WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

….
Kasancewar gawan ana kawo su, aka kira masu fixing din su, suka gyara gawar. Aka mata dressing sannan aka sakata a cikin akwatin ta, kuka mahaifiyar ta, take kamar zata shide ita ce kawai Y’a mace, gashi dan mugunta har da Yaron su aka kashe balle a samu wanda zasu na tunawa da ita.

      Wajen karfe shida na asuba, jirgin saman emirate ya sauka a garin Busan, sai da aka ɗauki lokaci. Bayan fasinjojin sun sauko ya fito a hankali, P.A din shi yana biye da shi Khalil Ibrahim Khalil. A tare suke sauko yana bin bayan shi.  Har suka shigo cikin arrive, da sassarfa Faisal ya iso gare shi, suka rungume juna.

“Ya isa Man” janye jikin shi yayi, sanye yake da sweater suit sai farar shirt na Nike, sai dogon wandon shi jeans brown. Fuskar shi toshe da sunglasse wanda ba zai nuna raunin da ya ke cikin idanun shi,. Ya boye shi cikin duhun madubin sai dai ya gaza boyewa akan fuskar shi domin tayi jajjur.

    Jerawa sukayi a tare suna tafiya babu wani abu da ya shiga tsakaninsu, but haka ya rage mishi nauyi da yake zuciyar shi domin yana da ciwo a rayuwar anya zai iya sake ya saka rayuwar wata Y’a mace a hatsarin da ya saka sauran? Ina ma hannun agogo zai dawo baya tabbas da yayi abubuwa dayawa. Har wurin motocin da suka zo daukar shi ya nufa. Faisal da P.A Khalil Ibrahim Khalil, suka bude motar shiga yayi Faisal ya shiga daya gefen Khalil ya shiga gaba, tare da É—aukar wayar da take ringing na ubangidan shi.

  Kwantar da kai yayi yana jin wani kunci a ran shi, duk da duhun asuba ne, amma ba zai hana ka hango damuwar da take shimfide a fuskar shi ba.  Motar shi ce ta fara bin jerin gwanon sauran tafiyar minti goma kacal ya kai su gidan su, haka ya fito daga cikin motar.

   Suna bin bayan shi, kallon agogon hannun shi yayi, a tare suka wuce part din shi me girman bala’in gaske, tunda ya nufi part din wani irin kewar  matar shi da dan shi suka dawo mishi. Yana shiga falon shi ba farko ya zube a sofa, yana sauke wani irin kwalla masu zafi, ta gefen idanun shi kan shi a jingine da sofar. Rabon shi da kuka tun mutuwar mahaifin shi yau yana kuka domin iyalin shi me zai yiwa halin Jikamshi ya huce da abinda suke mishi, yasan ta kowani bangaren yana da makiya amma ba zai iya cewa kiyayyar su ta kai su illata shi ba, sai yanzun Meye ya musu da zafi haka?

    A hankali Faisal ya zauna a kusa dashi yana kallon yadda yake kokarin boye kukan shi.
“Ba zan hanaka kuka ba, amma kayi hakuri har yanzun akwai lokaci zaka iya kuma nasan zaka yi din ne,amma dole ka kayi hakuri da lokaci da”

Mikewa yayi a hankali ya nufi dakin shi da yake can gaba da wani corridor, ya shiga da sallama, sannan ya nufi ban daki kayan jikin shi ya cire, yana kallon kome a shirye,  ji yayi kamar zuciyar shi zata fita haka ya rage kayan jikin shi ya fara, kokarin yin wanka.

Asalin Labarin.

Bilal Ahmad Jikamshi, wanda mahaifiyar shi take kiran shi Gong Yoo, da Yaren korea, Da ne ga Alhaji Ahmad Abbas Jikamshi,  shahararren dan kasuwan karon da karafuna na yankin Afrika baki daya, attajiri ne da ya cika ya tumbatsa da dukiya kafin ya koma ga Allah.

Malam Abbas shi ya haifi Ahmad, yan k
Gudumar  Jikamshi ta jahar katsina. Kafin nan Malam Abbas dan kasuwa ne, da yake fatauci tsakanin arewa da kudancin Nigeria, yana kai shanu da awakai Allah yayi mishi dinbun arziki kasancewar shi bafulatanin garin jikamshi, sai dai wani abu daya yana da mata Biyu.

      Marka itace uwar gida  tana da Yara biyar sai Yadiko wace sunanta Adama, tana da Yara biyu kasancewar yaranta wabi take yi, idan ta haifi Yaran basa amsa sunan su suke komawa. Dakyar Allah ya taimaka ta samu Yara biyu Ahmad da Atikah.  Shima kuma Malam Abbas yana mugun son Ahmad da Atikah, dan gani yake kamar zasu rasu suma, abinda yake wa Marka ciwo kenan ta fito da kiyayyar Adama da Yaranta.
Yaran Marka sun haɗa, Adamu, Abubakar, Abdulkadir,  Humaidah da Turai, wacce sunanta Dayyibah.

   Tun suna yara suka tsani Ahmad da Atikah, Sabida suna ganin kamar Baban su yana fifita su Ahmad akan su, a da can Yaran basu karatun boko sai na Muhamadiyya, wani kai kaya da yayi lagos aka damfare shi, suka cuce shi, yasa yana dawowa bai yi wata wata ba, ya watsa yaran a makarantar boko. Adamu da Abubakar guduwa suke, Turai da Humaidah basu zuwa sai su fake da basu da Lafiya, daga Ahmad sai Abdulkadir da Atikah suke zuwa makarantar,. Aikuwa baki daya Malam Abbas ya daura musu soyayyar duniya, kiri kiri yake musu hidima bayta haɗawa da sauran, sai wani sabon kiyayya ya kuma darsuwa a ransu, tare da cewa ai Yadiko Asiri tayiwa Abdulkadir, yake zuwa boko dan ta rabasu da shi.

Babu laifi dukkan su uku sun mai da hankali, ganin kamar kannen su zasu tafi su barsu, yasa suka yi maza suka koma Makarantar suma.

Haka suka yi ta gwagwarmayar karatu, dake Humaidah da Turai suna da garin jiki, iyakar su sakandari suka yi aure kuma a gidan auren su basu zauna haka ba, domin mazajen su yan boko ne.

     Ahmad ya kware a lissafi, yasan me ake kira lissafi. Dan haka lokacin da ya gama sakandiri, kai tsaye ya samu jami’ar Ahmadu Bello da ke zaria, anan ya karanta lissafi,  inda ya samu degree din shi na farko, ganin kwazon  shi da hazakar shi yasa ya samu scholarship zuwa kasar Russia,  anan ya had’a masters din shi,. Aikuwa suka nemi rike shi yace bai iya ji ba. Shima zai dawo kasar shi.

   A shekara ne Allah ya haɗa su da Kim Eau wacce sun zo yawon shakatawa ne da iyayen ta, kasancewar Mahaifin babban dan siyasa ne, aikuwa tana ganin Dan mutane Katsina ta Hauka ce, tace tayi miji duk yadda mahaifinta yaso ta hakura amma ina ita ce babbar Yar shi sai me Binta Kim Jong, ganin tana kokarin guduwa wurin Ahmad yasa Mahaifinta yazo har makarantar su Ahmad, suka yi magana bai ji kome ba domin shi lokacin da yake jin labarin mamaki yake bai taba ganin ta ba, idan ma yana ganinta bai dauka da gaske son shi take ba, dan tun zuwan shi bai bada fuska wa yan matan turawa ba.

    Dan haka bai wani ga abin kunya ba, sai ya amincewa mahaifinta, amma bai yarda da ayi aure a wata duniya ba, gwara su koma garin su zai zo da mahaifin shi.

Bayan mahaifinta ya zo mata da zancen aikuwa ta buga tsalle ta fita da gudu sai gidan da Ahmad yake, tana shiga cikin gidan, ta samu yana abinci a kitchen.  Kallon dakin take ganin yadda yake cike da lissafi yasa ta kara mutuwa akan shi, dan haka yana zuwa ta bayan shi.

    Ta rungume shi, jikin shi ne yayi sanyi ya dawo da ita gaban shi yana kallon ta.
“Me yasa kike son aurena?”
“Abubuwa dayawa, amma basu suka dame ni ba, kawai ina sonka ne da gaskiya da kuma zuciyata, shine gaskiyar abinda na sani.” Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mata.
“Iyayena basu kai iyayen ki ba, asalima abinda kika gani ba shi daki samu ba”
“Idan har ina sonka da gaske ko a karkashin kasa kake raye zan zauna da kai haka kai nake so ba daukaka ko dukiya ba”

     Ya kuma kallon ta kafin ya ce mata.
“Ni musulmi ne!”
“Babu damuwa, na maka alÆ™awari duk Yaran da zamu haifa addinin ka zaku suyi.” Ta fada tare da mika mishi hannu.
Riko hannun ta yayi tare da saka nashi a cikin shi yana faÉ—in.
“Nayi miki alkawarin bawa Rayuwar ki kariya har karshen rayuwata.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button