WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kai Maganar gaskiya yarinyar nan ta gama da kai, kan Uba wato ta kalli kayan ka, toh waye ya sani ko ta dauka a wayar ta, mutnen nawa zata basu labari gaskiya ya kamata ka nimo yarinyar domin ka mata iyaka da kai.” Juyar da kai yayi ran shi yana kara tabbatar da shawarar Khalil har suka isa Apartment din Mr Jikamshi.

Rufe jaridar yayi ya fito a hankali, suma duk suka fito, Khalil ne ya wuce ya bude cikin gidan, sannan ya kalli Mr Jikamshi.
“Sir na gama”
“Zaka iya tafiya” ya fada, yana kallon Faisal da yayi zuru zuru gwanin ban tausayi.
“Barista zamu tafi ne!” Ya tambayi Faisal.
“A’a jeka kawai zan gana da Bilal” ya saka hannu a cikin Aljuhun shi, sannan ya nufi gidan.
“Ok sir, karka manta da yarinyar nan ka nime ta.”

Share shi yayi tare da shiga cikin gidan, Mr Jikamshi yana baya shi kuma yana gaba. A cushion na falon ya zube tare da dafe goshin sa.
“Ya kamata kayi aure.” Ya fada tare da barin wurin.

“Kai kai kai, meye nufin ka?” Ya daka mishi tsawa, kamar zautacce,
“Aure nace kayi” daga haka ya shige cikin dakin shi ya bar Faisal da takaici kamar Ya mutu, sanarwar da aka yi a airport din ne ya dawo mishi.
“Jirgin Japan zai tashi”  bai kuma bin kan  Mr Jikamshi ba yayi waje da sauri, har ya fita ya kuma dawowa da sauri ya dauki key motar Mr Jikamshi , ya fita da sauri gida ya nufa ko wurin Ummin su bai shiga ba, ya haÉ—a kayan shi baki daya.

     Sai da ya nutsu sannan ya nufi makarantar su,dakyar ya samu ganin shugaban makarantar, yana gabatar mata da kan shi ta mike, kamar ta ga asalin Jikamshi da kan sa.
“Yallabai me kake bukata a kawo maka Coffee ko shayi”

    “No need, akwai yarinyar da suka tafi Japan a cikin makarantar ku wata ba fara bace can,.tana nan tana da duhu wata yar karama ba can ba” shiru tayi tana kallon kasa, kafin ta ciro mishi hotunan yan Japan din.
“Wadannan ne suka tafi Japan.ka duba su ko zaka ganta” amsar hoton yayi ya fara budewa a hankali idanun shi ya sauka akan fuskarta tana murmushi. Cizon lips din shi yayi yana kallon ta.
“I found her” ya ajiye mata hoton.
“Sunan ta?” Ya kuma tambayar ta,
“Rahmah Ishaq DaÆ™ayyawa, sixteenth year old Ss2 class captain, mark 98” kallon ta yayi a hankali ya mike yana kuma kallon hoton Rahmah.
“Me suka je yi a Japan?”
“Sun tafi gasar Mathematics na duniya ce, kokarinta yasa a wata shida zuwa bakwai da tayi a makarantar aka bata class captain, sannan nutsuwarta da tsafta ta yasa aka riritatta a makarantar Sir idan babu laifi don Allah karka ce zaka mata wani abu dan nasan haka kawai ba zaka zo niman ta ba”

   Hannu ya saka a cikin Aljuhun shi, yana kallon ta. Kafin ya ce mata.
“Bari mu karkare zancen ina son a mata transferred zuwa Jikamshi Model school.”
“But Sir”
“I said do it, ko kuma na karya career din makarantar”

Shiru tayi tana kallon shi. Kamar ba xata ce kome ba.
“But Sir”
“Shiiii! I said do it!”
“Da kabar ni nayi magana domin ba ita daya bace a nan akwai kanwarta Wasilah, itama.”

“Bana son na kwashe muku Hazikai ne amma da na tattara baki daya masu kokarin na zuba a Makarantar” yadda ya lura da ita tana kwana kwana.
“Bani account din ki” babu musu ta miko mishi, kallon ta yayi tare da ciro wayar shi, yayi yar danne danne, can taji kara. Tana dubawa ta ce.
“Sir na baka ne a yanzun ko sai ta dawo?”
“Now” ya kalli agogon hannun shi, zai bi shortcut ne, zai fara bin Dubai daga nan ya samu jirgin can. Tana gama kome ta mika mishi. Sign tai shima yayi sannan ya kalle ta yana faÉ—in.
“Zaki iya gayawa Guardian dinta abinda ya faru ko zaki gyara zancen ne yaji kayan had’i” ya fita yana murmushi.

    *
Cikin gidan Alhaji Muhammad Lawal Dambatta suka shigo, nan suka hadu da su Jadwah da Jawahir, kallon su.Ammyn tayi tana faÉ—in.
“Wato ku ba za a gankun ba sai an shigo ko?”
“Ai basu da kirki, Ammyn su ina surukata?” Inji Hajiya Karimah,
“Tana gida” ta bata amsa tana kara zama suka gaisa tare da fadawa hira,

   Anan suke kara tattaunawa akan Rabi’ah.
“Ni dai ban fidda rai ba, domin ina jin duk inda take tana cikin koshin lafiya,abu daya yake min ciwo yadda na so daukar yarinyar nan aka hanani domin bata da lafiya sosai”
“Kiyi hakuri” inji Mammyn tana shigowa falon.
“Toh ya zamu yi, duk abinda Allah ya tsara tun fil azal ya tsara sai dai muyi fatan Allah ya kawo mana sauÆ™in shi ya kuma bamu ikon cinye jarabawar mu”
“Amin Ya Allah” nan suka shiga hiran Aaman da aka kuma tura shi India course a institute of Police academy, da yake garin hydeerbad yankin tamil nadu.

    “Allah Mammyn su, kiyinta nishi addu’a, ba dare ba rana, sadaka da azkar maganin kowani masifa ce, babba dan haka ayi ta addu’a, Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu. Ta fada tana share kwalla. Domin cuta kan ta san an cuce ta, kuma an kasara mata rayuwarta da na Yaranta, an lalata mata goben su Allah kadai zai saka musu.

**
Abuja
Duk shirin da aka Maman Steven bata sani ba, dan haka tana zaune baki a sake bayan ta gama min duka, ta kora ni waje tana masifa, zama nayi ina kuka. Kaina a tsakanin cinyata. Ji nayi an dafani.
Da sauri na d’ago kai,.ina kallon ta.
“Yau ma ta dake ki?” Gyada mata kai nayi.
“Bari na shiga na Nimo Miki abincin” ta fada tare da shiga cikin gidan,
“Mimmah don Allah bani abincin zan kaiwa.”
“Na rantse da Allah idan ma Aljanu kika kwaso Dr yasan yadda zai yi dake fita ki bani wuri”

“Please mimmah, bari na kawo Miki ita ki ganta,” ta fita da gudu. Ina zaune na ganta, nasan hala Mamanta ba zata bata abincin ne yasa ta zo gaya min.
“Zo muje na gayawa Mimmah ke mutum ce shine taki yarda” ta kama hannuna ta shiga dani gidan dai-dai saukar Madam Fate akan mashin,sake baki tayi tana kallon mu, har muka shiga cikin gidan.

     “Mimmah gata nan” ta kai ni har gaban Maman,ganin yadda na koma jikin bango na makale, ina sauke ajiyar zuciya.
“Aslam zuba mata abincin ka kawo Mata” da sauri ya mike tare da yin abinda ta ce.
“Ya sunanki?”
“Rebecca Uchanna Jeshua” mika min abincin yayi na zauna na fara zuba loma.
“Ban yarda ba ha sunanki?”
“Rabi’atu Ishaq” na bata amsa nutse bayan na cika bakina da loma, wani irin shiru tayi tana kallona.


“Heeee Mary! Da sanin ki Yarinyarki take shiga cikin gidan Makotanki? Ogini? Meye ya shiga kanki? Coman tashi muje ko dawo da ita,”

  Cikin fushi da b’acin rai tace.
“Heeee wannan Yarinyar zata kashe ni,  yau sai na bata mamaki”
.suka fita fuuuuuu sai gidan Dr Hayat Abdulwahab.
A gidan kuwa kallon kodaddu kayan jikinta tayi tana mamakin yadda aka bar dan mutum yayi irin wannan dattin haka.
“Ka shiga ka fito min da yarinya na ko koma na kira yan sanda” jin hayaniyar da kuma yadda jikina yake rawa yasa kallona. Kafin ta fita ganin yadda take cike da nutsuwa ga kamala a shimfide a fuskarta, yasa Mamna Steven ta sassauta muryan ta ta ce.
“Hajiya Nazo daukar Yarinya na ne”
“Ok” ta fada tare da cewa.
“Rebecca”
Da sauri na fito duk na sake fitsari a jikina.
“Madam daga Addinin Kirista zuwa na Musulunci babu wanda ya bawa wani damar cutar da wani dan Adam, idan muka duba rayuwar baki daya bata da yawa, Yaron da ka cutar wata rana sai Allah ya albarkaci rayuwar shi,  balle kuma mara. Wannan yaron ba Nice na haife shi ba, Mahaifiyar shi tana nan but ko sau daya ban tab’a Mishi tsawa ba, sabida ina son shi ina son mahaifin shi, dukkan addinai guda biyu sun koya mana yadda zamu rike Maraya da kuma falalar rikon maraya, Karki manta Mary mother of Jesus Christ, mareniya ce aka bawa Annabi Zakaria ya riketa, a cikin Alkur’ani an fada mana a Suratul Maryam sannan a cikin bible an fada mana ki je ki duba da kyau, wata rana sai labari.”ta riko hannuna ta mika mata ni, daga ita har kawarta jinin su ya kafe, jikin ta yayi mugun sanyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button