ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

   _________________

   *INDIA*

_NEW DELHI_

   “”Tun Suna Nageria dama Kawu already yagama mgana da Asibitin ta yanar gizo,sun san da zuwansu,suna sauka sai ga Motar babban Asibitin na *FORTIS HOSPITAL NEW DELHI* Sunzo tare da Manyan likitocinsu sun daukesu,zuwa Asibitin inda nan take babban Likitan kashi wanda Duniya ke Ji dashi *DR KABIR KHAN* Wanda ya kasance musulmi ne gaba da baya,kuma Ba indiye ne ta uwa ta uba,yasa aka Shiga dashi Thearter Room,Tunkafin zuwansu dama Tuni kawu yagama Turamusu dukkan Bayanai game da ciwon nan Aliyu,kuma hatta da kudaden aiki sai da ya Tura musu ta bankinsu dake yanar gizo,Tunda suka shiga dashi basu Fito ba har Tsawon awa biyu shine dalilin Daya su Umar suka bar Asbitin sukaje suka kama musu masauki wanda ke kusa da Asibitin wani kayatattacen hotel suka kama musu, mai Suna _JW MARRIOTT HOTEL NEW DELHI_ Suka kuma kira su kawu awaya suka sanar dasu,sanin ba yanzu za”a Fito da Aliyu ba yasanya dukkansu suka nufi masaukin kowa yayi wanka suka ci abinci kafin sukara dumguma sukoma cikin asibitin,kuma Abun Sha”awa,harda motoar da zata dinga zirga zirga dasu mallakin Asibitin ne,komai nasu cikin tsari.

 Suna komawa ba Dadewa sai ga Aliyu an gunguroshi kamar gawa zuwa dakin Hutu,indiyan likitocin kuwa sai bama junasu hannu suke suna ma juna barka da alamun dai aikin da sukayi ansamu Nasara ganin haka yasa,su maimartaba sakin ajiyar zuciya suna mai Hamdala acikin zukatansu.

*Janafty*

*ALIYU GADANGA..!*

 _(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

   _I dash to whole page 4r My one and only *YAYA*???? D person of *IBRAHIM* Yaya I.B..Tanque so very much Yaya for ur luv,support and care,Allah ubangiji yabaka Mata tagari wacce zata kula dakai kamar yadda kake kula da *KANWARKA* Ameen_????????

       *Chapter..37*

  “”Dr Kabirkhan Shiya nemi ganawar Sirri da maimartaba dasu Kawu,inda yake sanar dasu cewa aiki yayi kyau masha Allahu,ya sanar dasu lalle gadanga ya Auna arziki domin da”ace an kara daukan wani lokaci da kafarsa inda wacce ke dauke da harbin bindiga sai dai ayanketa,kuma taimako ma na biyu shine sanda harsashin ya Shiga Tunkan yagama huda nama jikinsa,akayi Saurin Fidda dashi shima yabada Taimako sosai wajen Rashin lalacewar kafarsa tasa, kana daga karshe Dr kabirkhan yayaba da Jarumta tare da Dauriya irinta ta Da”nsu Aliyu gadanga,domin ya iya tsawon kwanakin daya dauka da wannan Rauninka ajikinsa tabbas ko acikin Sojojin shi na dabam ne,ammh yanzu haka yana dakin hutu kuma babu wanda zai Shiga inda yake sai nan da kwana biyu lokacin ya Farfado,kuma duka aikin nasa baza”a warwareshi ba,sai nan da wata biyu,lokacin suna saka Ran Insha Allahu komai yazama Tarihi Aliyu zai taka da kafarsa ya Fito daga cikin Asibitin nan yakoma kasarsa da kafarsa

  Hakika su Maimartaba Sunji dadin bayanan Dr kabirkhan wanda yayi musu Shi cikin harshen Turanci,godiya sukayita yimishi,shima yana gode musu,kafin su Fito daga office din nasa maikama da aljannah Duniya,Koda suka Fito Abunda ya karanta musu,shi suka karanta ma su goggo dake waje hamdala kowa ya Shigayi Tare da Fatan Allah yasa anyi aikin cikin Nasara,basu koma masauki ba sai chan dare bayan sun leka Aliyu ta cikin glass,din inda gadon dayake kwance yake,gabada kafafunsa suna sagale ne jikin wani karfe,mai aiki da wasu Na”ura,haka hannunsa,shima an sagala shi,jikin wani Abu mai kama da roba,dai dai inda hannun yake anyi wani Filo,yadda hannun yayi bisa,kodaga chan suna hango Fuskarsa yadda tayi Haske,ammh yayi Rama sosai,dukkansu sunji dadin ganinshi domin yafi yadda suka taho dashi,addu”an samun lafiya sukayimai kafin su rankaya zuwa masaukinsu.

 

Kamar yadda Dr kabirkhan Yafada kwanan Aliyu biyu ya Farfado,kuma Alhamdulillah jikinsa yayi kyau sosai,domin koda likitoci suka gama bincikensu akanshi,suka Fito bayan sun bama su kawu damar Shiga wajensa,ammh banda doguwar mgana,koda suka Shiga sun Tarar da wata Nurse ta tadashi zaune ya jingina bayansa da wani Filo mai kyau da taushi,Yana ganinsu yafara mirmishi alamar Sauki ya samu,Tea mai zafi Nurse din ta hadamai ta mikamai,ya karba da hannunsa mai lafiya,Umar ne ya karisa da hanzari zai karbi Kofin Nurse din ta dakatar dashi kafin tace abarsa yasha da hannunsa saboda inyana motsa wannan hannun nasa,shi zai taimaka wajen Motsa wanchan hannun mai Ciwo,kai ya gyadamata alaman gamsuwa kafin ta Fice ta barsu,nan fa suka zagayesa suna hamdala,goggo ko Kallonsa take hawaye suna taruwa a idonta,girgizamata kai ya hauyi kafin yace”karki kuka goggo,kin manta kece ke man kirari da gadanga kusar yaki,ba gaba da gaba ba ko ta bayan ma karya sukeyi? yafada cikin sanyin murya dariya goggo tayi lokaci daya da mirmishi,Kofin tea din ya mika Umar yana Riko hannun goggo yace,”Toh kuma Shine kike kuka,kinsan baza su iya ba,baza su iya ja da gadanga ba,gadangan goggonsa. ba.”Yafada yana Sharemata kwallah,dariya ta kubcema kowa ganin goggo na kuka tana dariya hannunsa ta kamkame tana Fadin!”Tabbas bazasu iya ba,Nasani baza su iya jada gadanga na ba,Allah ya baka lafiya”Da Ameen ya amsa kafin yace”Kawu wai muna wani gari ne,sai naga kamar nan ba Nageria bane,duba ga likitocin da suka zo suka dubani yanzu..?

 Maimartaba ne yayi mirmishi yace!”Alhamdulillah Tunda yanzu kadawo hayyacinka,yanzu haka muna babbar birnin india,New Delhi,acikin wani Asibitin kashi..”Gyada kai yayi yana mamakin duk yaushe sukazo nan,kawu ne ya karbe da cewa”kuma kwananmu biyu yau da zuwa,kuma sai yau ka Farfado bayan aikin da”akayi maka Tun bayan zuwanmu..”gyada kai yayi yana bin Su Jabir da Haisam da kallo,wadanda sukayi wani kalan Tsausayi,dariya ta kamashi ya daga hannu yana Fadin”hey ya’n kannena,ban mutu bafa naga kunyi wani kalan Tsausayi ne..”,Hararansa Haisam yayi kafin yace!Suwaye kanneka…? kai tsaye yace”Kumana..”Jabir ya yi Saurin Dunkule hannu zai sakamar bisa ciwo,da hanzari Aliyu yace”Kai Dude Don Allah bari wlh kuna gaba dani..”Yafada yana Zaro ido,sauke hannunsa Jabir yayi yana dariya gabadaya su goggo dariyan suke,na ganin diramar su Aliyu,mai hali dai baya chanza halinsa.

 Suna Shirin tafiya masauki ne,Aliyu yakira goggo wacce ke Shirin Ficewa dawowa tayi tana Fadin”gani gadanga ko kana bukatar wani Abune? girgiza kai yayi yana Fadin”A’a goggo..”Kallonsa tayi kafin tace'”Toh mene ne? lumshe ido yayi kafin yace”,Ammr,nace ba goggo banga Azeema bace ko ba”a zo da ita bane…”?Yar dariya goggo tayi kafin tace”Allah sarki ai nasan zaka tambaya,wlh Azeema na gida,bamu Taho da ita ba,kai batamasan Abunda ke Faruwa dakai ba gaskiya don ni na hana a sanar da ita,tunda aka nemeka aka Rasa,Azeema ta shiga kunci,gashi kuma cikinta ya Tsufa,kaga kuma sanar da ita kamar kara mata damuwa ne..”Dan Ware ido Gadanga yayi kafin yace”Cikin yayi kato ne goggo..? kansa ta dungure kan tace “Ban sani ba in tazo sai ka ganninma idonka…”Washe baki yayi yana Fadin”Da gaske pretty zata zo wajena..”Gyada masa kai tayi kafin tace”Haka nake so,da zarar mun koma zasu zo ita da Gimbiya Razeenah da Baba Ade,Allah barshi sai ta zauna anan har ta haihu,lokacin kuma nasan kai Alhamdulillah kasamu lafiya sai ku tattaro ku dawo gida,ko baiyi ba..”da hanzari Aliyu yace”Hakan ma yayi goggo Allah ya kara girma..”kansa ta Shafa kafin tace”Sai da Safe Allah ya kara Sauki…”Tafada tana fita daga dakin,dayake Asibitin basu da bukatar wani mai jinya,sai dai in daga nesa kukazo,ku kama masauki kuna zuwa kuna ganin majinyacin har ya samu lafiya,ammh ba’a yarda da kwanan Asibiti ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button