WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

    “A’a ni dai”
Haka suka gama musu kafin suka amince tafi tare, mikewar da Rabi’ah tayi ne kafarta yayi mugun tsami, komawa tayi tare da zama tana kallon ta.
“Tafi kawai Karki jima don Allah”
“TOH” sai ta kasa tafiya tana kallon Rabi’atu. Komawa tayi ta zauna, tare da rike hannunta tana faÉ—in.
“Idan ban dawo ba, karki zauna jirana ki tafi idan na dawo kuma zamu tafi tare” ta fada tana share kwalla,

       Sai da ta nufi hanya kamar zata juyo kuma tayi ta fitar ta, Allah sarki tafiyar kenan domin tana isa bakin titi garin tsallakawa wata mota kiran Honda civic, ya kwashe ta can ya watsa ta gefe, a matukar rude mutanen cikin motar suka fito tare da shiga tashin hankali, ganin mutanen wurin babu wanda ya damu da ita, domin ba daya daga cikin su bane, daya cikin su ya ce musu.
“Don Allah wannan ba yarku bace?”lekewa suka yi suna kallon ta,  kafin kowa ya juya suna girgiza kai.
“A’a bamu santa ba!”

“Alhaji kaji basu santa ba.” Dafe goshinsa yayi sannan ya ce mishi.
“Dauke ta mu tafi domin Bauchi muka nufa!”

     A hankali ya dauke ta, duk nufi wani asibitin a cikin Kano, sai da aka gama duba ta, sannan ya kalli Likitan ya ce mishi.
“Ya ake ciki?”
“Alhamdulillahi, ta bugu ne akanta nan da kwana uku zata farka sannan idan da halin ta ga kwararren likitan Æ™waÆ™walwa.”

     “Masha ALLAH, sai dai daga maradi nake, zan tafi Bauchi ne. Don Allah ka kula da ita gobe inshallah zan dawo ga katina suna na Brigedia Aliyu Assadullah Aliyu, zan je gaida surukai na ne, Insha Allah ina dawowa zan kaita babban Asibitin mu da yake nijar”
“Yallabai kayi abinda ya dace kuma zata samu kulawar da yafi namu. Allah ya tsare”
(🤣 Kun ji ba, ta fada hannun Maude me sha’ayi muje zuwa)

              Yana gama cika wasu takardun ya juya ya fita, tare da alkawarin inshallah zai dawo.

..
Lokacin da Rabi’ah taga bata dawo ba,  sai ya mike tare da dingishi, tana niman ta, kasancewar kayan barci ne. Jikin ya, yasa kowa yake mata kallon mahaukaciya, babu wanda yabi ta kanta.

     Wani mota ne mirecende, yayi parking a gabanta. Zuge glass din yayi yana kallon ta, kafin ta ce mata.
“Ki shigo na kai ki gida, suna can suna jiranki”

Kallon shi tayi tana cewa.
“Ban ga Junainah ba, ta tafi gida zo na kai ki gida”

Ya fada yana kara karantar fuskarka, domin yayi amfani da damuwarta ne yake cankar abinda yake tunanin haka ne sai gashi yana canka daidai. Bude mata motar yayi, yana kafar idanun jama’a, tana shiga cikin motar ta rufe tare da jan motar ya manna a guje. Dake Allah ya kawo mu wani irin karni ne, babu ruwan wani da wani.

   Suna tafiya ya mika mata hanky,ta share kwalla a hankali barci ya dauke ta, bata kuma farkawa ba, sai da misalin karfe tara na dare, ta bude idanunta a wani gida,  Yara ne yan uwanta wanda ba zasu wuce sa’o’in ta, kallon su tayi tana ganin kowa yana harkokin gaban shi. Shafa kanta tayi taji babu tulin gashin kanta.
“Hello! Yara” tashi tayi katifar ta, tana kallon su.
“Kuzo muje wurin addu’oi!”

    A hankali ta sauko tana bin yaran har wani daki, me É—auke da alamar Jesus Christ. Durkuwa yaran suka yi har Rabi’ah, wani ikon Allah ta kasa buÉ—e baki tayi magana, dan haka ta durkusa itama, haka suka hada hannun su, tare da rufe idanun su.

Addu’oi aka musu a kiristanci, shiru sukayi can suka amsa da “Amen”

  **
JF Group conference Room.

Taro ne na manyan yan kasuwa da suka zo a gina Kamfanonin JF,  cikin shigar kamala, Ummi  ta shigo cikin room din, mikewa sukayi sakamakon shigowar ta, Faisal  yana rike da jakarta, sai da ta zauna sannan ya zauna.

   Murmushi tayi cikin nutsuwa ta gaishe su, kafin aka fara meeting.  Ana cikin meeting din aka kirata, kasancewar tana bayani, Faisal ne ya dauki kiran.

     Koda ya saka wayar a kunnen shi sai muryan Layinah tana kuka.
“Ya! Sabon mukami, ga Yarki a hannun mu idan kina son ta akwai wani sa hannun da muke bukata ki turawa Dan Yayanki ya saka mana ko kuma dukkan mu nan muyi ta hawa da sauka akan Yarki”

      Rintsa idanun shi yayi tare da budewa ya ce.
“Ba ita bace, Faisal ne dan haka za a muku yadda kuka ce, ku sake Yarinyar”

   “Kai mahaukacin ina ne zamu sake ta bayan bamu samu abinda muke so ba, idan kuka saka mana hannu ku tafi bayan Binta College ku dauke ta” daga haka suka kashe wayar.

       Murmushin  da yake kan fuskar shi ya sa bata fahimci halin da yake ciki ba sako ya tura ta wayar shi. Dan haka suka gama meeting din. Ana fitowa ta shiga cikin office din ta tana cewa.
“Ka kira min Layinah bata kirani ba, na barta zata abuja amma har yanzu shiru.”

Kallon wayar shi yayi domin  baya son ta fahimci abinda yake faruwa, can kuwa sai ga sakon aka ce mishi yazo.
“Ina zuwa Ummin mu”

       Kallon agogon hannun shi yayi, tare da nufar makarantar. Bayan mintinan talatin, ya isa bayan makarantarta, yana zuwa ya samu bata wurin.
Kiran shi akayi tare da cewa.
“Yallabai mun kama su, ga mu nan a Headquarter na yan sanda.”

Akan lokaci ya nufi motar shi.
“Ji mana! Kana da yan uwa ne a makarantar nan?” Juyawa yayi tare da kallonta, daga sama har kasa, zare madubin fuskar shi yayi, a karon farko da yaga wacce unifoam ya karb’e ta, ya kuma dace da jikinta kome na shi ya tsaya cak. Dauke kai yai daga kallon ta.
“Ai yanzu kurma ka koma, Allah ya baka lafiya,” bai bi ta kanta ba, ya shiga motar shi ya barta a wurin. Tabe baki tayi tare da d’aga kafadarta

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:55 – Nuriyyat: Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇🏾💃🏼Http://wa.me/+234 703 003 7697

28
“Wannan mutumin na tausayawa matar shi, kowa yana rayuwa cikin yanci da walwala shi fuskar shi kamar an zage, ba zaka tab’a ganin shi yana murmushi ba irin na mutane. Sai ka ga fuskar shi irin ta Aljanu” ta gatsine fuskar kamar emoji. Can kuma ta kwashe da dariya irin abun ya bata dariya.
“Rahmah Ishaq!” Da sauri ta juyawa tana kallon malamar su.
“Me kike a nan?”
Karamin murmushi tayi sannan ta ce.
“Babu kome Ma’am” wuce malamar su tayi tana sauri.

.. A hankali Ammyn take kokarin bata abinci, ta murmure kamar ba ita ba, kanta a kan littafin da yake gabanta.
“Maza amshi abincin nan mana, bana son kuna zama da yunwa zai tab’a lafiyar ku maza aamu” bude baki tayi ta zuba mata abincin, ta amsa a hankali.
“Ammyn nagode” shafa fuskar ta tayi, cikin tsananin kewar Autar ta.

   “Allah yayi muku albarka, ki nutsu ki ci abincin” ta fada tana me kauda books din gaban Jamilah.
 
“Assalamu alaikum” d’ago kai suka yi a tare, suna kallon shi.
“Wa’alaikumun salam.” Abinda ya faru a tsakanin Ammyn da tattaunawar da suka yi da Iyayen shi ya dawo ranta. Murmushi tayi sannan tace mishi.
“Barka da zuwa, zauna mana” zama yayi yana shafa kan shi. A sace ya kalli Jamilah da take fama da diban abinci tabai ci a hankali.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button