta ji duniya duniya ta ji ta, kyakkyawar mace ce ajin karshe.

Kana ganin ta kaga buzuwa, irin sadakayallar nan,  Hajiya Murjanatu Ahmad Abbas Jikamshi. Matar Later Alhaji Ahmad Jikamshi wace ake kiranta da Shuwa. Tana zaune gefe guda, tana kallon kowa kuma suma suna kallonta,  bata shiga shirgin kowa haka ma Yaranta bata yarda su shiga shirgin kowa ba.

   Asalin su familyn Jikamshi idan ka cire Hajiya Atikah Abbas Jikamshi, toh dukkan su kowa su yake ya bayan dan uwan shi akan abin duniya,  amma babu yadda suka iya domin gabar su bata kai wanda zai sanya su kashe junar su ba, amma maganar gaskiya sun tsani junan su, akan Kamfanin daya da ya had’a su. Wayar Hajiya Atikah ne yayi kara. ÆŠaukar wayar tayi cikin sassanyar murya tace mata shi.
“Faisal lafiya?”
“Ummin an kashe Ha Na, ita da Ahmad karami Yoo”
“Innalillahi wa’inna illahirriji’un, Yanzun ina Gong Yoo yake? Ya samu labarin?”
“Eh  ya samu labarin amma yace a tattara gawan su, a tafi dasu Korea shima ya wuce ba zai dawo ba,  ku d’aga meeting din nan sai wani watan”

   “Allah sarki, kai ban ji dadin wannan labarin ba, ka shirya mana tafiya insha Allah zan isa Busan na musu ta’aziya!” Ta fada jikinta a matukar sanyayye, tana kashe wayar ta zubawa Yan uwanta idanu, ita kan yanzun ta fara hango shawaran da Faisal ya bata da ya ce mata. Ta cire dukiyarta a cikin Jikamshi Family Company, ta zuba a nasu domin shine zai tsirarta da rayuwar ta, tsoron fitinar nan na yan uwanta yake karsu kashe ta a banza.  Gyara zaman hijab din tayi sannan ta mike, tana ce musu.
“Toh, nikam zan tafi matar Gong Yoo ta mutu, hankalin masu ruwa da tsaki sai ya kwanta.” Ta fadi haka ne domin tasan wannan ba shine karo na farko da aka fara ba, dan haka ta tafi haka. Matan shi biyu ana kashe su.

Ita Ha Na itace ta uku, kuma abin mamaki babu wanda ya san me ake musu biyan can sai dai a tadda gawar su. Matar shi ta farko Munibah yar kasar Somalia ce, domin irin Model din nan ce, a swimming pool aka samu gawar ta, ta sha ruwa ta koshi. Ga wuyarta da aka shake ta, matar sa ta biyu me suna Bioden yar nan Lagos ce babban ta shine Chef Imam na babban masallacin juma’a Lagos, da safe aka wayi gari an kashe ta, a dakinta.

    Wannan Dalilin yasa shi kin aure sai da Mahaifiyar shi ta tilasta mishi duk da bata kasar Amma tana mugun gudun abinda zai cutar dashi.

“Wannan wacce irin magana ce? Waye zai kashe mishi matar shi bayan kowa yana da abin yi?” Inji Alhaji Adamu Abbas Jikamshi.

   Kwafa Alhaji Abdulkadir Abbas Jikamshi yayi, tare da mikewa a fusace yana faɗin.
“Wato ke dan Danki yana tare da Jikamshi, shine kike jin kan ki?” Murmushi tayi irin wanda yake cusawa mutum b’acin rai ta dauki jakarta tana faÉ—in.
“Ya Abdulkadir! Ka iya takunka ka saukaka al’amarin ka, da harshen ka amma nayi nan domin zuwa Busan ta’aziya, duk wanda ya shirya mu hadu a garin Busan…”

Daga haka ta fita daga hall din tana mamakin halin Yan uwanta, daga Ita sai Alhaji Ahmad Jikamshi suka fito ciki daya,.kuma babu abinda ya raba su ba halin su É—aya.

Mai_Dambuu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I’m selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===150
1GB@=====270
2GB@=====550
3GB@====800
5GB@====1,350

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR Call 08066268951
Na
Mai_Dambu
Wasu dangin<10>

Hajiya Atikah Abbas Jikamshi,tana fitowa escort dinta suka rufa mata baya, daga cikin window dakin taron Alhaji Abdulkadir Abbas Jikamshi Abbas Jikamshi, yana kallon lokacin da Hajiya Atikah Abbas Jikamshi,ta shiga motarta. Kwafa yayi tare da É—aukar brifcase din shi yana jan tsaki ya fice daga cikin dakin taron yana jan numfashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button