ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

 Koda gari ya waye sai dai Asibiti ta cika da lbrin Majinyacin Sojan nan da”aka kawo daga Nageri,matarshi tahaifi Tripple,Mata biyu Namiji daya,kuma dukkansu sun zauna amahaifa dayane domin ko Azeema da Aliyu haryanzu sun kasa gane bambamcinsu,duk da kwana sukayi suna kare musu kallo,sun Rumgume yafi sau Biyar suna kara godiya ga Allah daya Basu wannan kyautar,Ummah mai babban daki sai dai Da Safe Dr khan ya sanar da ita haihuwan Azeema,duk da shima baya Asibitin waya akayi masa,jiki narawa suka nufa cikin Asibitin,sai dai suka tarar da Azeema zaune bisa gado tayi Ras da ita kamar ba ita ta haihu ba ga Gadanga a gefe bakin nan kamar zai yage,saboda murna Ummah mai babban daki ita takira Gida ta sanar dasu,gabadaya masarauta ta rude da murna Jikoki uku alokaci daya lalle Allah Abun godiya,Goggo ita ta kira kawu da kanta ta sanar dashi kafin kaceme haihuwan Tripple yazaga Duniya,Haisam na kano yaji lbrin ai sai ya kira jabir yana sanar dashi da zarar komai yayi daidai Aliyu ya dawo gida zasu fadama maimartaba suna so suma ayi bikinsu nan da wani lokaci domin zamowar Aliyu baban yan uku tabbas barazanane ga rayuwarsu????

 kwana biyu da haihuwan Azeema gimbiya Fasilatu da gimbiya Razeenah suka dira a india,murna ba”a mgana,ai gimbiya Fasilatu batayi shawara da kowa ba tayi saranda Taba goggo dama,Domin ta Fahimci tafi karfinta nesa ba kusa,domin tsakaninsu kamar tsakanin sama da kasa ne,duka duka Sati daya suka kara gabadaya aka Rubutama Aliyu gadanga sallama lokacin yana da wata biyu a asibitin,domin yaji sauki sosai koma nace ya warke,domin kafafunsa sun mike da kanshi yake takawa batare da Taimakon sanda ba.

 Asibitin sunsha kewa love birds,Azeema da Aliyu ga kuma Tripple masu shiga rai da Ban sha”awa,haka sukayi ta hotuna da likitocin da Nurses,suna bankwana da sabo suka rabu,Azeema harda kwallaar rabuwa ita da Ummah mai babban daki sunji dadin india,sosai Dr khan kuwa sunyi exchanging din Phone number da Aliyu,da cewa da zarar ya shigo Nageria zai nemesa,haka suka rabu da matarsa kareena wacce suka shaku da Azeema da Ummah.

 Ranar da suka baro india zuwa Masarautar Tambari buzu,sukowa ana chan ana gudanar da shagulgular murnan dawowar Aliyu da kuma murnan haihuwan yan”uku ,wanda ba”a tabayi ba tun sadda aka gina masarautar,Mutanen Nageria kuwa Sun dade da isa zuwansu Aliyu kawai suke jira,Hatta da jabir wanda yazo Shida Maminsa da Daddynsa,da Haisam ba”a barsu abaya ba domin sunce wlh wannan karon bazasu koma Nageria ba sai da matansu sun gaji suma,suna bukatar gwada karfin mazantakansu???? wannan karon ma kawu da duka iyalansa,harda su Anty madina sunce wlh suma baza”a barsu abaya ba,tab uwa uba kuma ga shi Sunan yan ukun za”a hadashi ne da bikin gwagwaran biyu Wato Jabir da Haisam,kawu ya roki alfarman kuma Maimartaba baiyi gaddama ba,sakamakon yadda yake cikin Farinciki na dawowar Aliyu,ga kuma wani kyautan daga Allah.

*Ina godiya sosai masoyana ina ganin duka comments dinku daga mabambamta group dadama,bana samun binku daya bayan daya na yi muku reply,saboda ina cikin busy ne ko Typing din ma kokari nake mu kareta mu huta hakanan Shiyasa,ngd sosai kujigaba da hakuri dani Allah ya bar zumunci Ameen*

  

_*Sisinah Aisha Alto,keda Sahibata Hafsat Hafan ina kai gaisuwa???? Alherin Allah ya lullubeku aduk inda kuke*_

*D’IYATA LADINGO GA SAKON JINJINATA????Allah yayi ma Rayuwarki Albarka can love u less diyar kwarai*

*Janafty*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 38*

   “Koda suka isa Masarautan, ta dinke babu masaka tsinke,haka aka yayyabe Aliyu da Azeema kamar za”a cinyesu saboda murna da Farinciki,Triple ko sunsha dauka sai da Gimbiya Razeenah ta daukesu ita da Azeema kwacokam zuwa shashenta,inda ta sanya Jakadiya ta saka wata baiwa ta saka mata katuwar gawar da Ruwan zafi ta shiga da Azeema tiolet ta gasata dakyau sosai ita kuma Baba Ade ta wanke yaran tas,aka Shiryasu cikin kayan sanyi masu kyau,aka kaima maimartaba su,shida kawu suka daukesu suka sanya musu albarka,shiko Aliyu bayan gaishe gaishe shashensa ya wuce,shida amininnasa,yasamu yayi wanka yaci abinci ya kwanta domin Hutu,suko Su Zafira da Safaru,suna dawowa goggo ta damkama Anty madina su tace amanar gyarasu na hannunta nan da nan ko tashige dasu Shashen goggo chan kurya domin cika Umarnin goggo,Ummah ko ita dasu gimbiya Fasilatu suna Shashen Azeema suna zaune suna hira cike da Farinciki da Annushuwa,Azeema kuwa tana gama cin abinci suka kulleta cikin daki wai ta kwanta ta huta,tana kwanciya kuma sai barci.

Tako’ina masarauta ta dinke da jama”a daga mabambanta wajeje a kasar Niger,dama kewayanta harda mutanen wasu yanki,domin samun damar amsa gayyatan Da maigirma Sarkin Agadez yayima jama”a na Murna haihuwar jokokinsa har guda uku,tare da Daura Aure tilon ya”yan nasa guda biyu,dole Abun ya Wuce hasashenmu,domin fa ashirya taro ne na azo agani,Hatta da Mallam lawal da Inna Ramatu sai da maimartaba yasaka akayi visa suka taho,domin yace har abada inna Ramatu tana mtsayin mahaifiya ne ga Azeema,sai ga Inna Ramatu zaune cikin masaraurar Tambari buzu rike da ya’yan Azeema,lalle duniya Abun tsoroce kuma hausawa na Fadin Abunda yabaka Dariya watarana Shizai sanya ka kuka,Sai kuma alokacin Aliyu ke jin lbrin Rasuwar Azeeza yaji ba dadi,ammh baiwani nuna damuwarsa ba,kawai yayi jim ne,saboda kada Azeema tace yana murna da Rasuwar yar”uwanta,ammh harga Allah ya manta da wata hallita Azeeza,Fatan dacewa wajen Allah yayimata,ammh akasan Ransa Yana fadin an rage mugun iri.

  Daga Nageria Aliyu ya samu waya dadama,ciki harda waya daga Babban headquater su na Abuja,sukayimai ya jiki,bayan nan ya samu waya daga abokan aikinsa dadama,cikin wayar data tsayamai arai itace wayar da Ni”ima tayimai tana kuka,tace tayita nemansa so ba adadi bata sameshi ba sai yanzu,tadamu sosai Allah yasa ya warke babu Abunda ke damunsa,Mirmishi kawai yayi mata kafin ya sanar da ita ya warke yanzu hakama yana Masarauta nan yake sanar da ita haihuwan Azeema,da kuma Aurensu Jabir,Ni”ima taji hawaye sun taho mata tayi Saurin dannewa tana fadin!”Allah ya raya su bisa sunnah Congratulation,”Lokacin datake Fadin haka yana jinta kuka takeyi,sai ya basar yana tambayanta yakamata su Fito da miji ita da muneera Suyi Aure saboda Shine mutumcinsu,Dariyan kuka Ni”ima tayi kafin tace”Muneera zatayi Aure in Allah ya bata miji na gari,mgana na kuma bata don bazan taba yarda na auri wani namiji ba sai mutum daya,in ban sameshi ba,sai da nakoma ga Allah banyi Aure ba..”Saurin katse kiran tayi tana Fashewa da kuka,Aliyu Tunda sukayi waya da Ni’ima ya koma wani Sukuku ranar,saboda kalaman Ni”ima,hakika in yace bayason Ni”ima yayi karya,kuma in yace baya tsausayinta tabbas yasan karya yakeyi,kawai Shi ra”ayin Aurenta ne bayayi,saboda Shi mutum ne,mai zuciya da tsayawa kan Ra”ayinsa tunda yarasa Ni’ima da Farko komai na plan din Aurenta ya Rushe,sai gashi Azeema dabaitaba tsara Rayuwa da ita tazo tazama kaddaransa,gashi yau an wayi gari bayan goggo bai da wata sanyin idaniya daya Wuce Azeema yanamata Sonda baisan iyakarsa ba,saboda kirkinta da sadaukarwanta gareshi,hakadai yayita tunane Tunane har ya kareta baisamu mafita ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button