ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Farar Shinkafa tadafamusu,saboda babu cefane,dama tazo da Soyayyar miyarta wacce taji kaji aciki,daga Niger wanda goggo da kanta ta soya mata shi,sukaci da ita,suna gama ci ta kwashe Abunda suka bata ta kai kichen ta wanke ta kife ta tsabtace wajen kamar ma batayi girki ba,tadawo Falo ta amshi Afra dake kuka tana Shiga bata Nono,Tagama bata kenan Ta karbi Anwar tana bashi ita kuma Afra baba lami ta sabata,tana dan jijjigata nonon ya kwantamata kada tadawo da ita,sai ga Gadanga yashigo da sallama,Azeema na jin sallamansa ta hade rai,tayi kini kini dashi,Baba lami ce ta zube tana jeramai Sannu da zuwa ya amsa yana mika hannu ya karbi Afra dake hannunta yazauna kusa da Afiya wacce ke kwance tana wutsil wutsil da kafafunta,kumatunta ya latsa yana Fadin”Afi Afi yanmata,kina wasa ne..? yafada yana daga Afra dake hannusa,Baba Lami kuwa Tunda ya amshi Afra ta shige dayan bedroom din da Azeema ta sauketa aciiki

Ta gefen ido yake kallon Azeema,ammh Abun mamaki ko kallo bai isheta ba,balle yasa ran zatacemai sannu da zuwa,itakuma abarayinta ta dojene Tayimai banza,saboda ita ganinta shiyakamata yafaramata sannu da zuwa saboda itace ta sha hanya kafin tazo inda yake,ammh saboda Wulakanci jira yake tamai mgana Shikuma ya tsinkata,aiko tace wlh ya bushe indai itace wlh.

  Ganin yadda tawani hade rai kuma ta dauke kaine yasa Shima ya tattarata ya watsar ya cigaba da wasa da ya”yanshi,ganin haka yasa Azeema ta mike tana gyara rigarta kusa dashi taje ta ijiyemai Anwar Tajuya ta Shige daki tana wani Taku,wanda har aran Aliyu yaji wannan Tafiyar,baki ya rike yana binta da kallo wai ma yaushe Azeema takoma hakane? Abun fa mamaki yake bashi,ya”yansa yayi Ta biyemawa yana wasa dasu yana kuma mgana kamar ya samu wasu manya,suko kamar sun sani suyita washe baki suna bangala dariya,yadda bai nemi abinci ba,shiyasa itama batayimai Tayi ba har sai bayan la”asar kana ya bar gidan,bayan ya kira Baba lami ya dankamata su Anwar yayi Ficewarsa.

Koda ya dawo bayan issha’i,ko takan Azeemar bai bi,yayansa kadai ya dauka yayi musu wasa kafin ya mikama Baba lami su,yayi Shigewarsa daya Bedroom din da kayansa ke ciki,itako Azeema tana jin adawowarsa taki Fitowa dama abincin dazu da Rana daya ragu sukayi Dinner dashi,saboda taga alamun bayan ita harta Girkinta ma baya Ra”ayi,shiko Abun ya dameshi na kyaluwan da Azeema tayi dashi,wlh bai zata ba,kuma tana sane itace bata da gaskiya kowa na ganin laifin kowa kenan.

Washegari Tun Safe Azeema tatashi ta tsaftace ko”ina kafin lokacin Tuni Baba Lami ta wankesu Anwar ta shiryasu cikin kayansu na alfarma,ita kuma Azeema harta Fada kichen tana kokarin nema musu breakfast,ganin duk babu cefanan Abinci yasa kawai ta dafa musu macaroni,Suka sake ci da miyar jiya,domin yadda takejin kanta bazata iya bude baki tace yayo mata cefane ba,toh Shi da baya cin abinta yaushe zai yomata cefane,????kaji mata kin bashi ne kikaga baici ba?

  Wanka tayi cikin Riga da wando na wani pakista,mai kalan pick,yayi mata kyau sosai,sai ta daure gashinta ta baya ta zuboshi ko dankwali bata sanya ba,tafito falo bayan takoma kichen ta sanyo musu macaronin ita da Baba lami ta kawo mata,ita kuma tazauna kan kujera tana tsakuran Abuncin kamar ansata dole,gefe daya kuma hankalinta na bisa talabijin tana kallon wani Shiri A Mbc2,Saiga Aliyu ya Fito sanye da bakar jallabiya alaman yanzu tatashi,gaisuwan Baba lami yake amsawa ammh idonsa na kan Abincin da suke ci,macaroni da miya dasafe kuma? ya tambayi kanshi kafin yakalli Azeema yace”ki Rubuta dukkan Abunda kuke bukata,in na Fiti nayo cefene”In kun tanka Azeema ta tanka,don saima tatashi ta Shige kichen tana wani takun dai dai kamar wata wahainiya,Girgiza kai kawai yayi yakoma daki,yayi wanka ya Shirya ya Fito,ko takanta baibi ba yafice,ammh bayan ya Shiga dakinta ya iske tana tiolet,kan Gadonta ya ijiyemata ledojin kayan da Ni”ima takowa yayi Ficewarsa,sai da Tafito taga kaya akan gado,zazzagewa tayi tana dubawa kafin tayi kwafa,ta maidasu cikin ledojinsu ta ijiyesu nan tashiga harkan gabanta,shiko bai dade da Fita ba sai gashi ya dawo dauke da cefane niki niki,duk Abunda take bukata sai da ya siyomata,Shida Baba lami suka dinga jindan kayan suna kaiwa kichen hakima Azeema na daki tana jinsu taki Fitowa,saima gyara kwanciya datayi Abunta.

Yana gama Shigo dakomai yayi Ficewarsa hatta Baba lami ta Fahimci tsakanin ma”auratan babu zaman lafiya Aranta tana Fatan Allah ya daidaitasu,tana jin Fitarsa tafito da hanzari Taja ledojin daya ijiyemata ta kaimishi daki ta dungurar kan gadonsa tayi Fitowarta kichen Ta fada tana dudduba Abunda ya siyo,nan da nan ta saka masu lalacewa cikin Fridge,sauran kuma ta sakasu cikin ma”adana,bata koma daki ba,ta kunna gas,don yau wlh Tuwon semo takejin ci,shi ta dora da miyar Kubewa danyan,don ta ganta acikin Cefane,don Ta lura ko agidan goggo Bata Rasa danyan Kubewa saboda Yaya captain.

Bata dauki wani lokaci ba,ta kammallah ta mulmule Tuwon aleda ta zubasu cikin wasu sabbin kololin nan kichen din ta bar komai bayan Baba lami ta taimakamata da wanke wanke Tunda su Anwar sun samu barci,ita tabar gyara kichen din,itakuma takoma daki ta Shiga wanka,ta Fito kenan Taji Mganarsa Afalo,yana ma Baba lami Fadan meyasa aka bar Afiya su kadai adaki,hakuri tayi ta bashi,tanaji yayi Fuu ya Shige dakinsa baki tatabe kawai tacigaba da Shafa manta,tagama kenan ta isa gaban Wardrope din ta na neman kayan dazata sanya ya Fado dakin Afusace dauke da lodejin dazu yana Shigowa ya nunota dasu yana Fadin

“Meye haka Pretty naga kin dawomin da kaya? aiko wani Abu ne kya jira nazo ki tambayeni nayi miki bayani..? yafada yana kafeta da ito,banza dashi tayi saima juya masa baya datayi tana Cigaba da Abunda takeyi,wani Abu yazoma Gadanga wuya ya jefar da kayan kan gado,da sauri ya isa gareta sai dai taji an wani Fizgota tatafi kamar zata Fadi,ya riketa da kyau har Suna gogan Numfashin juna,Kallonsa take ammh batayi mgana ba,ganin yadda yake wani Huci,shikadai yace”Ina miki mgana Saboda wulakanci kina min banza..?

Kokarin kwace hannunta take ammh takasa harara ta sakarmai tana Fadin”,Ina ce kunne keji ko,don Allah mallam ka cikani”Tafada idonta ya kwallah Tsuramata ido, yayi Fushinsa na Sauka kafin ya sausauta rikon dayayi mata yana Fadin”Ki kwashe kayannan, danaki danasu Afra ne, Ni”ima ta kawo tace na baki..”Yafada yana Sakinta yakama hanya zai Fita ta waigo tana Fadin”Au kace Tsohuwar budurwanka ta kawo,ai dole ta kawo Tunda bayan dawowarka ta maye gurbina,Kaga don tayima abokin Shasha……

  “AZEEMA…..””!!!!Aliyu ya katseta da karfi da kuma wata tsawa mai gigitarwa wanda sai da tayi baya jikinta na Rawa,taku yafarayi zuwa gabanta idanuwansa sun chanza launi,kafa daya yadora bisa gado yana kallon Azeema yace”Kinfi sanin Ni”ima ne?kokuwa na riga saninki kafin ita,in inason yin iskanci da ita ai ba sai kin Fada ba,datun Farko da mahaifinta yahani Aurenta dana samarma kaina mafita,yanzu Ni Azeema Saboda Ranin dakimam yakai haka harzaki bude baki kice ina Shanshanci ko? yafada idonsa yana wani juyawa Shuru tayi ta kasa mgana,dauke kafarsa yayi yana Sauke ajiyar zuciya kafin yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button