ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

  “Koda ina Saurayi ban lalace ba Azeema,kuma saboda Rashin sanin darajan kai narasa lokacin da zan yi Shashanci sai lokacin da kika zama jini da hanta na,kikagama mamaye dukkan Numfashi,bayan kin zamo uwar ya”yana?…Yafada yana nuna kanshi,Kuri yayi mata da ido,ganin yadda yake kallonta ne yasa ta sadda kai tana jin Nadamar Abunda Tafada.

Juyawa yayi zai Fita Yana Fadin”Babu komai Rayuwace…”Yafada yana kokarim Ficewa Saurin Shan gabansa Azeema tayi jikinta duk yayi sanyi,sadda kai tayi kafin tace”Ni ban fada haka har zuciyata ba kawai na fadane Saboda Haushin Ratayen nin dakayi shine kawai Fa..”Tafada idonta na kawo Ruwa,hannunta ya riko kafin yace”cikin ni dake waya Fara rataye wani ehe? nina Fara jan fadan daga baya ban kiraki ba kika kidaga kirana ba? ko ban Nemiki ba? yafada yana kallon kwayan idonta.

Raurau tayi da ido kafin tace’Nima alokacin Haushi naji ka doramin laifin da kasani ba laifina bane..”Matse mata hannu yayi yana Fadin”toh naji ammh kome nayi miki pretty ai ni mijinki ne,yakamata dakika dawo ki girmamani amtsayina na mijinki ammh kiduba yadda kika watsar da Rayuwata why pretty?yafada kamar zai mata kuka,itama kukan ne ya kawomata kawai Sai tafada jikinsa tana Fadin”Nayi kuskure mijina don Allah ka yafemin..”

Rumgumeta Yayi kamkam yana Fadin”Shii..Is ok komai ya Wuce nima kiyafemin kinji..”Yafada yana Shinshinar wuyanta,kamkame juna sukayi kamar wani zai Rabasu Fadi yace”Do u know wht? i miss u So much pretty wlh ko barcin kirki banayi saboda Tunanin kina Fushi dani plz karki kara barina,Rayuwa babu ke tamkar rayuwace babu jinin jiki..”Hawaye suka zuboma Azeema tace”Me too i miss u more,kuma i promise u am not let u down insha Allahu..”Jin haka yasa yadago kanta yayi Saurin dora lebenshi bisa nata yana yimata wani salo,wanda Tuni da dage ta nadeneshi tana mikomai harshenta da hanzari ya kama,yana mata wani Sumbata mai gigita ya”ya mata,kafin kace me,sun Rikita junansu,dama Azeema daga ita sai Tawel,wanda Tuni Aliyu yayi Fatali dashi,cak ya dauketa sai bisa gadonta,anan aka warware komai,Aliyu Tunda ya Shiga birnin Azeema Shikenan ya Susuce Fadi yake”pretty don Allah ki zauna dani,wayyo..””‘!Dadi wlh kina Rabuwa dani zan mutu ne..!Sai da Ta rufemai baki sanin basu kadai bane agidan,Itako daman Baba lami tana Falo,tun sadda taji hayaniyarsu ta kwashe yara su Shige daki,aranta tana addu”ar Allah ya daidaita ma”auranta.

Sai da komai ya kamkama bayan Sunyi wanka sun sauya kaya kana Suka Fito falo cin abinci,sunyi Shar dasu gadanga ko bakinsa har kunne,Ranar ma bisa Dining akaci abincin,Shiyasa Baba lami na ganin haka tace ita adaki zataci nata,saboda taga yau ma”auratan babu dama fa,aiko gadanga yaci tuwon nan sosai yana ta zuba santi,suna kammallahwa ta kwashe komai takai kichen,tana dawowa Tashiga dakin Baba lami ta basu Anwar nono,suka sha kafin tayi mata sai da Safe ta Fice,dakinsu ta koma inda uban gayyar ke jiranta tana Shiga ko ya kamata ya kamkame yana wani lumshe ido,datayi mgana sai yace shifa wlh an wahalar dashi dayawa gwara abarshi ya famshe da kyau.

Shikenan zaman ma”auratan ya Daidaita basu kara samun wata mtsala ba,sai ma wani karin so da kaunar juna sukeyi,Ranar da Azeeema tacika sati dadawowa Ranar Gimbiya Razeenah takoma Niger,ammh sai da Ummah ta matsamata ta rakata gidan Jabir taga zafira,murna ba”a mgana kuwa duk da basu dade ba,ammh sunji dadin zuwanta,ai Safaratu dake kano najin lbri takira Ta tana kuka akan wlh itama bata yarda ba sai tazo mata yata iya dole ta Shirya Ummah tarakata taje ta wunin mata,suka rasa ina zasu sanya iyayan nasu saboda farinciki kowacce tayi kiba bulbul Daga gani suna samun kulawa daga mazajensu,bata samu damar komawa wajen su Azeema ba,sai dai sukayi sallama ta waya dasu,suna bata sakon gaisuwa zuwa ga yan gida.

*BAYAN WATA BIYU*

Bayan wata Biyu Da Dawowar Azeema,Tuni su Afiya sunyi wayau sunkara girma kamar ba yan wata hudu ba ita kanta Azeemar tayi kiba takara haske da kyau,to takowani bangare suna samun kulawa,ga kulawar miji kamar ya cinyeta danya bata gasu ga,sunje kaduna sau daya bayan dawowarta,kuma su Haisam da jabir,sun zo Rana daya kowanne da matarsa sun musu kwana daya suka koma,mganar Auren Umar kuwa yazo Nageria sau daya Kawu maimartaba ya wakilta akan mganar babu wata bata lokaci har ansaka Rana Wata biyu yanzu haka biki baifi sati biyu ba ya rage,suna so suyi Shiri gabadaya ne daga chan dukkansu zasu wuce kasa mai Tsarki ne su sauke farali.

Koda Azeema taji lbrin Auren Muneera da Umar bataji komai ba,illah tsausayama Ni’imar datayi domin ko qur’ani zata dafa,Mijinta bayi da Ra”ayin Aurenta yanzu,ammh bata sani ba ko zuwa gaba,domin tataba latsashi akan mganar Ni”ima yayimata Fada sosai yace babu Ruwanta bata fishi sanin Ni”imar ba,daganan takama kanta,bayan an saka Ranar su da Umar,har Abuja sukazo suka wunin mata ita da Ni”ima sai alokacin Azeema tafahimci wacece Ni”ima sam bata da mtsala ko muneera datakeda Rawan kai yanzu duk ta rageshi,Ni”ima Tunda tazo take wahala dasu Afiya da wannan yayi kuka ta sabeshi ta goya,ta dauki wannan Ta hau jijjigawa,ita dai Allah ya Doramata sonsu,Umar da kanshi ya maidasu har  gombe da Kayan kwalliyan da Azeema ta hada musu,da farkoma kin karba sukayi sai da tace ko Sun Raina ne?shiyasa suka karba,Shiko Aliyu Tun zuwansu bayan sun gaisa yayi Ficewarsa ko daxasu Tafi Azeema ta kirasa awaya sai cewa yayi Allah kiyaye hanya yanzu zasu Shiga meeting ne,Azeema bata jin Dadin Abunda yayi ba sam wlh duk kunya yakamata,daya dawo sai da tamai mgana banza da ita yayi bai Tankataba Aransa yana fadin”mata masu Duniya yanzu fa daya dawo sai tace yayi laifi kuma oh sudai bamai iya musu sai wanda Ya hallicesu.

Yan Nageria basu Tafi Agadez da wuri ba Sai da Aka Daura auren Umar da Muneera wanda Kawu ya karbomai Aure don maimartaba bai samu zuwa ba,su goggo suna chan suna Shirye Shiryen Zuwan Amarya suko su gadanga sai Awashegari suka dumgumo zuwa Masarauta dashi da jabir da zafira sai Haisam da Safaratu,sai Kawu bala da Ummah,sai Anty madina da Anty mardiya,kowanne da yayansa da mijinta,sai Kawu lawal da inna Ramatu,sai Azeema da ya’n ukunta sai Baba lami,wanda daga chan dukkansu zasu wuce kasa mai tsarki Sai ko Amarya Muneera da angonta Umar,sai Aminiyarta Ni”ima,sai kanwar babanta daya da kuma Yar”uwan mamanta dasu kadai akazo saboda nisa,don itama Amarya da angon dasu za”a Tafi chan Saudiyan.

  Koda suka isa Masarautar Tambari buzu ko”ina ya cika da mutane anata Shagulgulan zuwan amarya,kai tsaye Shashen goggo aka kai amarya sai Awashegari ne,aka Kaita Fada jakadiya ta sanyanmata alkayyaban Sarauniyar Tambari buzu ta biyu,maimartaba ya sanyamusu albarka kafin awuce da ita Shashen mahaifiyarsa,bayan anfito da ita daga shashen Gimbiya Razeenah,daganan Ita Gimbiya Fasilatu tabasu kyautan kudi harda zinare,suka rankaya zuwa Babban Shashen na Yarima Umar,wanda lokacin kadan zasu zauna da sun dawo daga kasa mai tsarki zasu tarrara su koma Niamey inda yake aiki.,Duka duka kwana biyu su Ni”ima sukayi suka koma Nageria cike da Abun arziki tare da karramawa irinta masarautar Tambari buzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button