WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

 **
Yau tun safe Yoona ya kai mu Rehab, ganin kwararren da zai duba matsalar Jamilah, sai da aka gama mata bincike kafin Dr Lee Junki, sai da ya gama rubutu kafin ya kalle ni.
“Zamu kwantar da ita mu mata jinya sannan zaki na zuwa duk bayan kwana uku sabida kar kewa ya dame ta, duk da Center din akwai abinda take bukata da kuma abinda za ayi akwai nurse da manyan likitoci masu zuwa.” Mikewa yayi ya zauna a kusa dani yana kallon yadda jikina yayi sanyi.
“Idan ya kama ma a mata wankin Æ™waÆ™walwa zamu mata, ta jima da damuwa a ranta kuma ba a magance shi ba,sai aka daura mata wani abu na daban. Duk da nasan kafin Ku zo nan kunyi fama da wasu damuwa akan ta kamar yadda kika min bayani samu taimaka mata mu dai Allah ya bamu Sa’a”
  “Nagode sosai Dr kuma zan yadda kace, zan na kawo mata ziyara” na fada bayan na mike, dakin da Ya Jamilah take na nufa, na same ta tana kuka.
Shiru nayi ina kallon ta, bayan na ja kujeran na zauna. Ina wasa da yar karamar pose din hannuna.
“Adawiyya zan samu lafiya kamar kowa?”
“Eh insha Allah zaki samu lafiya, kiyi hakuri haka Æ™addara take zagaye damu. Allah yana tare da mu” na fada tare da yin kasa da idanuna ina tuno Ammyn last word dinta Kawai nake juyawa a raina.
“Rabi’atu Bilal ya tab’a gaya miki yasan kome akan ki?” D’ago kai nayi na Kalle ta, kafin na ce mata.
“A’a. RABI’AH don Allah ba wai zan d’aga miki hankali bane amma ki tambaye shi sauran Yaran da aka tafi da ku Chioma Abigel da Tara, ya dawo da su gida ne? Suma su kasance cikin farin cikin a cikin ahalin su”
“Ban gane ba? Me kike nufi?” Riko hannuna tayi tana kallona. Kafin ta fara bani labarin abinda Bilal ya gaya mata. Wani irin nauyi ne ya danne min zuciyata. Na kura mata ido kawai ina hango wasu abubuwa a cikin kwayar idanun ta.
Jamilah ba zata tab’a sauyawa ba, tana gaya min na samu Bilal da fada ne ko na mishi me? Me zan yi mishi dan ta gaya min. Murmushi nayi mata sannan nace mata.
“Ƙarki damu zan mishi magana,idan har ya dawo dasu zan gaya miki”.na fada ina mikewa.
Har na isa bakin kofar fita ta ce min.
“Mutumin nan lalata rayuwar ki yayi, sannan da yana sonki ba zai tab’a barin kiyi irin wannan rayuwar ba, Beeyah ki duba magana ta?” Juyowa nayi a hankali na koma wurin zaman da na tashi.
“Too selfish! Son kanki yayi masifar yawa, kina nanne as Ammyn she wishing ba wai dan ni da kaina ba. Ko cire Bilal a rayuwar ki, kawai just mind your own business.” Na fada ina me barin dakin baki É—aya.
   Ina fitowa ne samu Yoona yana jirana, shiga motar nayi tare da kwantar da kaina, ban san me Jamilah take so ba, dan haka na ajiye batun labarin da ta bani nayi na lumshe idanuna. Har muka isa gida.
“Mr Jikamshi ya iso”
Bude Idanu nayi na kalli motar da suke jere, sannan na fita a cikin motar na shiga cikin gidan, a Falon farko na hango shi, dasu Faisal kallon su nayi tare da cewa.
“Barku da zuwa” sannan na wuce abina. Duk da bai da wani jiki can amma kuma naga ya zabge sosai kamar ba shi ba, tab’e baki nayi ina ture batun shi domin nayi alÆ™awarin ajiye shi kome na fuskanci rayuwata.
A ɗakina naga tulin kaya,. Zama nayi ba fara cire takalmina. Fitowa tayi sanye bath dress, dauke kai nayi ina me kwanciya Abuna ina jan siririn tsaki.
   “Sannun da dawowa”
“Hmm” na fada ina kokarin d’ago kai na kalleta amma ta juya min baya. Tabe baki nayi na cigaba da kwanciyata,. Ina lura da ita tayi Sallah ta sauya kaya, tashi nayi zaune ina kallon yadda take gyara zaman mayafin ta.
“Daga ina? Ko daga Africa kike?” Juyawa tayi ta Kalle ni,. Nima kallon ta nake ina son tuna inda na san fuskarta.
“Eh daga Nijar” daga haka ta fita ina lura da Idanunta da suka cika da kwalla. Juyar da kaina nayi ina kallon bango.
“Kamar nasan fuskar ta?” Ba fada da sauri bayan na tashi zaune, da sauri ba fita daga dakin. Na same su akan table. Kallon Umma nayi da take kallona.
“Sun riketa a Rehab din ko? ” Ta tambaye ni.
“Eh zasu bata maganin wata biyar ne, umma ina kallon wancar fuskar kamar na santa long time ago”
” Ok ki Æ™addara ita din da kika sani ne”
Rike bakina nayi ina kallon umma nace mata.
“Umma Junay” ns kalli inda take, kamar ba ita ba, da mugun gudu na isa wurin ta tare da ture abincin na haye jikinta.” Itama kuka take kamar me haka muka tashi muka wuce dakin Ya Wasilah ta kawo mana abincin.
“Auta ki ci abinci dan na lura mika baki don son cin abinci baki daya”
“Eh wallahi bari naci yau tunda ga Bestie na”
Zaka abincin mukayi ina ci muka hira, muna gamawa ne, na fara bata labarin rabuwar mu a wannan dan karamin garin.
“Hatsari nayi ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai bayan wata biyu da aka min aikin Æ™waÆ™walwa. Sabida hatsarin da nayi na bugu a kaina. Adawy na sha karamin wahala, amma wahalar na kewar ki ne, Adawy Allah ya kawo mana karshen azzalumai kawai”
  “Amin Ya Allah” tuni na sake na samu yar uwa,. Ya Rahmah tayi iya kokarin ta ina shiga kitchen koyar girki da suka ishe ni na ce musu.
“Ku kawo min computer zan iya muku kowani irin hacking girki ba hubby na bane,. Daga ni har My future husband bamu da yawan ci idan ma muka haihu ba zamu koyawa Yaran mu cin abinci ba, gudun kar su koyi cin da zai dame ni” na fada ina barin kitchen É—in da suka zauna suna mita Umma ta ce musu..
“Ku kyale ta. Mijin ta da zata aura zai daukar mata me koya mata girki.”
  …
“Faisal baka ga abinda take min bane? Yarinya kamar wata babbar mace, sai dan banza shariya” murmushi Faisal yayi yana kallon Bilal yayi tare da cewa.
“Toh idan bata ja maka aji ba uwar me zata yi? Ina son mace me class, ba irin marasa kamun kai musu niman maza ba su aure ba, Malam Yamzun xaka san me ake kira da soyayya duk auren da kayi sha’awa ce kadai da kare kai.”
“Ban gane ba! Dama can ba soyayya nayi ba?” Kura mishi Idanu Faisal yayi tare da cewa.
“Kana sane da abinda ka fada shekarun baya matar da zaka so zaka bata kariya, lokacin kuwa ko tudun Kirji babu a tare da ita, yanzu kuwa da ta cika dama da kasa ai wallahi karya kake kace ba zaka duka mata ba”
“Kai bana son shirme! Babu wani soyayyar da zan yi kawai zan rage time ayi bikin mu kawai” ya fada yana tsare gida.
“Insha Allah ba zata yarda ba, domin ba sakarya bace da zata yarda a aura mata kai babu soyayya sai kace zamanin jahiliyyah,”
Faisal bana son hada husuma, taya zaka ce zamanin jahiliyyah bayan nasan mun jima da barin wancan era din kawai zan shiga na fita.”
“Ba irin su Rabi’atu akewa wannan abun na muje zuwa….
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/15/22, 07:53 – My Mtn Number: 79
Wata ƙatuwar harara ya watsawa Faisal yana faɗin.
“Banza mara kishin dan uwan shi, baki daya auren wancan yarinyar y mai da kai wani irin mutum ko kishin dan uwanka baka yi”
Dariya Faisal ya saka yana kallon Bilal sannan ya ce mishi.
“Kasan Allah babu rashin kishin kai, kawai ka nime soyayyar ta kafin aure,karka sake ka tafi kamar wani robot” daga haka suka sake hiran.
 Muhammad da suka zo da Junainah sai da yayi kwana uku, kafin muka raka shi Airport,muna tsaye jirgin su ta tashi zuwa kasar shi. Ajiyar zuciya Junay ta sauke na ce mata.
“Lafiya?”
“Adawy Muhammad shine Æ™addarata, ban san yadda zan miki bayani ba, amma ina cikin damuwa, bani da sake matukar yana wuri”