WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

         Turo kofar dakin aka yi, likitan da yake duba matsalar Jamilah ne ya shigo dakin ya ganta a bakin kofar shine ya shigo da ita sai zare idanu take kamae makaryaciya.
“Ina Auta?” Ammyn ta tambaye,
“Tana gidan Gwaggo Lami” ta fada tana zare ido.
“Ya me jikin bari na duba dakin gaba na ga tana barci” inji likitan.
“Ayya kayi hakuri na ga wasilah na manta da kai, tana barci ma”
Jinjina kai yayi sannan ya ce mata.
“Toh Alhamdulillahi.” Ya juya ya fita.

    Ajiye mata abinci Ammyn tayi tana kallon ta, tayi wani zuru zuru.
“Kuma kika barta a can? Hm” kawai tace amma a kasar ranta bata so zaman Rabi’atu a can ba, amma babu yadda ta iya domin, tunda koda ta nuna damuwarta akan Rabi’atu ba zai magance kome ba dan haka ta ce mata.
“Kin je makaranta yau?” Ta tambayi wasailah, kallon ta tayi da idanun da suka ci ciko da kwalla kafin ta sunkuyar da kanta kasa, kwalla na zuba mata.  Na tausayin Yayar su. Cika bakinta tayi da lomar tuwo, kafin ta ce.
“Hm da naje sai gulmar mu ake har da tambayana” ta fada tana kuka, bata fasa cin abincin ta ba, shiru dakin ya dauko. Ammyn bata ce mata kome ba, sai dai da ciwo a ce irin wannan al’amarin yana faruwa.

Har dare suna asibitin kafin Sadam yazo ya dauke su, domin Aaman baya gari ya tafi Lagos wurin mahaifin shi.

      Yana sauke su a gida suka shige, tare da rufe gidan, suka nufi dakin su suka kwanta, sai dai dukkan su babu wanda ya iya rintsawa sabida Rabi’atu bata cikin su.

..
A can gidan Gwaggo Lami, tunda suka lakada mata mugun duka, suka barta a wurin a yashe, ta suma. Har dare sai da mijin Gwaggo Lami ya dawo kasuwa ya ganta a wurin ya fara fada da cewa.
“Taya zaki bar yarinya a mugun hali kin san ba zaki rike ta ba, kika tafi kika dauko ta ni bana son mugun hali” sanin cewa yana da zafi da fada yasa ta ja Rabi’ah zuwa wani dakin tsumokara ta watsata tayi tafiyarta. Tun daga nan bata kuma bin kan Rabi’atu ba, har dare itama dake dogon suma tayi bata farka ba sai goshin Asuba, tana buÉ—e idanunta ta ga duhu, ihu ta fasa tare kame jikinta wuri guda, tana kerma rintsa idanun tayi bata iya bude idanun ba, sai da taji saukar ruwan sanyi akan ta a lokacin ta sake ajiyar zuciya, bata gama dawowa daidai ba aka rufe ta da mugun duka, sai da ta mata likis dan mugun ta, gashi duk dukar da zaka mata bata kuka ba zata tab’a bude baki tayi ihu ko kuka ba.

         Da gari ya waye da jikakken kayan ta daura mata tallar, yau ma kamar jiya haka Buhari ya mata mugun duka, ya dawo da ita hanyar gida, tana kaiwa gidan ta samu ba Gwaggo Lami, baki daya suka mai da yarinyar jaka karfi da yaji.

    Washi gari ma haka abin ya kuma faruwa dan haka tana masifa tana zagin Rabi’ah tare da tsinewa Ammyn, shigowar makociyarta Asabe ta zauna tana cewa.
“Yau naga me kashin mindiriki, idan taki ba sai ki had’ata da yar duwala ba, yanzu ta kawo min kudin aikatau din sailuba”

     Gwalalo idanun tayi tare da rike habb’a ta ce mata.
“Don Allah asabe? Kudi dayawa kuma?”
“Wallahi dubu sha biyar, kuma na rantse renon take kawai! Kin gan shi” ta nuna mata damin kudin.
Shiru tayi kafin ta ce mata.
“Toh ya kike ganin zan yi da ita, domin kar abin ya zama tashin hankali”
“Kwantar da hankalinki, yar dan uwan ki ne, babu me Miki magana idan wani abu haka ya taso, dan haka jibi yar duwala zata koma su tafi tare domin akwai wasu Yaran har biyu zata tafi dasu.”

       Shiru tayi kanta a kasa tana nazarin yadda abin zai zo mata babu matsalar mutane da uwar Yarinyar, d’ago kai tayi tare da cewa.
“Toh bari zan yi shawara da Yar uwata duk yadda muka yi zaki ji ni.”

“Amma Æ™arki sake wannan damar ta subuce Miki domin kuwa irin wannan damar sau daya take zuwa miki, idan kika yi sa’a, har auren ta su zasu mata kayan daki.” Inji Asabe, a hankali take korewa Lami bayani da yadda kudi suke shigo mata a matsayin na aikin Y’arta. Abin ya kuma cika zuciyar lami da kwadayin samun abun duniya tunda har kaya ake kawo musu daga gidajen aikin Yaran su,  sannan ta gaya mata ai ta koyawa Rabi’ah kananun dabaru.

“Dabaru kamar ya?” Gyara zama tayi sannan ta ce.
“Kin san Sahurah ba ni ce na haife taba, Asalima yar Kani na ce da aka ya haife ta a can inda yake cirani ina ganin kamar kunsawa Uwarta cikin yayi shine suka kawo min ganin abin kunya zai ishe ni, na dauke ta na bawa Yar duwala, kafin nan na gaya mata idan ta samu yan kananu canji ta kwashe, idan me gidan ko Yaron gidan ya ce zai yi wasa kwakule da ita zai bata kudi ta amsa tayi shiru babu kome ai ba sakawa zai yi ba, dan suma suna gudun abun kunya, kin ga kuwa ai fata lafiya nama lafiya, yanzu bayan kudin aikinta ta bawa Yar duwala dubu biyar kyauta ni kuma ra turo min da wasu goma kin ga idan ba hada da kudin aikinta ashirin da biyar da ba wurin yar duwala talatin ga kaya, ga naman kaji kai abin sai san barka”

“Ikon Allah, dama akwai hanyar arziki haka baki gaya min ba, wallahi dole ma taje kin ga gobe ma idan ta shirya su tafi idan yaso nasan yadda zan bi da kowani shege babu me min iko da yar dan uwana, ai na jima ina son na am shi abata!”

      “Kin ga kin kashe bakin kowani shege kuma wallahi karki ga yadda Sahurah ta koma Æ™atuwar budurwa, gwanin ban sha’awa, naso wannan zuwan su zo tare toh matar da take wurin ta wai zata yi tafiya kasar waje, shine zata kaita gidan iyayen mijin su kuma Æ™arki ga yadda yarinyar take samun kulawa, gashi tana zuwa mahamadiya ai yaro ba zai manta karatun sallah ba “

Gyara zama Gwaggo Lami tayi tana kara jin harkan arziki, ta ce.
“Na dafa ki da arziki kina nufin har makarantar Muhamadiyya aka saka yaran? Gaskiya sun cab’a”. Aikuwa Asabe ta tunkudo dan kwalinta gaba ta ce mata.
“Toh kiji in gaya Miki a gidan da Sahurah take aiki akwai Yaron gidan da ya auri wata yar aikin gidan, suna kasar waje yanzu haka, dan haka nake gaya Miki arziki ne aiki da masu kuÉ—i”

       Sake baki tayi kamar doluwa, daga jin batun arziki har haka, dan haka ta karkace kai ta ce mata.
“Ai idan wancan me fuska kamar an dama kashi ta samu miji a can wallahi sai dai a sauya da Sakinah yar wajen Bashariya domin bana kaunar shegiyar can su cigaba da uwarta kuma kudin aikin ba zai shiga hannun Uwarta ba, domin billahi ba zan yarda ba”

“Ke waye ya aike ki, ai ko kin ce zaki bata na tsine miki albarka, ki ji in gaya miki, yarinyar nan shine nake fatar ta samu wani Yaron gidan ya aure ta, Nima ko zan huta yar duwala take gaya min, na rantse Miki da Allah arziki ne a wurin va na wasa ba”  cikin zumudi da masifaffen gulma da son zuciya, ta kara zama sosai ta ce mata.
“Toh ya suke biyan kudin aikin  domin na san yadda zan ajiye a bata kafin lokacin yayi.”

“Gaskiya ni duk bayan wata uku ake kawo min da shatara na arziki, kin ga su dubu biyar biyar ake biyanta duk wata” ta gayawa Gwaggo Lami.

“Dubu Biyar?” Ta tambaye ta cikin al’ajabi.
“Kwarai da gaske, domin kuwa gasu nan na wata uku”
“Ikon sai na ja’u, kuma wani irin aiki take?” Ta kuma tambaya,

Cikin izza da jijji da kai irin na wanda ya isa da kuma samun da yake ta ce mata.
“Reno mana, renon yaron gidan take, kai naga abin mamaki, dole ma masu kuÉ—i su huta, irin wannan arzikin haka ke ko kayan da aka bata…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Leave a Reply

Back to top button