ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Ranar Da Azeema ta cika Sati biyu da haihuwa da misalin karfe 10:00am na safiyar Ranar jumma”a Duban mutane da sarakai,suka Shaida auren Haisam da Safaratu sai Jabir da Zafira kan sadaki mafi daraja, afarfajiyar Fadar maimartaba Sarkin Agadez Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,Daurin Auren daya amsa sunansa,wanda ba”a tabayi ba masarauta tacika makil da yan gida da yan waje,busan algaita kadai kakeji da kade kade da raye raye na Masarauta,abinci ko tako”ina kawai afitowa dashi ake,daga cikin masarauta kuma Yau din ne ake Sunan Triples,wadanda suka ci Sunaye masu daraja Daya taci Sunan goggo SUWAIBA ,Dayan kuma FATIMA,Sai Namijin yaci Sunan Maimartaba wato ABDULNASEER,Wanda ada sunan kawu akaso yace,kawun da kanshi yace maimartaba yafishi chanchantan samun takwara da farko,shima inda rai da rabo,mai sunanshi na zuwa,sunsha wanka cikin kayan alfarma,suda Mahaifiyarsu Azeema,wacce ke sanye cikin wani leshi,mai tsada da yarari,kunnuwanta da hannuwanta gabadaya Sanye da zinarai suna daukan ido,Hakama ango karni sanye da shadda fara riga da wondo harda babban Riga Shida aminan nasa,guda biyu duka shiga iri daya sukayi harda cikon Umar na Hudunsu,Ana gama Daura auren suka nufa shashen Aliyu suka gudanar da wata yar kwakwaryan walima,bayan la”asar nayi aka Fito akayi wata kayatattacan kilasa,mai ban Sha”awa Da dadin kallo,haka duka zaratan maza su hudu ke bama doki wuta sunajan limzami,kowa da kowa yafito kallo,harda maimartaba,Amare ma suna gefe,kowacce ita tarike ma mijinta limzaminsa kafin afara kilasan,Hakama Azeema tayima Aliyu gadangan kusar yaki,daga karshe maimartaba da tawagansa suka Rufe kilasa,yau hatta da kawu Bala Da mallam lawal da sun hau dokuna,Atawagan Sarki,itako inna Ramatu Tunda sukazo take Shashen Azeema ta karbi su Ummah ita ke kula da ita da Triple,Tayi nadama sosai in kuka ganta kamar ba ita ba,Abun jin dadinta ma babu wanda ya riketa da Abunda ta aikata kowa amasarautar yana bata girma amatsayinta na Uwa ga Azeema,Gadanga ne dai haryanzu bai saki da ita sosai ba,don shi mutum ne mai Ra”ayin bala’in in baya Ra”ayinka Tun Farko Abu ne mai Wahala yayi Ra”ayinka daga baya,kawai mazayewa yake saboda Uwar mata Azeema,don ya lura Tunda ta haihu takoma masifaffa,mgana kadan sai ta hau Fushi,shiko yanzu Aduniya in akwai Abunda ya tsana to yaga Fushi Afukar pretty yanzu nan zai Rasa natsuwarsa,shiyasa in gaya su Jabir na Rawan kafa kan su Zafira mamaki suke bashi,dariya kawai yake Aransa yana Fadin”Yarinta haryanzu na damun su Jabir,Allah ya kaunda Fitina,tunda daga su Jabir din har Su zafira shegen Rawan kan tsiya????

  Wajen kwana biyu aka Dauka ana gudanar da shagulgula Amasauratar Tambari buzu,saboda jiran Visan su jabir ta Fito,Ranar kwana uku da Daura Aure visan ta Fito sai haraman komawa,Haisam gidanshi na kano zai wuce da Safaratu,itako Zafira cikin Cikin barrak zasu zauna ita da jabir,sai fa alokacin ne koke koke ya tashi suna kuka sun rike gimbiya Razeenah akan su sun Fasa aure,Abun ma dariya yabama Azeema,sai da taje ta kira Aliyu yazo,tsawa daya ya daga musu kowacce ta Shiga natsuwarta.

Goggo ce da Gimbiya Razeenah zasu raka Amare,Ummah mai babban daki tace wazai zauna tab,wlh dole ne aje da ita gwara tayi amfani da lafiyanta kafin karfinta ya kare tazaga duniya????Sai su Ummah dasu Anty madina da zasu koma,Inna Ramatu dai tana nan sai Azeema tagama wanka sukoma Tare hakama Shima Aliyu ko Shirin Tafiya baiyi ba,su suka raka Amare da angawaye har Filin jirgi,inda suka sha tsiya wajen gadanga yanata musu iskanci yana Fadin”yaga Sai rawan kafa suke,toh ko sau dari zasuyi Arana bazasu taba kamoshi ba,kuma wlh duk wanda yayagamai kanwa da yawa Allah ya isa????????Jabir ya bashi amsa da cewa”Wlh tallhi yage yagema mallam,kai don Ubanka daka yaga kanwar wani wayamaka mgana,kajimin dan iskan Yaya”Dariya Umar ke tayi Shiko Aliyu hade rai yayi yana Fadin'”Yau ga surikin zamani,yanzu ni kake cema Dan”iska ko,ke Zafira zo nan”Yakira zafira wacce ke tare da goggo,ganin haka yasa Umar ya taresa yana Fadin”Allah huci zuciyar magajinmu rabu dasu,ai kowa ya sani ba wani babban Sai Baban yan ukun mu..”jin haka yasa ya washe baki yana Fadin”Allah yaso ku da na kirata nace ko kazo ta matse kafa????????”..Dukkansu baki suka rike suna kallon Aliyu shiko gwalo yayi musu yana dariya,daga Haisam har jabir binsa sukayi da gudu kowa ya dungule hannu na cin ubanshi yaje ya makale bayan kawu Bala yana Fadin”,Kawu ga gansu ko,daga ina musu nasihan hakuri da Kawaici ,saboda dai wanda ya riga ka kwana dole ya rigaka tashi ko mami? yafada yana kallon Mamin Jabir tana Dariya ta amswa da cewa”,Hakane Aliyu,babu kuma wanda yakamata yagayamuku gaskiya bayan Shi,yarigaku auren nan,sannan kuma yaya yake agareku Tunda kuna auren kannensa”Suna jin haka sai kawai suka juya suna hararansa,gwalo yake musu yana yar dariya,shi wlh dariya suke bashi in ya kallesu kowani shege ajirace yake da mace????Azeema ce tazo ta murdemai kunne ta baya yayi yar kara yana kallonta kafin yace”Pretty mugunta ko? zaki cirema Baban Triplet kunne ko? matse mai gefen ciki tayi tana Fadin”Kabarsu Jabir hakanan don Allah,tunda kai lokacinka babu wanda Yasa maka ido..”Hannuwansa yahada yana Fadin”toh angama Ranki shidade maman yan”uku”Dariya kawai tayimai ta wuce shiko yabita da kallon sha”awa azahirin batu anfara kureshi fa haba,hanya fa ba kyau,tsakani ga Allah yakamata pretty tazo taji dashi Tunkan yafita daga hayyacinsa.

 Basu dawo gida ba,sai da sukaga tashin jirginsu,kana suka koma gida cike da kewa,Shashen Azeema ya rage daga Baba Ade sai Gimbiya Razeenah sai Inna Ramatu,hakama Shima Aliyu yaji shuru saboda harda Umar aka tafi zasu koma Asallamesu kafin su biyo jirgin sojojinsu su dawo kasarsu.

  **************

 Koda suka sauka A Nageria,direct Su goggo kano suka wuce da Safaratu,Awata anguwa mai Suna Tarauni,gidane babban kirarre,sai wanda yagani komai na alatun Rayuwa akwaoshi acikin gidan,babu Abunda zasu nema su rashashi,nan suka kwana sai washegari suka bar kano zuwa kaduna dukkansu,ammh shi kawu tun jiya yakoma kaduna abunshi,da zasu taho sai da goggo ta damkama haisam cheque dinsa na milayan uku,wanda maimartaba yabashi kyauta,tare da albishir din kujeran makka,shida Safaratu,Ummah harda guda da rawa,tana ta godiya balle su madina da sukayi ma Haisam chaa,wai yakowo su ijiyemai kudin,banza dasu yayi,shifa duk ya kosa su watse don wlh arike yake fa????Karfe 2, da wani abu na Rana suka bar kofar gidan Haisam,suka bar shi daga shi Sai Safaratu sai halinsu sai dai Fatan Allah ya basu zaman lafiya.

Hudu da wani Abu na yammah suka Shiga kaduna direct to barikin Su jabir suka yada zango,shima din dai apartment din na jabir kamar na Aliyu komai ya mallaka,gyare gyare kawai sukayimata da Sauran abubuwa,basu kwana ba,tunda kaduna gidane,dama tuni iyayan jabir suka bi kawu bala,tun jiya suka dawo kaduna abunsu,shima irin kyautar da maimartaba yama Haisam irinta akama Jabir,tare da kujeran makka Shida zafira,Murna kam ba’a mgana basu wani jima sukayimata Abunda yakamata suka barta daga ita sai Halinta kowanne yakoma gidansa,gimbiya Fasilatu da Goggo da ummah mai babban Daki gidan Kawu bala suka sauke gajiyansu sai sungama hutawa ko zasuyi Shirin komawa Niger,saboda atsakanin nan sun yawatu aduniya ba laifi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button