WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   Mr Ardu baturen kasar Amurika, mutane ruwa biyu me masifar wayon Bala’i, sannan yana iya rike desires din shi saboda bai yarda da matan da suke cikin gamayyar kungiyar su ba,  domin sun fi shaidan shaidanci yake fada.

   “A’a rike hannun ki, sama ban ga wanda yake da purple ba? Kinsan ya kamata yazo nan domin ya amshi kudin caccar shi”  ya fada yana kallon ta.
“Banza, ba zai zo ba sai dai zan kai mishi kudin shi” ta fada tana kara rike kofin wine dinta.
“Da kudi da makiyi dem deserves death, ba zan baki ba kawai bani bayanin shi”  kura mishi ido tayi kafin ta taka gaban shi zata mishi magana P.A dinta ya mata magana.

Murmushi tayi sannan ta ce mishi.
” A tsarin saye da sayarwa muka yi tafiyar dan haka ka gayawa Mr Devd a mai do min da Yarana” daga haka ta juya zata tafi.
“Ke Yar iska kin isa ne? Nawa kike bukata a baki Yara sun rigada sun tafi babu abin jira”

“Dalla miliyan dari bakwai” ta fada tana tafiya cikin NUTSUWA abinta,
“Crazy bitch, ki rage wani abu?”
“Dari takwas?”
“Ashhhhh! Mahaukaciya she driving me crazy. Shi kenan an baki bakwai din harkalla ta fada ko?”
“Wait for me zan dawo kanka dan Ubanka” ta fada tana tafiya,

Tana isa ta budewa Aunty Blessing hannu, murmushi tai tana cewa.
“The she is safe I thought?”
“Yes ma! Yarinyar tana da ban tausayi na damkata hannun da ban sani ba ko an dace.”

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 40

Murmushi tayi tana me mika mata cup din wine, tana murmushi ta cewa Aunty Blessing.
“Duk inda zata shiga ba zata tozarta ba, zata rayu domin kare kanta da kuma inda take tsaye”
Gyada kai Aunty Blessing tayi tana shan wine É—in, kafin aka fara sanarwar akan caccar da aka yi. Inda Hanan tafi kowane dilalli na duniya samun kuÉ—i na fitar hankali, sannan kuma shi wanda yayi zaben purple din yafi kowa kudi a cikin kungiyar sai dai wani abu da ba a sani ba, ko ya daure musu kai ina mutumin yake?

   Babu shi babu labarin shi, dan haka aka ajiye mishi kayan shi, a wani gidan tarihi dake garin Paris na kasar Faransa.
*
Red line life orphanage.

A hankali muke takawa, har zuwa cikin gidan sai kalle kalle nake.
“Kina son nan ko?” Kallon ta nayi, sannan nace mata.
“Ina Aunty Blessing?”  Murmushi tayi sannan ta ce min.
“Aunty ta je sayo miki chocolate, kina son shi?” Gyada mata kai nayi domin nasan shi Steven yana sayo min. Kallon yaran da suke zaune a kasar grass cafet, sai abubuwa suke, kowa da abinda yake yi, da gudu wani yaro yazo ya bangaji Nurse Clara. Murmushi tayi tana cewa.
“Jay kayi a hankali?” Gyada mata kai yayi sannan ya wuce yana murmushi, shafa Aljuhun ta tayi taji babu wayar ta, da sauri ta juya tana kallon shi yana nuna mata.
“Bani wayata” mika mata yayi, murmushi tayi min tana faÉ—in.
“Naga kina mamaki ko?” Daidai muna shiga cikin wani office.

     Shiga cikin muka yi wata dattijuwa ta mike, tare da mikawa mutumin da yake zaune a gaban makeken table.
“Jessica Simpson ga Yarinyar nan!” Murmushi dauke akan fuskarta ta kalli inda muke da Nurse Clara.

“Clara ki kaita dakin su”  juyawa tai tana kallon shi cikin fushi ta ce mishi.
“A cikin yara goma sha biyu muka yi da kai zan cire maka mutane uku, taya zaka mara min ya kai sha uku bayan kasan shekaruna jan baya”

   “Samun nagartattun Yaran da zasu iya daukar kasada muke bukata, sannan dole kiyi shiru da bakin ki, ki dauki yarinyar” ya fada tare da nuna ko in kula.

         Kura mishi idanu tayi, sannan ta juya ta fita daga cikin office din, cikin sanyin jiki. Amma tabbas sai ta dauki matakin akan abinda yake mata, fitowa tayi ta dan-danna wata computer sannan ta wuce waje.

Har ta fara tafiya, sai ta tsaya kamar, jim tayi kafin ta kuma juyawa ta koma cikin gidan,har office din. Tana zuwa sai da ta buga.
“Yes” shiga tayi ta same shi tsaye daga shi dai yar shimi. Ya kwantar da wani yaro yana tura mishi zandarniyar shi a takashi.

“Mr Robert zan dauki newborn din amma sai dai ka bani ita a personal!” A matukar firgice da yadda yake turawa yaron abin shi ya ce mata.
“Ok!!!!” Tsaki tayi tare da b’ata fuska, ta juya abinta ta bar office din. Kai tsaye dakin kwanar daliban ta je, nanny dinnsu ta samu tana gyara musu kayan su.
“Amada, bani yarinyar da Clara ta kawo dazun nan” ta tambaye ta.
“Rebecca!” Ta kira sunana, saukowa nayi daga gadon, na kalle ta ina cewa.
“Yes!”
“Madam Jessica Simpson take miki magana.”
Juyawa nayi na kalli matar, kafin na mai da idanun na kanta.
“Muje” ta kamo hannuna, muka fita matar ta muka shiga, aka wuce damu, zuwa wani unguwa na daban wanda yasa ni fahimtar mun yi nisa da garin, tun daga bakin titin muka sake hannun sai kauyen babu wasu gidaje a cikin kauyen sai dai-dai ku, sannan suna nesa da juna, amma gidan da muke shiga shine ma baya sosai, amma a haka akwai wani gida a kusa dashi. Muna shiga cikin gidan mamaki ta kama ni domin ta fi kama da irin manyan gidajen Alfarmar nan, daga waje babu wani burgewa, sai daga cikin shine zai baka mamaki.

   Kalle-Kalle nake har muka isa cikin gidan, wani katon kare ne ya taso yazo yana shafa jikinta. Yana gani na ya fara haushi. Dan haka ta ce masa.
“Tom” shiru yayi ta rike hannuna har zamu shiga cikin gidan, ta dawo dani, ta nuna fuska na a jikin wani abu kamar Camera ta ce.
“Rebecca sunanta, Yar shekara goma sha daya, idanun ta cikin shi golden ne, fatar jikin ta Caremel, tana da bakin gashi, haÆ™oranta fararre ne masu tsawo,.” Yadda take bashi bayani yana dauka, bayan ya gama ta ce mishi.
“Sai ka shigar.”
“An gama” kallona tayi sannan ta ce min.
“Toh mu shiga.” Komawa gefenta nayi sabida karen na shiga cikin gidan me É—auke da wani irin daddadar kamshi me cike hanci da zuciya, wani irin kamshi me dadin tsiya ne ta ziyarci hancina har da Æ™waÆ™walwata.

    Muna shiga falon ta zaunar dani, sannan ta ajiye jakarta ta wuce ɗakin ta,can sai gata da wasu kaya, ta mika min tare da rike hannuna, ta shigar dani wani daki da yake falon, sannan ta ce min.
“Wannan dakin ki ne, akwai kome a cikin shi. Idan na gama abinci zan kira ki” ta fada bayan ta ajiye min kome ta fita, haka na dauki kayan shima kalar wancan na gidan marayun ne, dan haka na saka dake nayi wanka a can.  Kwanciya nayi a hankali barci yayi gaba dani domin har yanzun ban gama samun lafiya ba, so bani da wani kuzari sai a hankali.

    Koda ta gama abincin ta shigo muje na ci ta samu nayi barci, gyara min kwanciya tayi tare da rufe ni, tsayawa tayi tana kallona.

Tuna hiran da suka yi da Carolina yasa jikinta ya kara sanyi. Idan take gaya mata ta dauki Yarinya.
Jessica har yau zyciyarki bata yi sanyi bane? Kamata yayi zuwa yanzun a ce kin hakura kin bar kome ya wuce, don Allah ki bar kome ya wuce Nicole Brohna ya wuce yadda kike tunani kawai ki mai da yarinyar domin kara sabon nauyi ne

Murmushi tayi tana share kwalla, tare da kallon Rebecca, shafa kanta tayi tana faÉ—in.
“Zan horar dake yadda zaki zame min makami me linzamin da zan cilla shi zuwa gadon bayan makiyana daga yau an fara yakin niman Yanci”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button