ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Washegari Maimartaba da Waziri sai Goggo da Gimbiya Fasilatu Suka nufo kasar Nageria cike da alhini tare da tararradin Halin da zasu iskeshi ciiki,gimbiya Razeenah anbarta ta zauna Da Azeema ita da Baba Ade da Ummah mai babban daki,wanda sukama Azeema karya Da cewa zasu wani bikin masarautar yanki dake gabas dasu ne,kwana biyu zasu suyi dawo,bata damu ba don yanzu Abubuwa dadama basa burge Azeema,ita burinta Allah ya bayyana mata mijinta tare da Fatan Allah ya sauketa lafiya.

Koda kawu Bala ya isa Abuja dakyar aka barsa yaga Aliyu bayan Anfito dashi daga Emegency,wlh sau daya ya kalleshi bai kara ba,saboda yadda yaji kwallah sun tahomai,yanzu Gadangan goggon ne ya dawo haka gabadaya kafafunsa sagale cikin wani karafa,duka kuma nannade da bandeji,bayan Kafadansa shima daure a wuyansa,shima nannade da bandeji domin Shima karaye ne awajen,sai goshinsa wanda shima Wani katon Rauni ne awajen,gabadaya dai Abun Tsausayi,har kuma zuwa lokacin bai Farka ba,tun bayan Farfadowan da yayi lokacin ana Gyaramai Dauri,Kawu waje ya Fita yana Share kwallah,bai dade da zuwa ba,sai ga Haisam,ai Shi yana Shiga ya kame atsaye hannuwansa dafe da kai yana salati su Umar ne suka rikosa ganin yana neman Faduwa fadi yake su Fadamai gaskiya anya Gadanga na raye kuwa,?Sun tabbatar mai dayana raye,kawai dai ya jiki ne.

Sauran Sojojin dasuka dawo hayyacinsu suke bada lbrin Abunda Yafaru Ashe lokacin da yan boko haram din suka kawo masu Farmaki,suka yi ta bata kashi,toh lokacin da aka samu Rabuwa Sojojin acikin daji,harda su Aliyu aciki wanda sakamakon haka suka harbeshi akafarsa ta dama,Faduwa yayi akasa,ammh sai yayi kokarin mikewa,ganin ya kasane yasa ya Fito da karamar wukar dake kugunsa ya yaga daidai inda Harsashin ya Shiga ya saka wuka ya tsaka ya cillo shi waje yana ihu yana komai,saboda azaba,haka ya saka wani kyalle ya Daure wajen,ya mike yana dingishi ya cigaba da gudu yana rike da bindigarsa,ganin bai da wani karfi ne yasa suka mamayesa suka kamasa,suka kuma saka Sauran Sojoji 8 dake tare dashi su Mika kansu ko kuma su kasheshi,toh wannan Shine dalilin dayasa suka Ajiye makamansu suka mika kansu,shine fa suka ijiyesu anan sunata musu Azaba,dama sunce lokaci kawai suke jira dukkansu zasu kashesu,lura da sukayi kamar Aliyu ne Shugabansu yasa suka ware shi dabam suna mai Azaba kala kala,shine fa har yasamu wadanan Karayan da kuma Sauran Rauninka,suna kokarin cinye wa!adinsu na kwana biyun da suka diban musu na zasu nunasu Afaifan Vidiyo,su bada sanarwa cewa ko gwannatin Nageria su sakarmusu mutanesu suma su sakin musu Sojojinsu,in kuma sunki yarda toh suma zasu kashesu Dukkansu,toh Ana cikin hakane Sojojin sukazo suka Farmusu kuma Allah yabasu Nasara.

   *****************

Maimartaba basu samu isowa ba sai Washegari,lokacin da suka Shigo cikin asibitin sun tarar da Kawu Bala da Haisam,sai Umar da Jabir,sai wasu Security dake tsaronsu,Yanayin yadda goggo taga kawu tun anan jikinta yayi sanyi kafafuwanta sukayi Nauyi,lura da Halin datake ciki ne,yasa maimarta riko hannunta ya matse alamar Karfin gwiwa kallonsa tayi wasu hawaye na gangaromata,likitocin sunyi complain Majinyacin baya bukatar hayaniya,saboda Baida de da Farkawa ba,ganin kimar Maimartane yasa aka barsu suka Shiga inda Aliyun yake,kai kodaga ganin yanayin dakin,gabadaya glass ne,zaka Fahimci saima Mutum yaji kamshin mutuwa ake kawosa irin wannan Dakin????,lokacin da suka Shiga Dakin goggo na rabe bayan maimartaba Gimbiya Fasilatu ce kan gaba sai Waziri sai kawu bala dasu Umar,su goggo suna bayansu,Waziri keta salati yana kiran Sunan Allah lokacin dayayi Tozali da Aliyu,itakanta gimbiya Fasilatu da damuwar Abun baiwani dameta ba,sai da tayi baya tana dafe kirji idonta ya kawo kwallah,wani imani yakara Shiganta lokaci daya,yanzu Aliyu ne yakoma haka? ganin haka yasa maimartaba karisawa bakin gadon na Aliyu yana kallonsa da duka idanuwansa waje,Goggo dake bayansa tayi Saurin Rufe bakinta wanda kuka kenan Kwacemata hannu maimartaba ya sanya ya cire gilashinsa mai karamasa karfin ganin,hawaye suka taru acikin idanunsa,har sai da suka kwaranyo bisa hannun Aliyu wanda yake da lafiya,jin sanyin hawayen maimartabane yasa ya motsa hannunsa,lokaci daya da bude kumburarrun idanunsa,dishi dishi yake gani,ammh duk da haka sai da ya gane goggo da maimartaba dake gabansa,bakinsa ne yafara motsi,shiyasa da hanzari goggo ta duke gaban gadon tana Riko hanunnsa take Fadin”gadanga….”Tafada tana kuka kallonta yake,shima hawaye suna zubomai ta gefen ido,dakyar ya Furta”Na”am goggota…”Yafada murya shake,goggo Runtse ido tayi tana Rumgume hannunsa take Fadin”Allah ya Tada kafadunka Gadanga,Allah yabaka lafiya..”Take Fada tana wani kuka,wanda duk wanda ke wajen sai ya tsausayamata,Umar da jabir dake gefe banda Share kwallah babu Abunda sukeyi,Haisam ko waje yakoma don yadda kuka yaci karfinsa,Maimartabane yayi Saurin Ficewa da hanzari,Waziri ya maramai baya Shida Kawu Bala.

Gimbiya Fasilatu da Tsausayin goggo ya cikata ta Durkusa tadafa kafadanta tana Fadin”Ki bar kukan Suwaiba,kuka bazaimana mgani ba,addu”a zamu tayimai Allah ya bashi lafiya..”Goggo na jin haka tamike da hanzari,itama gimbiya Fasilatu ta mike,saboda yadda goggo take jikintama babu karfi saboda kuka,shiyasa kawai Tafada jikin gimbiya Fasilatu takara Fashewa da kuka mai cin rai,itakuma ta riketa tana lallashinta,Aliyu na kwance yana jinsu shima kukan yake,yana so ya tambayi,goggo ina Azeema ta haihu ne?ko haryanzu da Saura ammh kuma bakinsa yayimai Nauyi bazai iya mgana ba

Ashe Fitar su maimartaba sukayi Office din likitan yaje,yace ya Rubuta musu takarda yanzu zasuyi Transfer din Aliyu zuwa wani babban Asibitin kashi dake kasar india New Delhi,nan fa sukace basu san dawannan mganar ba,saboda gwannatin Nageria karkashin Sojojin kasa,ita keda alhakin kula da Aliyu Ahalin yanzu,kuma yana karkashinta babu yarda za”ayi su basu shi su tafi dashi,batare da gwannatin Nageria tasaka hannu ba jin haka yasa nan da nan Akayi waya zuwa ga *BRIG.GEN.S.U KUKA SHEKA* Shiya sanar da maigirma Chief Amry of Staff *LT.GEN.Y.T BURATAI* Abunda ke Faruwa babu Bata lokaci sai ga tawagarsa zuwa Asibitin da Aliyu ke kwance,nan suka hade dasu maimartaba bayan gaisuwa dawani dogon Turanci dole dai gwannatin Nageria ta rarrataba hannu tabasu Yaronsu,ammh sunyi kokarin nuna duk wani taimako da”ake nema suna Shirye suke dasu badashi,domin haryanzu Captain Aliyun yana mtsayin Sojan Nageria,Fatan Alheri ne ya biyo baya tare Da Fatan Allah ya bashi lafiya.

Kawu Bala shiya ta kokari har suka samu Visa zuwa gobe da Safe,shiyasa basu daukeshi daga Asibitin ba,sai Awashegari,bayan sunje hotel sun kwana,karfe 9:30 Jirgin nasu zai tashi ababban Filin jirgin *Nnamadi Azikiwe International Airport Abuja* Motar Asibitin da taimakon wasu likitocin suka daukosa daga Asibitin zuwa Airport din,Abunda zai baka sha”awa dukka masu Fada aji agwannati suna wannan wajen,harda wasu Sojoji wanda suke ta Farate,tare Sarama Shi Aliyun lokacin da”aka Fito da gadon marasa lafiya daga cikin jirgin za”a Daukesa zuwa ciki,yana kwance kamar baya Numfashi sakamakon sunyimai Allurar barci ne wacce zata daukesa har na tsawon awa biyu,bai Farfado ba,har aka Shiga dashi cikin jirgin baisani ba,su Maimartaba Sukabi bayansa,shiga da goggo da gimbiya Fasilatu sai Waziri da kawu Bala,sai Umar da Jabir da Haisam suma ba”a barsu abaya cikin lokaci jirgin da zai yada zango a babban birnin india ya lula sararin samaniya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button