ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Sai Ranar Daura aure kana Sarki Aliyu Abdulnaseer Tambari buzu,dashi da tsohon sarki Abdulnaseer tambari buzu,sai ga kanin kwamishina daya hana auren Ni”ima Da farko kunyama tanahashi bada auren akaro na biyu,sai wani ne ya basu Auren,yau ga mahaifin Aliyun dayace sai yazo,toh gashi gabanshi wanda ko daga ido ma yakasayi ya kalleshi bayan Daura Auren kwana daya kawai sukayi Aliyu ya tarraro matarsa suka dawo masarauta,inda ya hadata da Azeema yajata mata kunne,kuma koma baijamata Ni”ima Ta riga data sani Azeema ta mata Zarra,ko goggo Fadan datayi mata kenan Ta girmama Azeema,kowama haka yake Fadi,aiko dole ta girmama Azeema ko taki ko taso,itako Muneera bata zo bikin ba,suna Niemiy, cikinta ya Tsufa yarima Umar ne kadai yazo,shima kwana biyu yayi yakoma Wajen aikinsa.

Ni”ima Ta yarda Azeema ce ke gaba da ita binta take sauda kafa,domin Aliyu ya sanar da ita da Amincewarta ya aurota,so dole ta godemata,ita kuma Azeema ta kama girmanta domin itace Shugaban matan Sarki kuma Sarauniya kwara daya tal mai mulkan zuciyan Aliyu,kowace Ranar datake da kwana zata bi miji Turaka,ammh ita Azeema Aliyu da kanshi yake binta,ita ta hanashi saboda tabashi hadin kai ya kwantanta Adalci.

   Ayanzu haka Ni”ima nada diya daya mace mai Suna Umaimah,suna kiranta Ummah,sai Azeema wacce takara bayan Sajida tayi Jabir,sai Bala na karshe wanda suke kira Kawu,Muneera ma ya”yanta biyu Aliyu da Abdulnaseer,sai Jabir dake da uku Haisam kuma biyu haryanzu Safaratu bata kara haihuwa ba,zaman lafiya tare da zumunci yana kara karfi atsakaninsu Inna Ramatu kuwa da Mallam lawal Tuni maimartaba yaci galaba akan Baban Azeema sun dawo masarauta da zama,yau sai ga Inna Ramatu na tsoma biyar tana wanke goma,harta da bayi tana dashi bayan katon Shashen dasuke zaune wanda yaji kayan alfarma.

Su Afiya kuwa sun girma don Suna da shekaru Shidda kenan Aduniya yara ne kanana ammh masu Tunanin manya mgana chakwai babu wanda basayi sun ruga sun saba da Baba lami da Maminsu Ni”ima Shiyasa Azeema in ba wani Abu sukeso ba,basa ma nemanta suna Sheshen Tsohon sarki Abdulnaseeer ko Shashen inna Ramatu ko wajen Ni”ima.,ayanzu haka Azeeema nda katon phamarcy acikin Masarautan wanda Aliyu yasa aka kirkireshi saboda ita da kuma karatunta aka Cikashi da mgunguna,duk Abunda ake bukata konawani mgani zuwa kawai za”ayi A nunamata da kanta zata je ta dauko mganin saboda tariga ta karantu akai.

Shekara Daya da da komawarsu Niger,Siyasa ta kusanto,kawu ya Fito takarar gwannan jahar kaduna cikin ikon Allah kuwa yasamu nasaran Hayewa kujeran gwannan jahar kaduna,ayanzu haka suna gidan gwannnati Abunsu,suna cikin Shekara na biyu kenan akan karagan mulkin.

  ********************

   Sarauniya Azeema ta zauna a kayatattacen Falonta wanda yaji kayan alfarma zaune take Akan wani Tuntu,jikinta sanye da wata alkayabba mai Ruwan zaiba,kallo daya zakamata ka Fahimci tsabar hutu da Mulki tare da jin dadi sun lullube Azeema,tare da wani girma kamar ba yar Shekara 28 aduniya ba,gefenta yar Amananta ne Baba lami,wacce haryanzu suna tare basu rabu Azeema na nan A uwar dakinta 

Tuffa takeci Baba lami na gefenta suna mgana kan Wani lokacin achan baya Baba lami na bata lbrin ada ita batasan Tuffa ba,don ita ta aza wani Abu ne dabam,dan dariya Azeema keyi cike da Nishadi,sai ga Anwar ya Shigo da gudu bayanshi Afra ne basu dire ko”ina ba sai jikin Azeema Baba lami ke fadin “A’a megida meye yafaru kuma? wayar hannunsa ya mikama Azeema yana Fadin”Ummi wayarki wlh Tun dazu afra ta dauka tana miki game aciki,kuma Abbu sai kira yake”Karbe wayar Azeema tayi tana kallon Afra dake hararan Anwar,shiko yana mata gwalo,kunnenta ta kamo ta matse tana Fadin”Kin Rainani ko,bakijin mgana ta ko? har yaushe zance kada ki kara daukan min waya ammh bakiji ko,wlh koda wasa kika kara sai nasa sarkin dorina ya zanemin ke,wuce kibani waje..”Tafada tana sakinta,kuka ta fashe dashi ta Fada jikin Baba lami,itako tariketa tana lallashinta tana Fadin”Ke share hawayenki,so kike Maimartaba yace ya fasa auren,kefa matar sarki ce maza share hawayen”Tana Fadar haka ko ta Share hawayenta ta mike tinkis tinkis ta Fice sai Shashen su goggo tana zuwa Ta fada jikin Tsohon sarki Abdulnaseer,tana kuka rikota yayi yana fadin”waye mai tsautsayin daya tabamin ke? matse kwallah tayi tana Fadin ba”Ba Ummi bace ta min Fada ba..”,Baki Maimartaba ya rike yana Fadin”a.hhhh babban mgana lalle dole Ummi zata Fuskanci Hukunci kinji share hawayenki kinji amaryata”goggo dake gefe ita da Gimbiya Fasilatu suka tabe baki suna Fadin”Wannan amaryan taka ta Cika shagwaba”cewar goggo,Mele baki Afra tayi kafin tace”Sarkina ka koresu su fita”Dariya maimartaba yayi kafin yace”Angama ranki shi dade..,kutashi ku fita tunda kunji Abunda Amarsu tace”,Tashi sukayi dukkansu suna Fadin”Ko bakace ba gaka gata zaka nememu ne”Mirmishi yayi yana Fadin”injiwa Ga Amaryata ni ba wanda zan nema”Yafada yana dariya itako Afra ji’iran Yarinya harda musu gwalo.

achan bangaren Afra na Ficewa wayar Azeema ta sake daukan Tsuwa jin Riging tone din mai kiran kadai sai da ta murmusa,mikewa tayi tsam ta koma cikin bedroom dinta tabar Baba lami suna chasheta ita da Anwar dama dan Rigimar tane,sai ta fada bisa gado kana ta daga kiran Tana Fadin”Allah taimaki maimartaba mai mulkan mutanen agadez…”Mirmishi yasaki mai kayatarwa kafin yace”Kin Fadi jarawabawa pretty,cewa zakiyi maimartaba mai mulkan zuciyar Azeema Shikadai,da’ace kin Fadi haka Tun Farko da kinsamu wata kyauta..”Dariya tayi mai kayatarwa tana Fadin”ko ayanzu ban makara ba bari na gyara maimartabana wanda ke mulki tare da iko azuciyar Azeema ita kadai..”Dariyan Farinciki yayi kafin yace”Maki goma pretty…”Bata Fuska tayi kafin tace”kawai maki goma Yaya captain”saurin katseta yayi da cewa”ba kawai bane preety maki goman dana baki,sunfi maki darin da wani zaici awajen jarabawan Fita daga jami”a,yanzu dai duk ba wannan ba,nayi kewarki kwana biyu ne,wlh ko zaman Fada nakasa yi,shiyasa nace atafi hutun rabin lokaci,shine na samu daman kiranki..”Baki ta rike tana Fadin”a”a Mijina,kafasan sai gobe ne zaka dawo wajena,yau Ni”ima ce keda Turaka,don Allah ka zauna,karfa ka manta akwai hakkin jama”a dadama akanka,bani so ka zama mara adalci agaresu don Allah…”Shuru kawai yayi yana jinta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace”Shikenan pretty zanyi Abunda kikace,Ammh wlh bazan boyemiki ba, nidai an cuceni an hadani da aiki ga Sarauta ga karin kwanaki kafin na kasance dake mtseww..”Kawai taji ya yanke kiran,ajiyar zuciya ta sauke tana Tunanin yaushene yaya captain zai rike Sarautar da Allah ya bashi,kullum cikin cewa yake shi an cuceshi anhadashi da aiki,daman ma tana iya bakin kokarinta da batason mai zai yi ba,tashi tayi tsam ta Wuce shashen Ni”ima don batajin dadi tun jiya tana ta fama da amai da zazzabi likita tazo ta gwada ta ta tabbatar da ciki ne da ita 

Koda Azeema ta isa shashen Ni”ima chan ta sameta kwance su Jabir nata duduma kanta,shida Sajida,Ummah kuma na gefe tana wasa,Afiya babbar banza ta zaune kan kujera tana ta lissafin banza,domin itace sak mahaifinta kwata kwata bata da yawan Mgana,ko zasu kashe kansu bazata tataba tankasu ba,tsawa Azeema ta bugamata tana Fadin”zan makeki yanzunan,wawiya kawai kina ganin bata da lafiya bazaki iya hanasu damunta ba,ammh kina zaune kamar wata sokuwa..”Narke Fuska Afiya tayi kafin tace”To ni Ummi ya zanyi dasu..”Harara Azeema ta sakarma kafin tace”Maza kwashesu sukai su Shashen momy yanzu”Dakai ta amsa kafin ta mike taja hannun Ummah da Sajida jabir kuma ya bisu abaya,don sunsan hali Azeemar bata musu da wasa saboda taga kaf masarautan babu mai Kwabamusu yara,suna ta Abunda suka ga dama,karisawa tayi ga Ni”ima wacce ke kwance ta zauna agefenta tana Fadin”ya jikin naki Uwar biyu..”Yar dariya Ni”ima tayi kafin tace”Wata uwar biyu nima Ummi wlh bani son cikin duka duka Shekaran Ummah daya fa”Yar dariya Azeema tayi kafin tace”lalle nema Mami,toh Tun Wuri ki maida wannan mganar ki hadiyeta karki bari Maimartana yaji,don ranki sai ya baci,kin manta na sanar dake su Afiya nada Shekara daya na samu cikin Sajida,ki godema Allah bata da Wani rigima kina yayeta ki mikomin ita nan,in zasu tafi nageria hutun karshen Shekara su tafi ma da Ummah da takwaranta don tana nemanta..”Jinjina kai Ni”ima tayi kafin tace” To Shikenan Allah ya kaimu yakuma saukeni lafiya”Da Ameen Azeema ta karba kafin tafara kalle kalle tana Fadin”Mami nifa wlh ina jin kamshin maimartabana,anya baya na nan shashen kuwa.?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button