ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Kowani ango awannan daren ya maida amayarsa cikakkiyar mace,Abun ba ragowa ko kadan da alamu dai sunji maza,Ammh dukkansu sun tsinci kansu cikin wani nishadi mara misalatuwa jabir ne yace aransa”Dama Tuni irin wannan Dadin gayen chan ke kwasa,lalle dole yacemana yara,ammh wlh danasan haka aure keda dadi da Rahama da wlh Tun da na balaga zanyi aure,domin na mori Abun da kyau????kuji fa jabir daga Shiga sau daya yafara sambatu,shidai Umar Tuni ya wuce sansaninsu,ammh shima kasan Ransa yana Cewa ne daya koma kasarsa zai nemi mata yayi aure,shima ai ba Dutse bane.

Sati daya cur su goggo sukayi suna hutawa kafin sukoma kasar Niger,koda suka koma Tuni yan uku sun kara girma da yau kamar ba yan wata daya ba,Fati itace suke cema Afra,sai suwaiba suna kiranta Afiya,sai Namijin suna kirana Anwar,Azeema kuma na cigaba da samun kulawa sosai gimbiya Razeenah na kokarin saka ido akanta kada tayi danyen jego,shiko Aliyu yayi nacin da bin,ko zai samu ya samu Ritsa Azeema ita kadai babu dama,ko gaishesu yazo yi da safe,su Inna Ramatu na wajen da Baba Ade,kuma Abunda ke bashu haushi suki tashi daga wajen,Abun na bakantamai rai Shiyasa kwana biyu yayi musu yaji,da Azeema taga haka sai dauki waya ta kirashi yana dauka ya balbaleta da masifan ta rabu dashi yaji da Abunda ke damunshi kawai ya yanke kiran,itakuma sai ta zuciya kan mene zai mata tsawa haka alhalin yana sane ba laifinta bane,kuma tayaya zata bashi kanta alhalin jiya jiya ne tayi tsarki,kuma ko samun damar zuwa Shashensa bata dashi saboda Baba Ade bata barinta Fita ko’ina suna tare da ita toh ya zatayi,toh dalilin yasa kowa ya Share kowa kenan harsu goggo suka dawo ana gaba,duk da sai su shafe kwana uku basu hadu da juna ba,don ko Su Afiya sai dai ya aiko jakadiya ta daukan mishi su,ko shashen Azeeman bai kallah saboda takara batamai rai saboda ta rainashi ko zuwa ma tabashi hakuri batayi ba,kuma ya sake kiran wayarta tanagani taki dauka,kwafa yayi aransa yana ayyana yadda zaiyi mganinta.

Su goggo basu Rufe sati da dawowa ba Aliyu yace shifa ya shirya zai koma bakin aiki,Abun yaba kowa mamaki,bama kamar goggo,wacce sukayi mgana yace sai Azeema tagama wankan yara sunyi kwari zasu koma tare da ita,da goggo ta tunamai sai ya bata rai yace ya chanza ra”ayi ne intagama wankan tazo daga baya ganin yadda ya mtsane yasa maimartaba ya amince aka neman masa Visa,Shida mallam lawal wanda maimartaba yayi yayi dashi yadawo masarauta su zauna tare yaki,yace abarshi a inda yake saboda yafi sabawa da chan,kuma ko ahaka babu Abunda zaice sai godiya ga Allah,ta sanadin Suwaiba da Azeema bazai kirga alheran daya samu ba,gashi ayau saboda ita zai je kasa mai tsarki lalle Allah ne Abun godiya.

Daga Aliyu sai Mallam lawal suka bi jirgi suka koma,domin goggo tace Inna Ramatu ta zauna,in za’a maida Azeema sai ataho tare da ita,Abun bakinciki Azeema batama san Tafiyar Aliyu ba sai washegarin daya tafi taji suna waya da goggo,lokacin tana bawa Anwar nono wlh dawani bakin ciki ya Turniketa batasan sadda ta ture anwar ba tatashi da gudu ta shige daki tana kuka ba,Baba Ade dake wajen tayi Saurin daukansa tana lallashinshi,tunda fizgoshi daga Nono tayi,Abun yama Azeema ciwo,itako mai tayima yaya captain da zafi haka har zaiyi iya komawa batare data sani ba,wato yanzu bata da wani amfani awajenshi Tunda tana jego,tagama wahalan cikin ya”yansa yanzu ta haifemai toh bata ita yake ba wata zuciya tace wama yasani ko saboda shegiyar Ni”imar nan yakoma,Tuna haka sai da tayi kwallah,bata son haka take kishin mijinta ba,sai Ranar haka ta wuni kuka bata kuma ci abinci ba, yara ko nata kuka ammh kota kansu batabi ba goggo ko ko kanzil batacemata ba domin ta fahimci Fushin na gadangantane dama Tunda taga Tafiya ba Shiri,kuma tun sadda suka dawo bata ganin yana shigowa shashen Azeeman tasan akwai wani Abun,sanin datayi daga Azeemar har gadanga yan buhu da rabi ne bamai gayamata Abunda yafaru Shiyasa takawo ido ta sanya musu kawai,chan ta matse musu shirtartu kawai,yara kuwa Ita ta daukesu ta tafi dasu zuwa Turakar maimartaba tana basu Ruwan zamzam da Dabinon makka,nan da nan ko sukayi Shuru da maimartaba ya tambayi Ina mamansu take tabe baki goggo tayi tana fadin”Yau Fushin d’ankane ya Shafesu ko kallonsu batayi ba Tun safe tana daki tana koken koken banza..”Mirmishinsu na manya Maimartaba yayi yana Fadin”Toh toh kice Abun na manya ne,toh Allah daidatasu,kinga ni yanzu kitashi ki maidama Baba Ade yaran nan,tunda nidai bama Fada ba,kuma bakya Fushi da mijinki,kiyi maza ki kaisu kidawo kiji wata mgana..”Dariya tayi mai tana wani kallonsa kasa kasa tana Fadin”Kai Yallabaina baka tsufa..”Farin gemunsa yashafa yana Fadin’,Kinji ki da wata mgana ina Tsufan yake Suwaiba,ai a soyayyarki ban mori komai ba yanzu ne ma nakecin lokacina,kedai yi maza ki dawo ki amsa kiran miji kada ki shiga Fushin mala’iku..”yafada harda kashe mata ido,sauri ta kwasa tana dariya tace “Yanzu kuwa Yallabaina’Tafice Shiko yana binta da kallon kauna.

 ______________________

 Aliyu yana komawa bariki tacika da murna da Farinciki hatta Dinner dare sai da aka hada aka ci aka sha,akayi Rawan Sojoji sunayi suna wakensu,dayake Jabir shida zafira suka daukosa daga filin jirgi,washe gari kuwa har nan barikin Chief Amry of Staff yazo,suka gana da Aliyu akuma nan take ya samu karin girma daga Captain zuwa *MAJOR ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU* Yayinda Jabir yatashi daga Captain zuwa *CONOLE JABIR*,dukkan sojojij da suka je wannan kwantar da tarzoman sun samu karin girma,Ranar barikin tarude da murna,kwana sukayi kide kide da wake wake,haka suka taru waje daya suna rawa da waka suna Fadin _Lalle mune soja,dama kunun salala gidan wuya aikin soja dama kunun salala…_Abun sai wanda yagani,Ranar hatta su kawo sunzo ciikin barikin sun tayashi murna,harda su Anty madina dasu Anty mardiya sai Zafira da jabir,wanda wani shagalin sai wani satin A abuja inda anan ne za”a sanyama kowa rank dinshi.

Haka ko akayi A babban headquater su dake Abuja aka sanyama kowa Rank dinshi,wanda kowani gidan talabejin da gidajen radiyoyi,suke yada wannan Abun dake Faruwa life,Cikin masu kallo harda Ni”ima wacce murna ta cikata sosai,nan take ta dauki waya taturama Gadanga sakon taya murna da Fatan alheri,sukuma su maimartaba Atashar CNN suka gani har lokacin da’ake sanyama Aliyu Rank dinshi na zama major,Murna ba”a mgana domin Shima maimartaba biki na musassam ya shirya,sai alokacin Azeema take jin lbrin Tun komawarsa aka karamai girman yanzu taron tabbatarwa ne,Abun yayi mata tsaye arai wato itace mara amfani ko,domin hatta Safaratu da haisam tagani,taga kowa da kowa,ammh ita saboda bata da wani amfani ko bazata jeba agayamata ma ai wani abune,shiyasa bata karisa kallo ba tabar wajen tana dauke hawayen daya zubomata,Anan wajen aka sanar da anyi Transfer din Major Aliyu daga 1 Division Nageria Amry kaduna zuwa Barikinsu na Abuja mai suna *ABACHA BARRAK*…Sai dai kuma yan kaduna sunyi rashi gashi an saba,ammh babu yarda zasuyi Tunda cigabane kamar ma jabir yaji lbri,kuma anan wajen aka karramma Sojojin cameron,da chadi da Niger,bayan Maigirma shugaban kasa ya jaddada godiyarsu garesu,tare da Fatan Alheri,daga karshe gwannatin kasar Nageria tasanar dasu cewa bazata taba mantawa hallarcinsu gareta ba, Allah yabar zumunci,nan da sati daya duka sojojin ,zasu koma kasashensu cike da samun nasara,suma shawagabanninsu sun yaba da kokarin na gwannatin Nageria tare da jajircewa na sojojinta agaskiya tsarin ya burgesu,sun kuma yaba da wannan tsarin gwannatin Nageria nabama mutane tsaro da kare rayuwankan da dukoyoyinsu,sun kuma yi alqawari bada kowacce gudummuwa in bukatar hakan tataso,jawabin daya sanyaya zuciyar yan kasa,sukaji suma yau suna alfahari da kasar su Ta Nageria nan take aka saka Taken Nageria inda kowa ya mike ya kame,yana bin Taken Nagerian daduka muryansu,dayawan sojojin saboda daraja kasa,yadda sukabama Tutar nageria martaba,sunayi suna kwallah????,Don Allah masu karatu duk wanda yazo daidai wajen nan akaratunsa yatsaya yayi godiya ga Allah(SWA) daya zamo damu daya daga cikin yan kasa Nageria,in zai samu ku gudanar da taken Nageria,nidai nayi nawa kuma na Fada da karfin *AM PROUNDLY TO BE A NAGERIAN*????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button