WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

    Haka kawai taji a ranta zata iya hakuri da rashin da tayi, kuma ta hakura insha Allah, ta barwa Allah  babban Damuwarta Rabi’ah ta dawo, dan haka ta rike hannun Wasilah da na Rahmah. “Zo Jamilah”  juyowa Jamilah tayi tare da mikewa zaune, ta yunkura zata sauko Wasilah ta isa wurinta, tare da riko ta, ta sauko a gadon sannan ta zauna akan pillow din da aka saka mata, tana zama suka zuba mata ido, a hankali ta fara cin abincin tana kuka, baki dayan su kuka suke tare da kokarin dauke samuwar su, musamman idan suka kalli gurbin zaman Rabi’ah a haka suka gama cin abincin sannan suka mike, Rahmah ta kaiwa Jamilah ruwan zafi ban daki, da taimakon Rahmah tayi wanka, sannan suka fito ta taimaka mata tasa kayan ta, ta kuma kai wa Ammyn ruwan wanka itama ta shiga tayi, sannan Wasilah ta yi itama, kafin su gama har Jamilah ta daura abincin Rana baki daya,  tana gamawa t0 nufi ban daki tayi wanka tazo suka zauna.

        Kallon Ammyn suka yi kafin suka tambaye ta.
“Ammyn ina Rabi’ah take? Ko su Gwaggo Lami sun hanaki ita ne?”

Kallon Yaran tayi idanunta cike da kwalla, kafin ta ce musu.
“Ta tafi birni aikatau!” Daga haka ta juya musu mata bata kuma magana ba, sai dai kuma hankalin su yayi Masifar tashi, Sabida yadda suke kaunar ta, haka suka yi kuka su kan su Sunyiwa Ammyn su uzuri domin dole ta shiga wannan yanayin.

   Dan haka suma suka shiga, matuƙar damuwa, amma haka Rahmah ta boye tashin hankalin ta, tayi ya rarrashin Ammyn su,.har ta samu kwarin gwiwa.

*
Busan. Korea republic,

Kwance yake cikin duvet cover, mugun zazzaɓi ya rufe shi, baki daya ya fita hayacin shi. Shigowa Seyo Na da NaNa suka yi, tare da Um Ma,  zama suka yi a family bed din dakin shi.
“Oshii, Oppa meke damun ka ne? ZazzaÉ“i yau kwana goma da binne Ha Na. Amma”

“Seyo Na, kyale shi Allah ya bashi lafiya amma dole ya hakura da Nigeria mutanen da mugaye ne” inji Um Ma,
Tashi yayi  daga kwance ya zuba musu ido. Sauka yayi daga gadon ya nufi ban daki, amai ya fara yi dukkan su, suka shigowa ban dakin. Sai da ya gama ya mike dakyar yana musu alamar su fita zai cire kayan shi, fita suka yi,  ya cire kayan shi ya tara ruwan zafi, sannan ya shiga ya zauna a cikin ruwan, abu daya yake damun shi domin yasan damuwar halin da yake ciki ne ya haifar mishi da wannan yanayin.

   Bayan ya gama wanka ya fito, ya dauko wayar shi ya kira family Doctor din su, can ya kira likitan ya mishi bayani, kashe wayar yayi sannan ya saka doguwar jalabiyar shi ya shimfida abin sallah, yana sallah likitan ya shigo.  Bayan ya isar likitan ya fara duba shi, yana mishi bayanin. allura yayi mishi sannan ya ce mishi.
“Yaushe zaka yi aure?” Bude idanun shi yayi tarr akan likitan, lumshe idanun shi yayi tare da mikewa yayi tare da jingina da allon gadon.

“Bana jin haka nan kusa, meye damuwar? ” Ya tambayi likitan yana dauke kan shi. Mikewa likitan yayi yana kallon shi kafin ya ce mishi.

“Damuwa da bukatar mace yake addabar ka! Idan zaka iya kayi aure zai magance matsalolin ka.” Shiru likitan yayi yana kallon yadda ya had’e rai, bai ce mishi kome ba, ya fita daga dakin bayan ya ajiye mishi wasu magani kafin ya ce mishi.
“Toh tunda ba zaka iya auren ba zaka iya tafiyar da rayuwar ka haka, akwai kyawawan mata da maza.”

“Fita” ya daka mishi tsawa,
“Kayi hakuri, zan turo maka da magani yanzun” ya fada tare da fita daga dakin yana dan duka mishi, tsaki yaja sannan ya lallubi wayar shi ya kira Lim shin, a kawo mishi Coffee mara madara. Can kuwa sai gata ta kawo mishi.
“Nagode” ya amsa yana kurb’an Coffee din shi a hankali, wayar shi ya duba tare da hango sakon Khalil, sai na Faisal. Murmushi yayi sannan ya tura mishi sakon.
Ina lafiya, yar fever nake fama dashi amma da sauki

Bai turawa Khalil haka ba, sai dai ya ce mishi yana lafiya, shigowa dakin Um Ma tayi rike da wani jakar kwali ta mika mishi tana me zama a bakin gadon fuskar ta a dame.
“Amma ba zaka koma ba ko? Domin mutanen nan basu da imani don Allah kar ka tafi.”

Shiru yayi yana jin ta har ta gama, sannan ya ajiye mug din coffee din a gefe ya tattaro hankalin shi gare ta, ya ce mata.
“Um Ma. Ba zan iya rayuwa babu cigaba ba, ba wai ba zan ji maganar ki bane, can É—in ma rayuwata ce, sannan idan na zauna anan na basu daman su cigaba da fadar cewa na zama É—an culti ina kashe mata na domin nayi arziki Um Ma tun karar makiya ba Abu me sauki bane, amma wajibi ne tunkare su, tunda har an kai matakin haka don Allah ki bini da Addu’a”

Ya fada yana dafe goshinsa, domin bai iya dogon magana ba, idan ya dage zai yi ma ciwon kai yake saka shi ɗan haka da ya kai aya, sai da ya kwanta. Bude jakar takardan yayi sannan ya ciro wani roban magani ya bude robon ya ciro capsule biyu, ya yafiya tare da kora musu sauran Coffee din shi da ya rage, yana gamawa ya sha sauran na zazzaɓin.

Shiru tayi tana kallon shi, bata san lokacin da tace Mishi.
“Kai kan ka dauko halin Ahmad na tunkarar makiyan shi, sai dai kafin ya rasu ya turo min da sakon sai dai ban kai ga budewa ba ka gaya min Ya rasu, yana cikin Email dina”. Murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Ya wuce sakonnin soyayyar ku ce.” Ya fada cikin son ya sakata farin ciki dan ya lura a dame take da gasken.

“Nima haka nake tunani” ta fada tana kallon shi.
“Kin ji dadin ki.” Ya fada mata yana me mikewa daga gadon ya ce mata.
“Toh Um Ma, bari na tafi wurin Wang Boon”  ya wuce tare da fita domin idan ya sake ya biye mata, zazzaÉ“in da yake damun shi zai karu, kuma karshe ta kashe shi da lallashi ya fasa zuwa nigeria.

**
Dutse. Jigawa

Sun shirya tsaf, tare da yiwa Rabi’ah wanka, inda suka nufi dakin Yar duwala.
“Toh akwai Na maroko a waje, na gaya mishi tun jiya yanzu haka yana can yana jiranku.”

      “Toh” inji Altine ta riko hannun Rabi’ah suka fita, har waje ta samu, me taxi, ya dauke ta sai Asibiti, anan suka zauna kafin Dr Musa ya zo suka nufi babban asibitin. Dutse anan suka ga likitan, sai da ya gama jin bayanin Dr Musa, sannan ya kalli Altine ya ce mata.
“Ki fita ki barta” mikewa Altine tayi zata fita, Rabi’ah ta rikota a rikice, dole haka ta cire hannun ta, aikuwa jikinta ya fara rawa, tare da niman inda zata boya, sai kuka tana wasu irin abubuwa kamar zata suma kamar zata fadi.

   Har ta gama likitan ya tashi tare da nufar ta, aikuwa ta fadi. Da sauri ta koma can wani lungu ta zauna. Take ya rubuta musu wani test har biyu, haka suka  nufi waje da ita, aka kaita aka mata test din ƙwaƙwalwa, sannan aka duba wasu abubuwa masu muhimmanci kamar zuciya da kodarta. Kafin suka dawo gida domin likitan kan ya tashi, amma Dr Musa ya kai mishi result din har gida.

  Kallon Dr Musa yayi tare da ajiye takardan yana me zare medical glass din shi, ya ce mishi.
“Dama tunda kace min baka tunanin an haife ta da ciwon na fara hasashen ko Autism ne! Toh da na saka ayi mata test din ya fitar min da abinda ban yi tsammanin shi ba.” Yayi shiru Yana kallon Dr Musa, da yake kage da jin wacce irin matsala ce.
“Karka damu ba wani babban ciwo bane. Phobia ce bari na maka misalin da kuma yadda ciwon yake damun al’umma da yadda take farmakar mutum, tsoro da damuwa yana cin kasuwar shi a wurin daba’aka ciwon cutar Phobia, tashin hankalin da mutum zai riski kanshi, yana tagazawa wurin haifar da ciwon Phobia, zai iya haukata tsarin dabi’ar dan adama
Dan damuwa mutum yana goge idanuwansa
Hotunan JGI/Tom Grill/Getty
Ma’anar ma’anar halayen phobic shine duk wani martani ga phobia. WaÉ—annan halayen alamu ne – alal misali, jin damuwa mai tsanani ko tafukan gumi — kuma suna iya kamawa daga mai laushi zuwa mai tsanani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button