WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali suka bar office din.
“Ammih ina ganin kamar aikin Rahmah ne, tana zuwa tana wuni idan yamma yayi na mai da ita gida, Sabida Jamilah.”  Shiru tayi na wani lokaci kafin ta ce mishi.
“Su kuma Yan uwanta fa? Waye zai kula da su?”
Ya san yadda take ji, dan haka ya sunkuyar da kan shi, ya ce mata.
“Allah, fatar mu Jamilah ta samu lafiya.” Kallon ta tayi yana manne da bango kamar ta shige jikin bangon.
“Shi kenan” ta fada bayan ta shiga dakin tana me zama.
“Jamilah na!” Ta kira sunan ta cikin raunanniyar murya. Kallon Ammih tayi tana ja da baya, bata son ta tab’a ta.
“Shi kenan, zauna ba zan Miki kome ba, zauna abinki kinji” ta fada tana me sake wani irin deeper sound na kuka,  yana kallon su kafin ya fita tare da danna wayar shi. A kunne ya saka  yana faÉ—in.
“Abba ya kamata kazo” kashe wayar yayi tare da sakawa a cikin Aljuhun rigar shi.

Daga asibiti Office din Yan sanda ya nufa, yana shiga ya amshi key cell din yana shiga, Baba Haliru ya fashe Mishi da dariya.
“Ka san yadda take ihu ne, ihu take tana jan farcen ta a kasa tana wayyo Malam Aaman, wayyo Allah na Wayyo Allah Wayyo Ammina. Ihu take Lokacin da nake ratsa tsakanin cinyoyinta da maranta, sai ji nayi wani abu me dadi ya sake a jikina. she…” Wani irin duka Aaman ya kai mishi, sai da ya kwara amai.

“Daga yau ko mace ka gani idan ka tuna baka da gaban da zaka kuma ratsa tsakanin cinyoyinta ba, zaka bada labari a wurin da ya dace.” Yana kai aya ya shiga dukar gaban shi, yana dukar shi kamar zai kashe shi, sai da Yan sandan suka leko suna faÉ—in.
“Sir karka kashe shi a kai shi kotu zasu yi sauran aikin.”

Cikin huci ya ce musu.
“Kar ku bashi ruwa, kamar yadda ya iyawa Innocent girl fyade ku bar shi a wurin.”

Ya fita yana jin kamar ya bindige Baba Haliru ya huta, domin zama da irin su, Asara ce babba.

Daga nan ya wuce gidan su Jamilah, ya dauki Rahmah da Wasilah da ita Rabi’ah ya kawo su asibitin. Kallon yaran Ammih tayi ta rungume su, tana jin wani irin kaunar Yaranta, gashi Jamilah ke ciwo amma sun koma kamar sune suke ciwon, kallon su Jamilah tayi, tana wani irin juya kanta, kafin ha fasa ihu. Me mugun karfi dole nurse suka shigo aka mata alluran barci, yadda zata samu hutu sosai. Amma kuma ba zai rage mata kome ba..

Ma_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny

Na
Mai_Damby
Ina mata yan kwalisa ina macen da ta yarda da kan su shin ko kunsan
MAMAN LABIB COLLECTION TAZO MUKU DA TURAREN WUTA MASU KAMSHI DA KAMA WAJE.

kAMAR SU KAJIJI, SANDAL FLAKES, SANDAL BANGE, SUGER CUBE, WHITE SANDAL, HALUT, DORUT, DUKKAN, AKAN FASHI ME SAUKI

Maza garzayo karki bari a baki labari… kayan mu akwai kyau da nagarta ga masu bukata zasu iya tuntubar wannan number sai kun zo👇🏾💃🏼Http://wa.me/+2348144687796

Wata kusurwanp<9>

Littafina na kudi ne don Allah bana son fitina da magana idan baki shirya saya ke daya ba, ki bar min abu na please

Rike Juna sukayi suna kuka kamar ransu zai fita, musamman ganin yadda yayar su ta koma.

“Muje  na ajiye ku gida” gyada kai suka yi, suna kallon Ammih su, a kauda kai tayi tare da rufe bakinta, sai Rahmah da take tare da shi tana kuka itama, babu me rarrashin wani, a waje kuwa Wasilah da Rabi’ah ne rike da junan su, suna kuka har suka shiga motar.

“Lami kin ji labarin da yake yawo a gari? Wai an kama Haliru yayiwa Yar Ishaq fyade?” Ta fada tana kallon Gwaggo Lami. Dafe kirjinta tayi tare da zaro idanu.
“Innalillahi wannan Harirah ta zame mana Masifa, wallahi sai na ci mutuncin ta.” Ta fadawa Asabe, haka ta tashi suka nufi gidan su Ammih.

     Daidai Aaman yana tsayar da motar shi suna isowa.  Ganin yadda Yaran suka razana, sun kasa fitowa daga cikin motar yasa Aaman ya kalli wajen. A hankali ya fito tare da bude musu kofar. Suka fito jikin su yana rawa, kallon su Gwaggo Lami tayi amma ta kasa magana sabida yadda Aaman ya tsuke fuskar shi, yasa ta kasa yin kome. Har sai da yaga shigar su cikin gidan yayi tafiyar shi. Yana tafiya suka shiga cikin gidan.

    “Daga ina kuka fito? Bayan uwarku ta baku lasisin karuwanci. Wato sharrin da uwarku ta yiwa ÆŠan uwan Ubanku shine ya fada kan ku yan kananu da ku har kun san bin maza!”

Tab’ata Asabe tayi sannan ta ce mata.
“Ke dalla kiyi shiru dama kika samu na arziki, sai ki kwashe su ki maida su gabanki kin ga uwar tana can tana jinyar Yayar su, ke kuma Allah ya kawo miki hanyar arzikin ki, sai ki fara daura musu talla kin ga an gama ai.”

Shiru tayi tana nazarin maganar me yasa bata yi tunanin haka ba, dan haka ta shiga dakin su, ta kwaso kayan su.  Ta saka su a gaba suka bar gidan.

         Idan ka gan su sai baka tausayi, haka suka tafi gidan ta, har dare matar nan bata basu abinci ba, Asalima mantawa tayi da su ta fita makota. Rabi’ah tana jikin Wasilah ta saka hannu a baki zunzurutun yunwa, sai tsotsan hannu take kamar yar shekara biyu. Wasilah ta kalle ta,
“Kina jin yunwa ko?”
Gyada mata kai tayi, tana jan hancinta, gwanin ban tausayi.
“Muje gida”
Tashi suka yi, wasilah ta ja hannun ta suka fita.

Bayan tafiyar su, dake matar Ammar ranar barci Gwaggo Lami tazo,  bata san me ya faru ba, dan haka bayan tafiyar su Malam Aaman ya kawo musu abinci. Daga kofar gidan yayi sallama sai Aminah wato matar Ammar.

       Fitowa tayi suka gaisa ya ce mata.
“Ina Wasilah?”
“Ban gan su ba, wallahi domin na zata basu dawo bane har yanzun” dafe goshinsa yayi sannan ya mika mata abincin ya ce Mata.
“TOH gashi idan sun dawo a basu, zan tafi asibitin.”

Ya juya ya tafi, yana tafiya ya shiga da abincin ta ajiye musu, shi kuma ga nufi asibitin, koda wasa bai musu maganar su Wasilah ba. Har zuwa lokacin jikin ta sai godiyar Ubangiji, kawai kuma ga makalewa Rahmah,bata son ko Ammin su ta mata magana, tayi kuka tayi kuka, har ta godewa Allah.  Baki daya ta tsani kanta da kanta, ta tsani kowa a duniya. Itama Rahmah tausayin Yar Uwarta ya hanata sakat, kallon ta take kamar zuwa wani lokaci jikin zai warke amma tana jin muryan namiji zata Fara ihu tare da tashin hankali kamar zata suma. Hakan yasa Dr maza suka daina kula ta dole sai mata suke kula da ita.

Da karfe bakwai Rahmah tayi musu sai da safe sabida ta ga Jamilah tayi barci, dan haka Malam Aaman ya dawo da ita gida, yana ajiye ta ya tambaye ta.
“Rahmah akwai gidan Yan uwanku ne a nan kusa domin dazun na kawo musu abinci basu nan fa?”
Shiru tayi gabanta yana faduwa, domin bata san me zata cewa Ammih ba, can ta bude baki zata yi magana ta hango su, suna dawowa.
“Laa gasu nan ma?” Ajiyar zuciya ya sauke tare da fitowa a motar ya nufe su.
“Idan zaku tafi wuri kamata yayi ku gayawa Matar Ammar, ta sani ba ku tafi dan kan ku ba. Hankalina ya tashi sosai.”

Rike rigar Wasilah Rabi’ah tayi tana kallon kasa.
“Kayi hakuri ba zamu kuma ba!” Inji Wasilah ta fada muryan ta na rawa, baki daya ya lura abinda ya samu yar uwar su, yasa su mugun sanyi tsuguwa yayi a gaban su, kafin ya ce musu.

“Ban ji dadi bane, amma ku kula kun ji, kun ci abinci?” Sake riÆ™e rigar Wasilah Rabi’ah tayi da karfi.
“Zaki yarda ni, idan kina jin yunwa muje kici abincin a ci mana.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button