WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri ta bude idanunta, ta kafe shi da su. Cikin wani irin tsoron da ya nunku a ranta, ta sauka da sauri tare da cewa.
“Don Allah kayi hakuri wallahi ban.”  Daukar goran ruwan yayi da yake can gefe guda, ya bude tare da sha, yana kallon yadda take kamar wacce tayi karya.
“Nazo tambayar ki ne, kina so na ko na tafi na nemi wata?” Shiru tayi mishi duk maganar da yayi, bata d’ago kai ta kalle shi ba, har ta gama maganar shi. Bayan na gama gundura da shirun tai  ne  yasa shi mikewa tare da kallon ta.
“Okay Nagode, ina ga zan nime Sabrina ina ga zata dace da ni, ai kinsan ta, Yar yayar Mijin Lubna.” Da sauri ta d’ago kai tana kallon shi, tare da kokarin danne kwallar da ta cika mata idanu, a hankali tayi kasa da kai kwalla suka shiga zuba mata da mugun gudu. Sai da yazo zai fita yaji shashekar kukanta.

“Ya kike so nayi? A wannan shekarun kamata yayi a ce ina da iyalina. Ina sonki shi yasa na shanye zama babu mace, Kinsan hatsarin da nake tsallakewa? Ina sonki shi yasa har nake nan domin ke, baki sauran matan ba, domin har office ake kawon min tallar kayan su.”  Ya fada a sanyayye,
“Toh ya kake son  nayi da Ammyn? Ni tsoron kar tayi fushi da ni yasa nake ganin kamar ka kara hakuri”
“Hmm! Wallahi ko na wata daya ba zan iya hakuri ba, idan har zaki tsaya ki mata magana toh,idan kuma kina ganin kamar na takura ki ne ba damuwa sai ki zauna amma tabbas na gaji..

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:57 – Nuriyyat: 46
Hàdiye yawu tayi tana kallon shi kafin tayi kasa da kanta.
“Duk abinda kayi dai-dai ne, bani da wani zabi sai abinda ta zab’a min ba i da ikon tsallake maganarta, sai abinda  ta umarce ni” ta fada tare da juyawa ban daki ta shiga tana me rufe kifar baki daya, shiru yayi yana mamakin hali irin na Ammyn su,domin wannan son kai ne kiri-kiri.

Ga Bilal baya gari ya tafi ya barshi da aiki, baki daya kome ya tsaya mishi a kai ji yake kamar ya cire zuciyar shi ya huta. A hankali ya sake kofar dakin yai tafiyar shi hawai ya bar compound na makarantar bane, amma kuma yana nan a cikin motar da ya dauka na masaukin shi. Ya jima sosai kafin ya tadda motar. Yana mamakin hali irin na Yarinyar baki daya bata da wani sabon abu akanta sai abinda Mahaifiyar ta, ta ce mata ba zata ta yarda yayi dogon alaka da shi ba, sai abinda aka ce mata. Taya zai yarda da macen da sai Abinda mahaifiyar ta, tace mata dan haka ya wuce gidan Lubna, yana shiga ya hango Sabrina.
“Uncle kunyi fada da ita ne? Har ka ce zaka aure” kura mata ido yayi sannan ya ce mata.
“Private life dina ne, bana son magana kiyi shiru ki bar kome a inda kika ji shi, bana son magana” baki daya shi yasa bai cika zuwa gidan Lubnah ba, domin wannan aljanaar yarinyar, tun zuwan farko sa suka yi Sabrina taga Rahmah tace mata.

“Ki daina boye abinda yake ranki, yana sonki, matsewar tayiwa.”  Tun a ranar ta fara tsoron Sabrina, kuma uwa Uba yadda ta gabsikr wani shigewa jikin Juna da Faisal yasa ta, jin bata son yarinyar, tunda suka dauki januay zai dawo da ita hostle take fushi, karshe ganin zasu yi rabuwar babu dad’i ya tambaye ya Meye yayi mata.
“Me zaka min kuwa bayan baka gaya min kana da wata budurwar ban sani ba?”
“Kina kishi ne?” Ya tambaye ta yana tuki,
“A’a me zai saka nayi kishi kuma, kawai dai tambaya nayi, kuma ai ba laifi bane, da ace Beeyah ta nan sa’arta ce kaga babu amfanin haka?”
“Kina so na amma kike nunawa bani damu da ni ba? Kina kishina amma kike abu kamar babu ruwanki? Ruwanki ne ki damu dani ko a kasin haka duk daya ne”

  Wani abu taji ya tsaya mata a wuyar, da sauri ya fito taga baya dakin, Wayarta ta dauka tare da kiran Ammyn.
“Ammyn! Don Allah kiyi hakuri”
“Da akayi me?” Ta tambaye ta cikin kulawa,
“Ammyn ya zo, yana niman na bashi dama!”
“Ki bashi dama a bankado sirrin Yayan Mahafinku ya tab’a lalata da Yar uwarki? A bashi dama ya bankado abinda zai saka zuciyata ta buga? Alakata da mahaifiyar shi daban, alakanki da shi daban. Ki rabu dashi bana son tafiyar ku tayi nisa, idan  kuma kika cigaba da saka shi a ranki tabbas ranki sai yafi na kowa b’aci domin haka, ki janye daga gare shi, bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, ki tsaya iya inda kike”

  Wasu irin kwalla ne suka xubo mata,  a hankali ya kashe wayar tana me kwanciya a gadon, wani irin zazzaÉ“i yana rufe ta. Domin baki daya ta shiga rudani me yasa Ammyn bata damu da ita ba sai Jamilah? Me yasa bata damu da tasu matsalar ba sai ta Jamilah har gwara Rabi’ah ta damu da ita, dan haka bata san lokacin da ta fashe da kuka ba.

      Wayarta ta janyo tare da kokarin kiran  Faisal, yaji yana busy dan haka ga kashe, tana sake wani irin kuka.

**
Busan korea.

Idan kaga Hajiya Humaidah tayi wani irin sanyi gwanin ban tausayi, domin tasan iya yanzun zaman Lagos ya fara fin karfinta, gashi duk da haka taki tacewa Bilal tasan wani abu da yake faruwa a cikin kamfanin su baki daya.

Shigowa Seyo Na da NaNa, sai Mimih da take bin bayan su.
“Mommy ya kike? Ya jikin Abban?” Ta tambaye ta bayan ta zauna, a hankali.
“Um Ma gida” ta zauna tana tambayar su.
Suma Seyo zama sukayi tare da tambayar su ya gidan,
“Lafiya lau, ya makarantar?” Hajiya Humaidah ta bata amsa,

Mai da Idanunta tayi kan Kim Eau Jikamshi,
“Maman Bilal har yau ban ji kince kome akan Mimih da Bilal ba?”Murmushi tayi tare d kallon yaran da suka mike baki É—aya,

“Idan yaran suna nan ki bar dauko irin wannan al’amarin, sannan maganar gaskiya bana jin Gong Yoo yana da sha’awar aure, ki kula da abinda yake gabanki karki dage sai shi.”

    “Kim Eau! Me yasa kike tunanin wani abu daban? Ina ga kamar nafiki iko da Bilal, ba iko nazo nima miki ba, nazo mu fahimci juna ne, na bawa Bilal Mimih domin ko na bai aure ta ba, ko ya aure ta ba shi zai hana masu niman rayuwar shi su kyale shi ba”

Mikewa Madam Kim tayi tana kallon ta, kafin tayi dariya sannan ta wuce tana dariya Æ™asa Æ™asa, domin abinda Hajiya Humaidah take yafi kama da fin karfi. Dan haka ta barta a wurin tayi ita É—aya babu me kula ta, tun kafin ta shiga daki ta watsar da zancen kamar ma ba ayi kome ba, wannan shine dabi’ar Kim bata tab’a ajiye abu ko dan wani dalili ba, a’a shi yasa danta shima ya kwaso kome bata, sai dai shi bai cika damuwa da abinda babu ruwan shi ba, wanda yake da ruwan shi da shima bai bi ta kanta shi ba, balle ya saka kan shi uku .

**
Karfe biyu na dare muka isa bakin bodar Mexico da United State. Kasancewar akwai rashin zaman lafiya ga kasashe gudu biyun Mexico da United State, yasa United State suka saka mugun tsaro a bakin iyakar su. Dan haka muka yada zango a wurin. Ina gefe da Anna, sojojin da suke kan iyakar United State, suka fara bin mu ana binciken.

     Wasu guda biyu sojoji biyu suka tsaya akan mu.
“Daga ina kuke?”
“Milan!” Shugaban tafiyar mu ya fada.
Shiru sojan yayi yana kallon mu, kafin ya ce.
“Me zaku shiga yi a cikin  Mexico?”
“Zamu shiga bikin ranar samun yancin yan LBQS na Duniya.”
Lashe bakin shi yayi tare da kallon su, sannan ya ce musu.
“Toh yanzu ku ware mana kan ku, yan lesbians da gays” abinda takaici haka maza da mata suka ta ware kan su, aikuwa sojojin nan suka shiga kwasan yan mata zuwa tantin su. Haka mazan ma basu kyale su ba, suka shiga dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button