WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
  Sauran Yaran suma da suka gama barci kowa ya fara, sai la’asar suka tashi, aka basu sabulu me kamshi da soson wanka, sai man shafawa me kyau da turaruka, manyan matan aka basu shaving cream su gyara hammatar su, Altine soso biyu ya dauka ita da Rabi’ah, dan haka ta je musu ruwan wanka ta shiga ban daki ta farawa Rabi’ah, ganin yadda take tsoron ruwan sanyin yasa ta fitowa niman ruwan zafi.
“Yar duwala babu ruwan zafi ne?”
“Yana can baya ku diba.” Haka ta nufi bayan ta diba musu, ta kai ban daki ta mata wanka tass, sannan ta wanke mata sumarta duk da ta ganshi a yanke, amma ta wanke shi da suka fito aka shiga tambayar su.
“Waye yake da kwarkwata, amasali, kyashi da kuraje, yayi magana za a bashi magani, masu gashi suyi magana a fara gyara musu kan su.”
Haka yaran suka fara fitowa ana gyara musu gashin su, sai da Altine ta gama wanka ta fito ta shirya Rabi’ah, sannan ya dauki kayanta ta wanke, wanda ta cire, ta saka mata wani. Sannan ta kawo ta aka fara gyaran gashinta, masu gyaran gashin sai da suka yi magana da cewa.
“Waye ya sake mata gashinta? Yarinyar tana da kome me kyau sai a sake mata kar a kuma tab’a mata gashinta”
“TOH” inji Altine,
   Har dare duba su ake ana basu kulawa, zuwan likitan da wasu abokan aikin shi, aka shiga duba su kamar me, tun karfe bakwai na dare har zuwa sha biyu na daren aikkn su ya tsaya akan Rabi’ah ce, dan haka suka kalli Juna, kafin Dr Musa ya ce mata.
“Yar duwala wannan yarinyar a kawo ta asibiti, domin zamu duba ta, ki lura yadda take komawa gefe bata son zama cikin jama’a, sannan da muka zo zamu dubata kin ga yadda ta razana ta Niman suma mana, a kaita birnin kudi zan duba lafiyarta a can, muga abinda hali zai yi.”
  “Shi yasa da na ga ta kawo min ita naso naki, Allah na tuba Meye za a yi da wannan domin dai tayi kankanta, kawai shegen son kudin mutanen kauye ne na tsiya.” Dariya suka mata sannan suka mata sallama suka bar gidan tare bada nufar asibitin su da suke aiki.
   Ita kan Rabi’ah tana samun jikin Altine ta lafe, sai ajiyar zuciya take, shafa bayanta Altine tayi tayi har suka kwanta, kasa barci tayi tana kuka. Dole Altine ta tashi tare da janyota ta sakata a jikinta, ita kuwa ta k’amk’ame ta, kamar zaa kwace ta daga jikin Altine.
  Daƙayyawa
Kowa yana barci amma ban da Ammyn da take tsaye a bakin kofar gida, Ammar yana tsaye a kofar dakin su, wannan shine karo na biyar da take fitowa tana leka waje, tare da kokarin kwala kiran sunan Rabi’ah, kunnenta ne yake jiye mata ihun Rabi’ah shi yasa take fitowa ta duba, ko ta wajen babu ita babu labarin ta, haka ta rufe Kofar gidan ta koma.
“Ammyn Jamilah, kiyi hakuri Rabi’ah fa bata nan, Kiyi hakuri Allah zai dawo Miki da Yarki cikin koshin lafiya. Amma ki mika Alamarinki zuwa wurin Allah yana ji yana gani shi rayayyen nan ne da baya mutuwa, haka da kike yi zai iya haifar Miki da wani ciwo na daban, kin ga idan aka yi rashin dacen sai ki rasa rayuwar ki baki ga Rabi’atu ba, amma idan kayi hakuri Rabi’ah zata zo kamar daga sama, balle nan da wani lokaci ne zata dawo gare ki Insha Allah.”
“Toh shi kenan, tunda kace zata dawo bari naje na kwanta, toh wa ya sani ko bata ci abinci ba, a ina take kwance, a hannun waye take? Tayi barci ko bata yi ba? Kaga duk ban sani ba, dole na damu Rabi’ah tayi kankanta tunda abin nan ya samu Jamilah Yan uwanta suka gaya min bata barci, waye ya sani ko bata da lafiya ne, ai ko jiya da naje gidan Lami na samu bata da lafiya, ka ga dole zuciya ta, ta damu waye zai yi jinyarta?”
Yadda take maganar zaka fahimci damuwa ya taba brain dinta domin maganar da take tayi yawa kuma bata hadiye numfashinta take sake wasu dan haka ya juya tare da shiga dakin su, ya dibo mata ruwa ya mika mata.
Sannan ya ce mata.
“Zauna ki sha” babu musu ta zauna a kujeran tsuguno na matar shi da ya dauki mata, shan ruwan tai sosai.
“Ki godewa Allah, Ammyn” ya fada mata,
“Alhamdulillahi” a hankali taji wani abu ya taso tun daga cikin ta, sai da ya hauro wuyarta ya tsaya cak, shi bai sauka ba,. Shi bai fita ba kuma sai ya haifar mata da shakuwa, haka ta sha ruwan sosai kafin ta daina shakuwar..
This is the Beginning….
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:53 – Nuriyyat: Yau da Gobe<18>
Haka ta kuma shan ruwan sosai, sannan ta juya ta koma dakinta, lokaci guda taji kukan ya tsaya cak tayi ma ta kasa, tashi tayi kamar zata fita sai kuma ta koma cikin dakin tayi alola ta fito ta daidaita nutsuwarta sannan ta fara gabatar da sallah. A hankali ta shiga jin wani irin nutsuwa yana sauko mata, har ta idar da Sallah, ta d’aga hannu sama tana Addu’a, ta jima tana kai kukanta wurin Allah, kafin ta sauke hannun. A wurin ta kwanta, cikin tsananin kewar Y’arta da aka raba su, ajiyar zuciya take saukewa a hankali har kusan asuba.
   Dake ta saka abun a ranta, sai gashi tana mafarkin Rabi’ah, gata ta dawo mata, a firgice ta farka tana juye juyen niman rabi’ah, lumshe idanun tayi a hankali taji kamar tayi kuka, ko tayi ta ihu, amma wannan abinda ya tsaya mata a makoshi ya hanata koda jan numfashi me kyau ma.
Har aka yi sallah Ammyn bata kuma rintsa idanun ta ba, haka ta tashi su Rahmah da suma suke cike da kewar Kanwar su, da gari ya waye ta koma bakin kofar shiga gidan ta zauna, tana me jin a ranta zata iya spend time dinta da rayuwarta wurin jiran Rabi’ah, zata zauna tayi ta dakonta har Allah ya nufa ta dawo, haka Ammar ya fito ya gaishe ta, sannan ya nufi kasuwa, Rahmah da wasilah suka kama aikin gidan, Jamilah ce kawai take daki, itama haukatar ta yayi sauki ko nace firgitan da take yayi sauki sai dai bata cika magana ba, kuma dama haka halin ta(idan mai karatu ya koma baya zai fahimci haka)
  Sai gashi dalilin fyaden ya kuma mai da ita wata irin miskila mara son magana, Kai ko yan uwanta ne bata musu magana, balle kuma Ammyn. Tana ganin su baki daya sai ta zama wata irin mara son shiga kome kuma ba lafiya ce da ita ba, balle kuma ta shiga harkokin su.
   Bayan sun gama abun karyawa, Rahmah ta shigo da abinci, ta ajiye musu abinci, sannan ta dauki pillow ta ajiye a kasa kafin ta ce mata.
“Yaya Jamilah sauko ki zauna ga abincin ki fara ci kafin mu shigo.”
  Shiru tayi bata amsa mata, har ta fita ta dawo, bata motsa ba kuma Rahmah tana ganin ta tana motsi, amma bata amsa mata ba, dan haka ta fita tare da dauko Ammyn daga kofar gida ta kawo ta cikin dakin, kafin ta kwalawa Wasilah kira tazo su ci abinci. Ganin yadda Ammyn ta koma kamar babu hankali a jikinta, abin da ya tsayawa Rahmah a rai kenan, ta fashe da kuka cikin fushi da b’acin rai ta ce musu.
“Nayiwa Jamilah magana bata kula ni ba, Ammyn na dauko ki daga waje ki karya kin zauna kina kallona, Ammyn ke Mahaifiyar mu ce, idan kika yi rauni muna haka zamu zama masu rauni, Ammyn kece kwarin gwiwar mu, don Allah ki daina kuka ina Rabi’ah ta tafi?” Ba tayi shiru ba tayi ta daina fadar abinda yake damun ta, wanda yasa su kuka dukkan su, sannan ta cewa Ammyn.
“Ban ga laifin ki ba, dan kin damu akan mu, amma Æ™arki manta dukkan mu mata ne idan muka koyi rauni a wurin ki a ina zamu koyi juriya da hakuri? A ina zamu koyi tawwakali da iklasi ? A wurin ki zamu koya, don Allah ki daina kashe mana kwarin gwiwar mu, kin ga yadda Yaya Jamilah ta koma “