ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Lalle masu iya mgana sukace Abun namu ne,toh haka tafaru da Aliyu da Azeema,don mantawa sukayi da kowa da komai suna rike da juna,suna hira gefe daya suna shan soyewarsu,har dare dakyar su Ummah mai babban daki suka tara Azeema suka koma masauki,ammh da Farko kuka tafara wai ita ba inda zata wajen Aliyu zata kwana,baki Ummah ta rike tana Fadin”Wai naji yaran zamani,toh in kin kwana,ina zaki kwanta gado dayane dai adakin,kuma yana kwance ko’ina tallabe? ko kallonta batayi ba ta fice tana Tura baki,Aliyu ko baitabajin haushin Rashin kwanan masu jinya ba sai yau,saboda Tafiyar Azeema ranar ko barcin kirki baiyi ba saboda kewa da damuwa,Tun safe ya ke ta kiran Jabir awaya don Allah ya kawo masa prettynsa Jabir sai yayi tsaki ya yanke kiran yana Fadin”wannan gayen Tunda yafara samuwa sai Allah kuma..”daga karshema kashe wayar yayi don yace yana barci bamai tashinsa,itako Azeema tun sallar Asuba bata koma tayi wanka ko karyawa batayi tatafi dakin su Umar tahau kwankwansa musu,Umar ne tafito,tana Neman yin kuka tana rokonsa yazo yarakata cikin Asibitin,ganin zatamai kuka ne yasa ya koma daki ya Shiryo yazo yatafi da ita ko Shiga baiyi ba ya juyo ya dawo yana Fatan Shima Allah yabashi mata wacce zata soshi ta kula dashi kamar Matar Yaya Aliyu.

 Gadanga na zaune Yana Tunanin Azeema,ko Shigowanta baijiba,sai kawai yajita ajikinsa ta fadomai tana Fashemai da kuka,rumgumeta yayi ta lallashinta itako Fadi take wlh bazata kara Tafiya anan zata dinga kwana,cikin kunar rai yace”Kwarai da gaske kinanan wlh keda mijinki sai ahanaki kwana dashi,watafi chanchanta tayi jinyata inbake ba,bari likitocin suzo ko susan Abunyi ko kuma su sallameni mukoma gida gabadaya”Yake Fada Ransa bace.

Haka ko akayi Dr kabirkhan na zuwa Aliyu yayi cikiciki da rai ba Annuri,kuma yaki sakin Azeema yana kamkame da ita,Dariya Da sha”awa Abun yabaiwa Dr kabir khan da Sauran likitocin,Yasaketama Adubashi yaki sai Fadi yake,Asan yadda za”ayi dashi ko ayima prettynsa waje ta rinka kwana dashi tana bashi kulawa,ko kuma Shima sallameshi su tafi gida tare,itako Azeema harda dagowa tana Sharbe kwallah,shiko yana lallashinta,Tafi indiyan likitocin suka saka saka musu suna dariya Dr kabirkhan yace cikin Harshen Turanci” Umh very nice LOVE BIRDS…”Yake Fada yana musu Dariya,nan da nan yayi waya daga cikin Asibitin ya bada umarnin kawo wani karamin gado,kafin kace me har an Shigo dashi an kafashi kusa dana Aliyu anyimai Shimfidun alfarma,hardasu blanket da Filo mai kyau kallonsu Dr Khan yayi kafin yace”Is ok ko,mrs Patient ankashe rigimar zamu iya dubashi yanzu?yafada yana dariya tashi tayi tana gyada kai,cikin yar kunya,kuma wai tana wani Share kwallah,suko suna musu dariya kusan fa indiyawa akwai Bama soyayyah muhimmanci,gefe Azeema ta koma har suka gama Duba Aliyu suka fice suNa musu dariya suna tsokanansu da love birds.

Koda su Jabir suka iso,suka iske sabon lbrin baki suka rike,Jabir da bai iya Shuru yace”Wai yau naga bariki umar,yanzu Kaduba gayen nan,duk Wahalan damukayi dashi baitaba nuna damuwarsa ba inzamu koma masauki,ammh yau Azeema tazo harda tada rigiman kota dinga kwana dashi ko asallameshi yadawo gida? hararansa Aliyu yayi yana Fadin”,Eh din,to daman ku gardawa dakune zan so ku kwana dani,Allah kyauta kai ni ko yanzu kuka tattara kuka tafi,Ayashe ta gaida Assha ko pretty? yafada yana kallon Azeema,wacce ke kunshe dariya ganin yadda Jabir ke hararansa,Jabir ya yi kuri yana kallonsa kafin yace”Toh ai ba damuwa ba basai ka koremu ba,zamu tafi kuma wlh zaka nemi ni banza mara mutumci kawai..”Dakin ne akasa dariya gabadaya ganin yadda Jabir yaji zafin Abun,Waje yafita yana ta zagin Aliyu shiko hardamai gwallo,Zafirace ta lallaba ta bi bayan Habibitan,Su ummah ko Aliyu sukayita ma Tsiya shiko ko ajikinsa don Abun yanzu ne yayi mai daidai.

 Azeema duk da tsohon cikinta bata nuna kiyuwa wajen kula da Megidanta Aliyu,itace bashi abinci,goggemai jiki sabida yaji dadin jikinsa saboda Rashin wanka,akwana hudun da zuwansu garin aka kwance Karayan hannunsa,kuma Alhamdulillah komai yayi kyau masha Allah,sai da kokarin yafara anfani da hannu,wanda wannan aikin Azeema ce,itace keta kokari kan haka kuma yana kokarin motsa hannu,koda daukan Abune na mara karfi,itama Asibitin suna kokarin kula da ita amtsayinta na mai ciki,tunda duk sun saba da likiticin kamar DR khan sun Shaku dashi,inkaga yadda suke hira da Aliyu sai kuce sun shekara aruaru da haduwa ne.

 Sati Daya su Gimbiya Razeenah sukayi suka koma,harda Jabir da Umar,Ummah mai babban daki tace ko ba inda zata zata,har sai Azeema ta haihu Aliyu ya warke kana ta biyosu su dawo,saboda itama ta kula dasu,toh ya suka iya dole suka barta sai Gimbiya Razeenah Tabisu suka koma tare,Ita kuma Ummah Dr khan yace ba”a barta ita kadai ahotel ba,gidansa dake cikin Asibitin nan Yakai Ummah mai babban daki,tazauna ita da matarsa mai Suna KAREENA,suna da kirki sosai,duk da Ummah batajin Turanci tana jin labarci,sukuma sun iya saboda sun zauna da larabawa sosai saboda yanayin aikin Shi Dr khan din,itama kuma Azeema aka barta ita da mijinta tana kara kula dashi..

   _________________

  *BAYAN WATA DAYA*

 Sauki tare da cigaba yana samuwa abangaren Aliyu,wanda har an kwance duka aikin da”akayimai akafafunsa,hannunsa kuma Tuni ya yawarke garas,in ka ganshi bazakace yataba samun Rauni ba,Kafafunsa kuwa haryafara koyon Tafiya dasu Duk da tafiyan bata nuna Sosai ba,ammh sakamakon sanduna guda biyu,suna taimakamai Sosai wajen Nunar da Tafiyar nashi,kullum safe da yammah Azeema ke Fitowa dashi suna zagaya Haraban Asibitin,suna tafe suna soyewarsu babu Ruwansu da kowa,Tuni sukebama duk wanda ke asibitin sha’awa ganinsu bakaken Fata,ammh kuma suna mutumta soyayyah da daraja Aure haka,Ba yadda Ummah mai babban daki batayi ba,akan Azeema tadawo tahuta Tunda cikinta ya isa haihuwa ammh fafur taki,wai Tunda lafiyanta kalau ita bazata ta zauna ba,dole ta zura mat ido toh yazatayi Allah ya hadata da yaran zamani.

Awani dare Azeema tatashi da Nakuda,Hankali Aliyu yayi bala”in Tashi ganin halin datake ciki,ko kafin ya danna Madannin kiran likita Azeema tafara Wani irin nishi,ko kafin Nurses din su kariso Azeema tayi wani nishi mai karfi sai ga Kan d’a ya Fito,Allah ya taimake Nurses din suna shigowa Kan Da’n na Fitowa da hanzari suka karisa suka saka hannu suka jawosa,ai basu bar wajen ba,Azeema ta bankare tana salati nishi take mai karfi sai ga wani kan yakara Fito,suka saka hannu suka jawosa,Aliyu dake gefe yahada zufa kota ko’ina yana rike da Azeema,wlh har sai da yayi mata kwallah,ai suna jawoshi,takoma takwanta tana maida numfashi,Ihu suke suna daga ya”yan suna bugasu,nan da nan suka chanyara kuka atare,Azeema dake kwance hannunta kamkame dana gadanga taji cikinta yakara murdawa Nishi take saki tana Fadin”Yaya inaji fa akwai wani acikin cikin?Tafada tana wani nishin mai karfi,Wata nurses ce ta ankare da hanzari ta kariso tana kara ware kafafun Azeema take Fadin”Anoder one…”Take Fadi tana ihu”push oya push…”take Fadamata Azeema ko jitayi kamar zata Shide saboda azaba,dakyar ta iya wani nishi mai karfi,wanda ya Fito da kan Da’n Suka sanya hannu suka jawoshi,suna murna gabadaya dakin ya gauraye da kukan jariran wadanda Nurses din suka dagasu suka zube bisa jikin Azeema suna dariya,jikinsu duk jini ammh haka Azeema ta rikesu tana dariya lokaci daya da kwallah,Aliyu ko kamar yasuma saboda dadi,Dakyar suka koreshi waje suka kwashe mabiyan Azeema suka gyara wajen gefe daya kuma wasu suna kokarin gyaran yaran,duk da asibitin na kashi ne,ammh Nurses din sun san Abunda sukeyi,shiyasa karban haihuwan Azeeman bai basu wahala ba,duk da Abun yazo da Sauki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button