WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

  Komawa zata yi cikin gidan, wani irin kara tayi tare da dafe kirjinta.
“Ka bani tsoro Aaman”
“Dake baki da gaskiya ba, da kina da gaskiya ba zaka ji tsoro ba, Me yasa kike Æ™oÆ™arin ganin kin cutar da kanki da Kannen ki?” D’ago hannun ta yanka ya daura a kirjin shi.
“Har yau ina son wannan matsoraciyar yarinayar nan da take ta kuka nazo na amshi kayana, zuciya ta bata daina dakon jiran ta ba. Kinsan yadda nake ji kuwa? Da kinsani ba zaki barni haka ba” zare hannun ta tayi daga kirjin shi, ta juya zata shiga cikin gidan ya fisgota. Fadawa tayi kirjin shi, zuciyar ta tana wani irin bugawa.

   Matseta yayi tare da sumbatar bakinta, a da kokarin kwacewa take. Amma ganin yadda yake mata, yasa ta shiru bata kuma magana ba, sai da ya kashe mata jiki da sumbatar shi sannan ya janye bakin shi. Yana kallon yadda take sauke numfashi.
A tunanin ta ina ma da Bilal ne ya kashe ta da wannan sumbatar. Baki daya ji tayi.kamar ba a duniyar take ba. Hanata komawa cikin wurin taron yayi tare da zama a wani dan benche a waje.

“Ki bar Rabi’atu tai farin ciki, kema kina da me saka ki farin cikin, kuskure ne abinda kike aikatawa, ban damu ba idan kika ce baki sona, Na yarda amma ba zan yarda na zuba miki ido ki hanata dariya ba bayan ta cancanci haka. Wancan ranar da a ce na bar ammyn  ta koma gida tabbas sa Rabi’atu bata ga rayuwa ba, wannan idan da na kyale masu bibiyar rayuwarki da tuni kin zama babu.

  Rayuwa da kika gan shi kamar labari ce, yau an baki gobe an baki jibi naki zaki bada, idan Allah yana son ka da arziki… Bai kai aya ba, su Bilal suka fito da sauri mikewa yayi yana faÉ—in.
“Lafiya?”
“Wallahi yanzu aka kira Faisal Nadiah Muhammad Alfa tai hatsari motar ta kama da wuta.”

A raxane Jamilah ta kalli Aaman, ta kalli inda su Nadiah suka tsaya wani mugun tsoro ne ya shigeta tam ta rufe idanun ta, tare da kama hannun Aaman. Ta fashe da wani irin kuka…
(Allah yasa haka ya zama sanadin shiryar ta baki daya damu baki daya)
3/17/22, 16:04 – My Mtn Number: 85

Yadda ya hango tashin hankali a cikin idanun ta da yadda jikin ta yake rawa yasa shi fahimtar tabbas fatar shi ce ta tabbatar addu’ar shi na tsawon lokaci ne ya amsu. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon su Bilal yayi musu alama da su tafi, anan ya zauna da ita a hankali yake mata nasiha me shiga jiki.

         Duk wanda yayi yunkurin shiga tsakanin soyayyar su mutuwa ce zata zame mishi abu mafi sauki a rayuwar shi! Da wannan hanyar nake cin abinci idan har na amshi abinda yake hannun ki karshe ni zan tozarta ina son sana’ata

Kalaman Shaman ya dawo mata, wani irin kifa kanta tayi a jikin shi, tabbas wannan wata aya ce da ishara Allah ya nuna mata, da ta sake ta bi su tabbas da tana cikin waÉ—anda za a yi sanarwar hatsarin da su. Dan hakan ta rushe da wani irin kuka, tana kara kankame shi.

   A can inda aka yi hatsarin wuta ce take ci kamar me, baki daya yaki bada damar da za a kashe shi idan aka watsa mishi ruwa sai ya kuma tashi, abin tsoro da tashin hankali, haka ba karamin d’agawa Yan Fire Services hankali ba, domin suna kokarin kashe wutar yana kara kamawa dan dole aka bar wutar sai da ya cinye tass, sannan ya mutu dan kan shi.

   Haka aka kwashi gawan su, aka nufi asibiti da su, Bilal da Faisal tare da Thomas da yake wurin suka nufi asibitin. Koda aka shiga da su har labarin ya iske Hajiya Humaida, wani irin ihu take da fisge fisge, tana kokarin ganin yarinyar ta, abin ba karamin tab’a yayi ba domin.

     Komawa gefe tayi tana kallon kowa da yake shiga da fita, bata kara ko tari ba, a yanzun gani take kamar kashe mata Yarinya aka yi ba wai ita ta mutu da kanta ba, karamin Æ™waÆ™walwar ta ya shiga bata ai da hadin bakin Bilal a mutuwar Y’arta da bai ce zai auri Rabi’atu ba, ba makawa da ba zata mutu ba da ita ce Amaryan shi amma ya tafi ya haÉ—a kai da Uwar shi sun kashe mata Yarinya.

   Sai ta hana shi aure har karshen rayuwarsa, kuma kamar yadda ta ke kashe matan shi sai ta kashe Rabi’atu har shi din ma, domin sai ta gama kunsa mishi bakin ciki sannan ta kashe shi ta kuma kashe mahaifiyar shi,. Sai ta kashe kowa ma tunda suka mata sanadin mutuwar Yarta.

  A ranta tana ji zafi amma tafi jin zafin Bilal domin shine yaja kome, tana kallon shi, har asuba tayi domin a cikin asibitin suka kwana baki dayan su. Wajen karfe biyar ba asuba.  Suka nufi gida, bayan an yayyafewa gawar Mimih ruwa ita da Kawarta.

         Hajiya Humaidah bata kara birkicewa ba sai da aka zo tafi da gawar Mimih, a lokacin su Jamilah da Rahmah da kowa sun zo asibitin. Anan ne ta fara ihu.
“Karku tafi min da Yarinya ta, wallahi bata mutu ba, wayyo Allah wallahi gata tana motsi” wani irin tsoron Allah ne ya kuma shigar Jamilah. Tuna lokacin da aka ce Rabi’ah ta b’ata da kuma yadda aka ce ta mutu, da yadda tayi ta azabtar da Ammyn akan ganin Rabi’ah. Wani irin kuka take.

    Abinda ya faru ya shiga dawowa kamar yanzun abin ya faru.
“Ammyn Rabi’ah ta dawo kuma tana bukatar kwace min Bilal wallahi sai ba kashe ta_

   Afirgice Ammyn ta mike tana kallon ta, jikin ta yana rawa. Bata san lokacin da ta mari Jamilah ba, ta kuma marin ta.
Kika kuma furta zaki kashe ta sai na saÉ“a miki na gaji da halin ki”

Shafa fuskar ta tayi tana kallon Ammyn. Tana faÉ—in.

“Tunda Æ™addaran nan ta same ni, kika juya min baya baki damu da damuwata ba, idan na tab’a Rabi’ah zaki iya min baki idan na tab’a Rahmah kuma me zaki yi”  cikin fushi Ammyn ta rufe ta da duka abinda bata tab’a yi ba, rike hannun Ammyn tayi cikin mugun rashin kunya ta daka mata tsawa.

  “Na rantse da Allah sai na kashe ki!” Ta fada da Æ™arfi, haka ya kashe jikin Ammyn dabas tayi zaman Yan bori, cikin wani irin kuka ta ce mata.
“Jamilah me kike bukata?”

“Ki cire ta a cikin mu idan ba haka ba wallahi sai na kashe kowa, kuma idan kina ganin karya ne, bari na nuna Miki abinda xan iya yiwa kaina”  Fadar haka da Jamilah yasa Ammyn yin danasanin bawa Jamilah farin ciki sama da kima, tana tir da bata damar tai abinda take so.

  Dalili haka ya sa Ammyn hakura da kome, domin ko dan farin cikin da ya dace a ranta tai na dawowar Autar ta bata yi ba, takan zauna tayi ta kuka kuma a wannan lokacin ba tana yi da abinda Jamilah take mata bane, a’a tana yi ne dan tauye farin cikin sauran Yaran ta bawa Jamilah ita kuma gashi bata mai da mata farin cikin ba, a duk lokacin da taga Ammyn tana kuka ta dinga kanannun magana tana cewa.
“Kina kuka ne dan su ba dan ni ba, ni ba dace na samu farin cikin ba su ba, tunda babu abinda ya faru da su, nice dai nake bukatar ki, amma kina juya min baya kamar ba ke kika haife ni ba, me yasa kika auri Abban mu tunda kin san Zuri’arsa ba mutanen kirki bane gashi da wannan tambarin zan koma ga Allah.

        Wani irin kuka ne ya kwace mata ita kanta tasan mutuwa ya fi dacewa da ita ba Rayuwa, domin iya abinda ta aikata ya ci ace tana cikin mutuwar,  bata san me yasa Allah ya tsirarta da ita ba, amma tabbas da tana cikin wannan iftila’in da ya faru da su, haka tayi ta kuka duk abinda ya faru wancan bokan ta gaya mata, kuma gashi ya faru, a koda yaushe zata tayi yunkurin shiga tsakanin su,.mutuwa zata cigaba da bibiyar ta. Bata kuma rudewa ba sai da ta tuna alwashinta anan ne fa kanta yayi mata wani irin kato tana jin kamar iska na shigar mata kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button