ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

******************

  Duka duka Sati biyu ne da zuwansu garin Suka tattara duka Ahalin suka yada zango abirnin madina,harda su Maimartaba da duka matansa guda uku,gaskiiya wannan Tafiya tafiyane mai cike da Nasara,domin sai da suka kwana goma Amadina suna Ziyara kafin su wuce garin makka,inda kowa ya zage Yana ta ibada babu kama hannun yaro,Azeema data ganta gaban ka”aba sai da tayi kuka,haka tayita rokon ma Mahaifiyarta gafara da kuma Azeeza,sai ta rokon ma mijinta fatan nasaran rayuwa dakuma Allah ya rayamata ya”yanta cikin Tafarkin Adinin islama.

Kwanansu goma Sha daya agarin makka,lokacin angama aikin hajji,su maimartaba da matansa da kawu Da ummah da mallam lawal da Baba Ade,da Inna Ramatu,a birnin makka suka bar su Gadanga suka koma gida,domin dukkansu ba gida zasu koma ba,daganan birnin london suka yada zango,sai da sukayi sati kafin su Wuce Canada,nan din sati sukayi kafin daganan su wuce india A birnin New Delhi,sai gasu har gidan Drkhabir khan,wanda Fadan irin murnan da Sukayi Shida matarshi bata baki ne,har cikin asibiti suka shiga zo kuga yadda ake ihun zuwansu love birds,sai hotuna ake dasu ana Daukan Su Afiya wadanda suka kara wayau suka girma,nan ma sai da suka Shafe sati suna yawata gari kafin suyi haraman komawa gida,ta Abuja suka sauka daganan aka Rabu kowa ya nufi inda yafi wayau sudai su gadanga sunzo gida ne,Haisam daganan suka wuce kano Shida Safaratu,sai su jabir dasu Anty madina suka wuce kaduna,Umar da Muneera kuma Tun a India suka rabu su jirgin Niger zasu Shiga sukuma suka Shigo na Nageria.

Bayan dawowansu ba Dadewa Aliyu yaje ya karboma Azeema takardun ta na gama mkranta a gombe yazo yayi mata Rigisteration a BASE UNIVERSTY inda zata karanci PHAMARCY,murna wajen Azeema ba”a mgana Ranar da zatafara zuwa daukan lecture saboda zumudi ko barci batayi ba,gari na wayewa sai ga sabon Suprise,sabuwar motar ta kirar Toyota 306 Aliyu ya dankamata yace Ayi karatu lafiya,Ai Azeema kamar zatayi hauka haka ta makale Aliyu tana kuka tanamai godiya,dama already ta iya mota bayan dawowarsu Abuja,sai ta dinga barin ma Baba lami su Afiya tana tafiya mkranta,inkuma sunada interval a mkrantan takan dawo gida Ta basu nono takoma.

Azeema shiganta mkranta takara wayewa sosai,kuma bata yarda tayi kawa da kowa ba,saboda kashedin Gadanga akanta,tsakaninta dakowa hy hy ne gashi Kwakwalwarta naja kaf Depertment dinsu asan da zamanta mai kokari ce,gata da kamun kai da tsare gida babu Ruwanta da naza,matan ma kwarjini take musu tsoron tanka mata suke,Wani lokacin batajin Tuki da kanta Shiyake kawota yakuma zo ya dauketa Domin preetty tazama shi,shikuma yazama ita,Abunda ke kara sawa yake kara sonta ko mai takeyi bata iya hadashi da Laluransa,shi na musamman ne,domin duk Abunda takeyi dayazo da bukatarsa zata ijiye taji dashi,shiyasa yake kokarin tallafamata tasamu tayi karatun nan saboda shine babban burin Azeema ayanzu.

_Today is a special Day To me_????????????????

*Janafty*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

    *KA’RSHE*…. _END_????????????✌

            *Chapter 40*

      

“”Azeema bata Rufe Shekara da Shiga mkranta ba,Ciki ya bulla ajikinta,lokacin sunyi jarabawar Karshen semister,sun tafi hutu suna Shirin zuwa aji biyu,Inda Allah ya taimaketa Su Afiya shekaransu daya lokacin da wata daya,tuni sun yi girma suna Tafiyansu ko”ina,in ka gansu bazakace Azeema ta haifesu ba,sakamakon basa kama da ita ko kadan,Sai da da Aliyu suke kama,kana ganinsu daga gashin kansu zaka zargi kodai sun hada jini da larabawa ko Buzaye cikin biyu za”ayi daya,balle yadda Su Afiya suka dauko bakin gashin babansu,suna kanana dasu,ammh in Azeema tamusu tsifa ta daure musu da band Abun sai masha Allahu kawai.

Da farko Azeema tayi bori game da cikin jikinta,ta dinga kawoma Aliyu uzirinta,ga yara basu bar shan nono ba ga Kuma karatunta ita yanzu ya zatayi,zama da ita yayi yayita lallashinta dayaga taki yarda sai ya dauketa sukaje wani privet hopital suka samu wata likita,yasanar da ita mtsalansu nan da nan ta Shiga yima Azeema Fadan,ya Allah zai bata kyauta kuma tayimai butulci,tasan Adadin mutanen da suka zauna a inda take,suna mata kuka Allah bai basu haihuwa ba,koko tasan Adadin mutanen dake zaryan awannan hospital din duk dan Allah ya basu haihuwa? Azeema ta girgiza kai Hawaye suna zubomata tacigaba da Fadin”Kuma Shine ke Allah yabaki Kike neman kiyi butulci toh ahir dinki domin sai Allah yabarki da dubaranki,ai yafi ki sanin kina da ya”ya kuma ya zabeki acikin dubu ya baki wannan kyautan,toh tun Wuri ki daga hannu sama ki godemai kada Allah yayi Fushi dake”

jin haka yasa Azeema ta daga hannu hawaye na zuba tana godiya ga Allah,nan likitan ta sausauta takaramata da shawarwarin yadda zata kula da kanta da ya”yanta,Tunda ma taji su Afiyan sukai shekara daya tace ta ciresu anono babu damuwa,Sai acigaba da basu abinci wanda zai cigaba da gina musu jikinsu,magungunar karin lafiya dana karin jini ta Rubuta musu sukayi mata sallama,sai da suka biya phamarcy suka siya magungunar kafin su Wuce gida,Ranar dai Azeema kuka ta Wuni yi,Aliyu na aikin lallashin Tunda aiki ya riga ya sameshi.

  Haka Azeema ta cigaba da kula da cikinta sukuma su Afiya Ta ciresu anono ta damkama Baba lami tana cigaba da kula dasu,itama kuma tana Renon Cikinta tana kuma cigaba da karatunta babu wani mtsala domin Aliyu na tsaye kanta ita da ya”yanta,Cikin ikon Allah sai ga Azeema ta haihu kusan lokaci daya da Zafira,Azeema ta haihu yau Zafira ta haihu washegari Kuma duka mata Ranar suna Yar wajen Azeema taci sunan Gimbiya Razeenah,,suna kiranta Sajida,sai yar wajen zafira taci sunan Mahaifiyar Jabir wato khadija suna kiranta Meenal,tsakaninsu da Safaratu kwana goma sha biyar ne ita ta sauka ta haifi danta Namiji wanda yaci sunan kawu Bala,suna kiransa da Sajjad.

  

*AFTER 5 YEARS*

“”Ashekaru biyar da suka gabata Abubuwa dadama sun Faru na Farinciki da akasinsa,na bakinciki Shine Rasuwar Ummah mai babban daki,tare da Rasuwar Baba Ade wadanda suka rigamu gidan gaskiya,Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansu Da Gafara Ameen.

Ababen Farinciki kuwa Shine Shekaru biyu dasuka gabata Maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yayi murabus daga kan karagan mulki ya nada da’nsa Aliyu Abdulnaseer Tambari,wanda yayi Retire,a aikin Soja,suka tararra shida da duka iyalansa suka dawo Niger da zama lokacin Azeema ta kammallah karatunta sai tazo nan tayi bautar kasarta,Nadin sarauta da sai da aka jadaga kafin Ayishi domin Aliyu Tuburewa yayi Shifa baya bukatar Sarauta yafi bukatar Aikinsa Fiye da komai,ga Umar nan Adorashi shi yabarmai har Abada,Sai da yaga maimartaba yanuna bacin Ransa sosai,kuma su Kawu bala da Mallam lawal suka tayimai Nasiha kafin ya yarda,itako Azeema daga sama taji Abun kamar almara wai Aliyunta zai zama sarki,bata nuna Rashin goyon bayanta ba,saima kara karfafamai gwiwa dataitayi,lokacin ma tana da wani cikin ajikinta,Shi duk damuwarshi daya yasan baza”a barshi yazauna da Azeema ita kadai ba,dayayimata wannan complain kallonsa tayi tana dariya tace”To sai me Ehe,ai wlh bana da wani haufi akan Sadaukina ko yanzu wata ta Shigo na tabbata ni Azeema nayi mata zarrah har Abada,saboda haka karka Damu kanka ga Ni”ima,babu wacce ta dace ka aura sai ita,domin itama masoyiyarkace ta gaskiya nekamar muneera taji lbrim wacce ke Fadin kyawawan Halayyan Azeema domin tana bata girmanta amtsayinta na Matar wan mijinta,ita ma Azeema tana tafiyarta da ita yadda Yakamata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button