ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

mikewa Ni”ima tayi tana Fadin”kema kinsani yanzu haka shashenki yaje bakinan,shine ya biyo sawu,dama ana Cika awa biyu baizo ya ganki ba,ai maimartaba sai yallabiyansa..”Tafada tana yar dariya ita ta ganshi Tun sanda ya Shigo falon,hannu yasaka mata abaki alaman tayi Shuru ya make bayan labule.

yar Dariya Azeema tayi kafin tamike tana Fadin”Au kema kin biyema su goggo ne,To shikenan ni kingama tafiya ta Tunda Abun hakane..”ko taku batayi ba yayi caraf ya dagata sama yana juyi da ita,ihu taso ta saka ya damke mata baki yana dariya kwabe Fuska tayi ta Maki rawaninsa sauko da ita yayi ya rike hannunta yana Fadin”Ke baki da kunya Sarki guda kike duka ko”Hannu ta daga takara makemai kewa tana Fadin”Bakajin mgana ko bance karka fito ba,sai angama zaman fada ba? Tafada tana murde kunnensa dake cikin Rawani,rike hannunta yayi yana Fadin”Wayyo Allah yi hakauri mama Azeema..”Yafada harda matso ido,gabadaya dariya Ni”ima da Azeema suka saka harda tafawa,hararansu yayi kafin ya hade rai yana kallon Ni”ima yace”Dukkanku kallon ku nake,kwana biyun bawacce ke kula dani,ke ya nuna Ni”ima Tunda kikayi ciki shikenan kifara lalaci baki da aiki sai barci da kwanciya,ke kuma ya nuna Azeema,baki da aiki sai yima yara Fada da dukkansu,da anyi mgana sai kice kada abarsu su sangarce,ammh ga aikin mijinki bakya yin ko daya,Allah Zaku sani ne,Aure zan kara dama Sarkin Garin dosso yamin Tayin Diyarsa gimbiya Aisha..”

Azeema ce tayimai wani kallo tana Fadin”au Allah to sai me,Toh Allah kawo ta lafiya ko tazo mungama kwashe romon da sauran wani mazantakan ka sai dai Ta auri saura wlh ko Mami?”Kai Ni”ima ta gyada tana Fadin”Mema zatayi da Tsoho wanda duk baki yacika da goro..”Dukkansu suna mgana ne yana musu wani kallo,sai da suka gama kana ya rike baki yana Fadin”Kutumelisi,ke yanzu nine zaki kallah kice kungama kwashe romon ko? lalle yaron to ko Rabi baku kwasa ba kekuma kina wani narkewa kamar ta Allah ni kikecema bakina duk goro ko? Toh duk na gode da gulmata da kukayi Allah ya kamaku,daga yau duk wacce tazo min Turakata nida ita ce”Yafada yana juyawa har zai Fice ya waigo yana kallon Azeema yace”Ke….”suka dago atare,Nunata yayi yana Fadin”Wuce ki koma Shashenki ko nazo nayi kasa kasa dake..”Tura baki tayi zatayi mgana yafara takowa zuwa gareta saurin Fara tafiya tayi tana kunkuni Ni”ima dake zaune tayi yar dariya tana Fadin”Yauwa tarata kutafi,ni Allah ma yau na yafemiki zuwa turakar Ummi,ban iya Fitinar mijinki,ba daman na dan kwanta sai yace nacika lalaci,kiji dashi har cikina yayi kwari…”Saurin waigowa Azeema tayi tana Fadin”Wa..? No..No yarinya bafa zai sabu ba,ban karba ba kuma bazan karba,nima ai in inada cikin bamai daukemin hakanan nake hakuri so kema ki hakuri gaskiya…”Tafada tana hararan Aliyu dake mirmishi.

Hannuta ya warfo yana Fadin”Ke rabu da ita tama yarda tagama mungode Mamin yara,kamar kinsani dama ta rage kula dani..”Yafada yana Rumgemta kokarin kwace jikinta take,ammh ya riketa kam,itako Ni”ima ganin Abun nasu bana kare bane,sai kawai tatashi ta Shige kuryan dakinta tana kokarin maida hawayenta ta yarda takuma sani Aliyu ba kowa ya biyoba sai Azeema dama ita yazo nema,kullum kafin atashi Fada aganshi sau uku ashashen Azeema,ko agaban waye baya iya boye son da yakemata,sai dai ita Azeemar macece mai tsananin taka tsantsan,saboda Ni”ima in yayi mata wani Abun sai ta basar,ammh ko ajikinta Shiyasa tace tace taji dashi cuz tasan duk mganar dayake ita yake bukata ba ita ba,share hawayenta tayi kafin ta Furta”Alhamdulillah nagodema Allah da tarin Ni”imarsa..”

Haka Aliyu ya tasa Azeema har zuwa Shashenta,suna zuwa taja ta tsaya tana Fadin”,haba…Haba wai meyasa kake hakane don Allah…”bata Fuska yayi yana fadin”Kuma Shikenan saboda ita na hana kaina Abunda nakeso,look Azeema ni bani na roketa ba ita gata ya kamata ta barmiki kwananta har ta samu lafiya,to kuma laifi ne don nanuna murnata Afili naga ke matatace kuma kowa yasani kece Fitilar raina,kinga wlh in kika karamin mganar wanchan mata billahil Azim zan iya sakinta takoma garinsu kowama ya huta,haba kinfa dameni dama kin amince in auretane don ki dinga hanani jin dadi dake ehe…”?Yafada yana daka mata tsawa idanunsa sunyi jawur,ganin haka yasa ta zabura tafada jikinsa tana fadin”,Wayyo na Tuba,bazan kara ba Allah huci zuciyar Gwarzon Azeema..”Fushinsa ne ke sauka jin yadda take kara kamkamesa,Hannunsa yasa Rumgumeta yana Sauke ajiyar zuciya Wuyanta yake kissing yana Fitar da Numfashi kafin yace”Ya wuce,ammh ki kiyaye,ni banga laifi na anan ba kawai kawai..”Yake fada da alamun haryanzu Abun nacimai Tuwo akwarya.

Dagowa tayi tana Fadin”Toh naji ammh don Allah zan Rokeka alfarma daya..?hade gira yayi kafin yace”Fadi indai bazata hanani jin dadi ba..”ware ido tayi kafin tace”Bazata hanaka ba insha Allahu,dama zance ne don Allah kadaina Satar Fitowa daga fada kana zuwa Shashena,wlh kowa yana kallonka harta bayi da Fadawa suna lura da Abunda kake,kada hakan ya rage maka daraja don Allah kadaina zuwa,In kanason ganina kamin waya sai nazo Turakarka na sameka..”

Wani kallon tara saura kwata yake mata kafin yace”Karma kikara hadani da Allah malama,don wlh bazai samu ba kikama bakinki kawai malama..”Yafada yana sakinta juyawa yayi zai Fice kafin yace”Ki saka ashirya kayan Yaran nan,Gobe in Allah ya yarda Umar zai biyo shida matarsa zai Wuce dasu Nageria suje suyi hutun karshen Shekara gidan Kawu..”Da kai ta amsa kafin tace”Nima dazu mukayi waya da Zafira tace,suma suna nan zuwa hutun karshen Shekara,harda Haisam da Safaru,wacce in tazo bazata koma ba,sai ta haihu..”Dan tsayawa yayi kafin ya waigo yana Fadin”Happy Family kenan can’t wait naga Su Dudes an zama iyayan yara”Yafada yana yar dariya,Azeema dake tsaye taga yakara mata kyau batasan sanda ta ruga ta fadamai ba Tana Fadin”Har Abada bazan daina Fadan ni mai sa”a bace…”Dagata yayi sama yana juyi da ita yake Fadin”A”a Pretty bake bace mai SA’A nine mai sa”a dana sameki amtsayin matata kuma uwar ya”yana…”Yafada yana Sauko da ita saitin bakinta ya dora lebenshi yana sakin mata nishi,kamkameshi tayi tana wani lumshe ido,Aliyu ya riga yasan lagonta,bakin kawai ta budemai ya cafki harshenta,yafara kissing dinta in a romantic way,tsayuwa taneman fa gagaransu,ganin zata Fadi ne yasa ya Turata kadan Tafada kan kujera,cikin kwarewa ya bita ya dan Doramata nauyinsa kadan yana kallon Kwayan idonta kafin ya Furta cikin Wani yanayi..” _*PREETY KE TA MUSSAMMANCE…._*..”Yafada kafin ya maida bakinshi cikin nata,suna cigaba Da kissing din juna cikin alamun Fittan hayyaci,Ina ganin haka na Rufe littafina da Birona na juyo ina mirmishi na Fita daga masarautar gabadaya Araina inajin Dole na bar Rayuwar Azeema da Aliyunta hakanan,ina cikin jirgin da zai maidoni Nageria nayi mirmishi nima na Furta..” _MASU KARATU KUMA NA MUSSAMMANE_……’

*ALHAMDULILLAH NIMA MAI RUBUTUN TA MUSSAMMANCE…..*

  

*Tammat bihamdullah Duka duka Anan Na kawo karshen Littafin ALIYU GADANGA.. !Fata kuskuran dake ciki Allah zai dubi Rauni na ya yafemin,Ladan dana samu Allah ya rabamana tare dani da masu juriyan bin wannan littafin Tun daga Farko har karshensa Ameen*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button