WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Daga haka ya mike tare da kunce shi ya nuna mishi hanya. Zubewa yayi akan gwiwar shi, yana kuka tare da rike kafar Bilal.
“Sir kayi hakuri don Allah ka yi hakuri ka yafe min”
“Ok zan baka last chance amma kafin na dawo kasan abinda zaka fada a idan aka nime sanin haka, ga kudi nan ga mota nan sai dai ka sani fita waje a gare ka masifa ce domin zasu iya farmakarka iya wannan zan maka ko ka rayu domin biyan bashi ko kuma ka mutu kana ji kana gani”

Wannan masifa da me yayi kama, Bilal na gama abinda zai yi ta dauki kayan shi ya bar gidan baki daya. Tabbas Bilal yayi gaskiya domin shi kan shi ya san matukar Ya fita Hajiya Shuwa, Alhaji Adamu da Hilal sai Hanan ba zasu tab'a barin shi ya rayu ba, dan haka yake ganin zama a  gidan shine ceton rayuwar shi.

Kai tsaye daga airport Nijar ya wuce, koda ya isa sai da ya kira General Aliyu Assadullah, ya gaya mishi. Bayan mintinan kadan sai ga motar sojojin kasar Nijar. Suka dauke shi har gidan G.Aliyi A Aliyu (Zanen qaddarata) suna isa aka kai shi dakin su Muhammad, sai da yayi Sallah sannan ya huta, yana zaune Muhammad ya shigo.
“Barka dai Mr Jikamshi” Murmushi yayi tare da cewa.
“Barka dai.”

   "Baban mu yana son magana da kai" mikewa yayi, suka fito har cikin gidan da farko matan gidan sun zata an zo niman Auren Junainah. Babban falo aka kai shi ya zauna, kafin wani lokaci Aliyu da Anum suka fito. Zama suka yi sannan aka gaisa cikin mutunttawa, sannan aka kira Junainah. 

“Bilal na kira ka ne domin wani binciken da muka yi gware wuri É—aya akan Mahaifin Junainah. Shekaru shida baya na tsince ta ne bayan an buge ta aka tafi aka barta. Tayi jinya amma Alhamdulillahi dan ta samu sauki sosai. Matsalar akwai wani abu da mahaifinta ya bata ne kafin a kashe su. Ka gan shi nan” ya mika mishi yar karamar sarka sannan ta shiga mishi bayanin bayan ya gaya mishi abinda yake faruwa har ya kai da sun duba cikin sarkan sannan suka fara magana na fahimtar Juna.

“Dr Musa yana raye da Yayan ta da Mahaifiyarta, matsalar da ake ciki duk wanda ya shiga cikin al’amarin ana bibiyar shi ne, sannan ita kuma bana son wani abu ya faru da ita akwai shari’ar da zamu yi idan aka gama akan lokaci sai a dawo da ita. Mahaifinta ma ina kyautata zaton ya bar kasar jiya, domin bamu son duk wanda ya shafi case din ya kasance a wurin da za a same shi.” Inji Bilal.
“Na fahimta, yanzu abinda za ayi zaka tafi da ita Korea domin tana kewar Rabi’a idan da hali ku tafi tare da Muhammad sai yaga inda take.” Ya fada bayan ya mike sakamakon kiran sallah Isha da akayi. Suka nufi masallaci.

Kusan rabin hiran su Labarin Bilal yake bawa General AAA, har dare. Washi gari kuwa suka shirya har da Muhammad suka nufi korea.

**
Fasa kome na Falon Hajiya Shuwa take tana fada da ihu.
“Waye ya isa ya lalata min shirina? Taya kome da yake tsare zai lalace lokaci guda? Waye me wannan Zarran?”
“Bilal mana, taya zaki na abu kina tsammanin ba kallon ki yake ba, kawai abinda zamu duk wani shaidar da yake da ita a lalata shi kamfanin shi ma a rufe”

“Kamar Ya? Taya kike tsammanin zan iya rufe kome na shi kawai nimo min wani hanyar dai”
“Ok wanda na gaya miki bai miki ba sai ki Nima da kanki amma tabbas gudu bai kare miki ba”

“Wannan wacce irin magana ce? Magana ce ta abinda ya dace, idan har zai iya barin kamfanin shi a hannun wasu mutanen me kike ganin zai faru kawai a kona kamfanin shi dukkan Uku”

 "Shuwa! Shuwa!! Shuwa!!!" Aka shiga kwala mata kira,. Cikin fushi ta juyawa tana jiran shigowar Alhaji Adamu da ya shigo cikin fushi.

“Lafiya?”
“Bilal da Atika, Jamilah da Kim Eau sub janye share din su a cikin kamfanin mu, sannan an ce manyan masu hannun Jari suna janyewa daga kamfanin mu Innalillahi wannan Yaron an yi tsinannen.”

Bata gama tsinkewa ba aka kirata a waya.

“Hello Madam ga kizo Yarki tana cikin wani mugun hali?”

“Wacce a cikin su?” Ta tambaya Jikin ta yana mugun rawa.
“Zuhairah Kabir Wazir, an kawo ta asibitin JF Hospital”

"Toh gamu nan" ta fada bata iya gaya musu kome ba, sai da ta fita suka biyo ta, koda driver ya ganta shiga motar yayi suka nufi inda ta gaya mishi. 

      Sai da ta shiga asibitin aka kaita inda Yarinyar take, an lullebe ta gwanin ban tausayi.

“Me ya faru da ita?”
“Wai sun yi challenges din Juna ne, akan kwanciya da maza shine maza uku sukayi ta saduwa da ita tun jiya, kuma ta gaba da baya. Bawai ta wuri guda ba, abin babu dadin gani dan mun kawota nan ko numfashin kirki bata Ja.”
Dabas Hajiya Shuwa ta zauna…
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/13/22, 18:05 – My Mtn Number: 78
   “Innalillahi wa inna alaihil raji’un allahumma ajirni fii musibati wa’akhlifni khairan minha, tun da Alhaji Adamu yake bai tab’a jin tayi salati ba amma yau da ta shiga ukubar rayuwa” dafe goshinsa yayi yana mamakin yadda aka yi wannan tabarar har yarinyar ta shiga. Kafin kace me yan Jarida sun musu caaa.

   A dakin da aka shiga da Zuhairah kuwa bata ko numfashi sai yadda akayi da ita, gaban ta kuwa kamar a saka muciyar tuka tuwo sabida yadda ta bude sosai bayan ta kuwa wato duburanta da zaa saka ba3 zai shiga domin kaca kaca suka mata jini sai zuba yake ta ko ina a gaban ta da bayan ta.
“Hajiya ku saka hannu a mata aiki idan ya wuce lokacin sai dai ta mutu”  dararrafe ta isa gaban likitan tana wani irin kuka.
“Don Allah ko nawa ne zan biya yarinyata ta samu lafiya nake bukata”. Juyawa tayi ga yan sandan ta ce musu.
“Muje”
Suna fita ta ce musu.
“Officer ka nawa ne zan biya don Allah ku kamo min Yaran sai na musu azabar da suka gana mata kafin a mika su.”

   Dariya suka mata sannan daya dan sanda ya ce mata.
“Dukkan yaran da suka yi wannan abun Iyayen su Yan siyasa ne, kuma idan har maganar nan ta fito kina tsammanin zaki iya barci ne cikin kwanciyar hankali? Ko an gaya miki kowa ne irin  Jamilah da kuka mata sharri iyayen yaran ba kanannun takadarirran Mutane bane, dan hakan kawai ki tsaya akan Yarinyar ki domin za a iya biyo ta har cikin a karasa ta, kuma babu wanda ya isa ya hana faruwar haka.”

  “Nawa aka biya ku xan ninka muku goma sau goma na kara muku goma akan goma” dariya suka yi mata sannan suka wuce har zasu shiga motar su dayan ya ce mata.
“Ba zaki iya ba domin an bamu kome domin rufe kundin ki, bamu san da case din ba,  bamu san anyi ba kamar yadda aka tulawa jami’in mu, kuka mishi sanadin barin shi aiki,dan haka mi gode ma da Yarki take Raye bata mutu na ai da wasu ne tuni sun kashe ta”

    Kura musu ido tayi tana jin wani irin abu a ranta, tabbas ba zata bari ba. Ba ta had’a Yaranta da kome amma suka mata haka. Tana gani suka saka kai suka fita bata ce kome ba sai hawayen da yake zuba daga idanun ta. Tabbas dan Adam me mantuwa ne, ta manta lokacin da ta saka ayiwa Jamilah kome, ta manta lokacin da ta saka a kashe Yaran mijin ta yau gashi itama tana girban nata matsalar.

    Komawa cikin asibitin tayi bayan ta biya kuɗin aikin suka shiga da Zuhairah.
Sai dai Fatan nasara kawai, domin a wannan duniyar abinda ka shiga shi zaka girba. Babu abinda zai naka mamaki kamar dan adam da yake da mantuwa, akan idanun shi za ayi mutuwa amma ba zai hana gobe ya cigaba da abinda yake ba, akan idanun shi xaayi kisan kai ba zai hana shi ya cigaba da kome ba, shi da kan shi zai aikata barna kuma ya rayu cikin farin ciki  da nutsuwa matukar burin shi da bukatar shi ba zai kuma damuwa da kome ba, ba zaka ji yayi ihu ba sai ranar da aka tab’a shi anan ne zaka ji ihun shi har da ratattu,yana shaidawa duniya an cije shi bayan shi ya ciji wasu sau babu adadi.

    Baki daya wasu sun dauki rayuwar sama da fadi, gani suke kamar ba zasu mutu ba,kome kan su kawai da yaran su, bayan su kan su abinda suka aikata yana bibiyar su, taya zaka zubda jinin wani kayi tsammanin Allah zai tsarkake  ka? Bayan kai kan ka baka tsarkake kanka ba,  idan da mutuwa tana sallama ce a kofar gidan kowa na rantse da Allah dukkan mu da mun gyara kuskuren mu,amma ina gani nake wannan duniyar lasisin xamanta aka bamu, babu ruwan mu da kowa abinda muka saka shi zamu yi. Gashi nan sun shirya  ta juya ya juyi ya fado kan su bari mu ga me kuma za a sake shiryawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button