ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

 Tsawon minti talatin kafin su samu Natsuwa Rumgumeta captain yayi yana saka mata albarka domin Duk sanda zai kusanci Azeema ji yake babu bambamci da daren Farko,abunka da mai Shigar ciki tare sukayi wanka kafin yayi wanka tsarki ya fito ya barta itama tayi,kayan jikinsa ya maida,sai lokacin kunya Abunda suka aikata ya Shigeshi yanzu taya zai iya Ratsa mutanen falon ya Fita haka dai ya kukan Kuran Fita,domin alokacin anata kira kiranyen sallar mangariba,Yana Fitowa yaci sa”a babu kowa afalo,sai su hibba suna wasa,Da hanzari ya sauko ya Fice,yana Fitowa yaci karo da su Haisam suma sun Fito zasu masallaci,suna ganinshi suka tsaya suna kallonsa yake yayi musu yana Fadin”Muje mana,ba sallah zaku ba..”Haisam ne yace ahankali”Kayi wanka kuwa..? zaro ido yayi kafin yace”,Wankan me? Jabir ne ya duke yana kallon Umar kafin yace”Wankan Janaba mana..”wani dogon tsaki Aliyu yaja yana fadin”Janaban Ubanka,kudai yan iskane idonku na kan Sunnah kuna saka ido,kuka sani ni banda lokacinku kunga tafiyata. “Yafada yanayin gaba,suko suna mai dariya,Umar dake gefe yana dariyan yadda yaya Captain din ya hade rai,wai shi dole tsare gida har sukaje masallaci bai kulasu ba wai shi adole bayasaon Raini,cikinsu maimartaba dasu Kawu ya Shige dasuka mai mgana yace”Gaskiya ya lura zaman dayake acikinsu ma zubar dakaine,a mtsayinshi na magidanci mai mata harda ciki,sukuma amatsayinsu na yara kaskancine,kawai su kama kansu shima yanzu zai chanza taku ne,gwara yafara zama cikin manya Shine mutumcinsa”baki Haisam ya rike yana fadin”Kut..Kai wai ban girmeka ba..?”Wani banzan kallo Gadanga ya jefamai kafin yace”Koda ka girmeni ai baka halliceni ba..”Yafada yana wucewa ya barsu suna zaginsa shida jabir,Aransa yace”,Na bar kara zama cikin yara daga yau..”yafada yana yar dariya????????

   Tun Adaren Aliyu ya samu kiran Ni”ima Tana mai murna,bayan itama harda mahaifiyarta tabamawa mami,wacce ketayashi murna itama amsa musu yayi kafin yayi musu godiya suka yanke kiran,Shuru yayi yana Nazarin wani Abu kafin ya saki ajiyar zuciya yana ayyana Abubuwa dadama.

Washegari suka wuce birnin zaria,A Fadar maimartaba suka yada zango,Maimartaba sarkin zazzau yaji dadin wannan ziyarar ta Sarkin Agadez maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yace dama yaji lbrin zuwansa bai zaci zai zo har Yankinsa ba,An gaisa cikin mutimci sosai kafin wasu jawaban su biyo baya,Maimartaba sarkin zazzau yayi mamaki wai sarki guda ya zauna agarin zaria abaya,lalle Allah mai hikima da kari,su jabir kam sai zagaye masarauta suke,suna fadin”daliin kaza gadangare kansha Ruwan kasko,yau gashi dalilin gadanga sun shiga masarautu dadama,haka su madina ke Fadi,ummah ko baki yaki Rufuwa godema Allah kadai take,domin dalilin goggo sun taka in ba basuyi tsammani ba,daganan Fadar tare da rakiyar Adalin Sarkin zazzazu suka iso anguwan dasu Goggo suka zauna,Allahu akabar Asalin gidansu nan nan kawu ya gyarashi yasaka wasu mutane suna zauna don Allah,saboda su kula da gidan karya lalace,zuwansu gidan yasa Sarki da Suwaiba suka tuna wasu al”amura da suka gabata inda dakinshi yake awanchan karon yanzu wajen ne aka kafa famfo,Maimartaba ya kurama wajen ido,hawaye suna taruwa a idonsa hakama Goggo,mutane anguwa kuwa da lbri ya samesu sunyi matukar mamaki,akwai dattawa dake da rai haryanzu,sai kuma wadanda suka samu lbrin bayan abun ya Faru,basu jima ba suka koma masaurata Tunda Allah ya wanke suwaiba da Da’nta,daganan kaduna suka dawo saboda Shirye Shiryen Tafiya chan Masarautar Tambari buzu ammh bayan An maida Auren goggo.

Kawu da Maimartaba basuyi Shawara dakowa ba,washegari bayan sallaar Jumma”a aka maida Auren goggo da Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,akan sadaki dubu Dari biyar,wanda awajen Daurin harda Maigirma gwannan jahar kaduna,Wanda aka daura amsallacin Sultan bello,Yan mazan ne kadai suke da masaniya sai da suka dawo gida suke Fada,goggo jitayi Abun yayimata wani banbamrakwai daki ta Shige tarufe kanta ganin yaran sun Faramata shakiyanci da Amarsu????,Gimbiya Fasilatu kam dataji lbri kamar ta mutu takeji ga Danta Shima gabadaya taga baya tsaginta yana manne da dan’uwansa kamar wani zai rabasu,ga gimbiya Razeenah itama ko ajikinta harda ita cikin masu cewa agyara musu goggo,don so suke maimartaba ya rude fa????Ummah mai babban daki kuwa wani lokacin tafi zama cikin Su Jabir kodon yadda take sakasu dariya,suko su Zafira basu iya saakewa ciikinsu saboda yadda su Haisam da jabir ke damunsu da kallo,Umar ne ya lura har ya shafama Aliyu,dariya takamasa yana fadin”Daz great,karabu dasu lalle wasu yara zasu dawo cemin babban yaya”Yafada yana dariya har ga Allah Abun yayi mishi dadi ko banza zai samu hanyar sakamusu da Abunda sukayi mishi,kuma zumuncinsu zai kara karfi fiye da Da.

 Washegari kawu ya umarci Ummah da Goggo da Azeema da Aliyu su tafi gombe su tattara kayan goggo,tayi sallama da mutane saboda jibi zasu tafi chan masarautar Agadez,Gimbiya Razeenah ma tace zata,nan su Zafira sukace suma wlh sui sunje suna makale da princess dinsu,Mota biyu sukayi daya Aliyu ke driving tare dashi Umar,sai baya kuma Ummah da gimbiya Razeenah sai Goggo,dayan motar kuma Haisam da Jabir sai Azeema da Su zafira,wadanda su Jabir suka dinga jansu da zence,itako Azeema sai dai tayi musu mirmishi,suko yan matan basu saba ba duk kunya sukeji,Aliyu ko bini bini ya kira Jabir awaya yana fadin”Subi mai mata da kanne a hankali in ba hakaba ya hana abasu auren”Shuru sukayi suna Tunanin kashinsu ya bushe Tunda yaji lbrin ai sufa sai Abunda suka gani.

 Sun isa gombe lafiya,su ummah suka Shiga gidan suka fara hadama goggo kayanta masu amfani,itakuma goggo tafara Shiga makota sallama,suna sallama tana kuka,sune har gidan Baba Ade,wacce itama tayi damara tace wlh da ita za’a Raka goggo masarauta????goggo ko taji dadi tace ta Shirya su koma kaduna tare,kai goggo mai jama”a ce haka layi yacika,duk gidan data Shiga sai sunyi kwallah rabuwa da goggo Shekaru wajen talati sai yau kwatsam ace za”a rabu,toh basu da yarda zasuyi Tunda yanzu goggo ta wuce da saninsu matar sarki guda,Anan sukejin lbrin dawowar Azeeza goggo taja hannun Azeema suka Shiga cikin gidansu,Wlh da goggo da Azeema da sukaga Azeeza basu iya ganeta ba,saboda yadda tazama wata kamar kwarangwal duk kiban nan bata yanzu ta rame ta lalace tayi baki sai wasu kuraje afuska,ta kode ta lalace tana kwance kan tabarma daga ita sai daure gaba tana wani numfashi ba dadin ji,dukawa Azeema tayi gaban Azeeza tana kallonta tana hawaye take Fadin”Azeeza..Kice kika koma haka meyafaru dake? Inna ramatu dake gefe ne tace tana hawaye”Haka Aka dawomin da ita Azeema,ashe tun kamata da”akayi take rashin lafiya,ciwo ba”asan daga ina yake ba,tunda dai tadawo take kuka da kirjinta sai kuma ciwon kai mai tsanani,tabari muje asibiti,taki bari bansan me take so amata ba..”Kuka share share Inna Ramatu take tana durkushe gabansu goggo tana fadin”Don Allah Azeema da goggo ku taimaka kumin aikin gafara,wlh harda hakkinku ke bibiyanmu,na kyamaceki na wahalar dake,ke kuma goggo nabata miki suna sosai agari na cewa Aliyu bashi da uba gashi yau Allah ya nunamin iyakata,Ga Azeeza itama wlh harda hakkinki Azeema don Allah ki yafemata..”Tafada tana kuka,kamar zata Shide Azeema kuka take tana rike hannun Azeeza wacce ke miko hannu tana so tayi mgana Rikota Azeema tayi tana fadin”Sannu Azeeza Allah yabaki lafiya na yafemiki Duniya da lahira..”Tafada tana hawaye hakama goggo ta riketa tana jadadda yafiyarta,suna nan durkushe sai ga Mallam lawal sun Shigo Shida su gadanga,Shikanshi Aliyu dayaga Halin da Azeeza ke ciki sai da ya kauda kai,jabir ne yafara Fadan meyasa ba”a kaita Asibiti ba,Mallam lawal ya amsa da fadin”Ba inda zan kaita indai da kudina ne,kubarta tana girban Abunda ta Shuka ne..”Goggo ce ta katseshi da Fadin”A”a mallam,kada kace haka itama ya’ce kamar kowa,kuma tayi nadama don Allah ka yafemata”Jin sun saka baki yasa yace ya yafemata,Azeeza na kwance tana kallon Captain Aliyu tana hawaye,domin duk inna tabata lbrin mahaifinsa da duk Abunda yafaru,hawaye take tare da nadamar Abunda ta aikata,gashi yanzu tana ji ajikinta mutuwa zata yi,ammh kuma zata mutu da soyayyar Aliyu aranta domin ba ita ta dorama kanta ba,Aliyu ya Furta yayafemata,ammh fa Susinshi baijin zai iya badawa,Azeema ce tabata Dubu hamsin,wanda cikin kudin da kawu yake bata in yazo take Tarawa,Haisam da tsausayi,shima 50k yaba Inna Ramatu yace akai Azeeza Asibiti Allah yakara lafiya,Shidai jabir da Aliyu sisi basu bada ba,don aransu ma dadi sukeji ko banza anrage mugun iri,sallama sukayi musu suka Fito,inna ramatu har kofar gida kamar zata kwanta musu saboda godiya,nan nema goggo tace su Mallam lawal su tashi su dawo gidanta da zama ta mallaka musu halak malak,in Kawu sun dawo zai sa azo abuge gidan nasu ahade musu da wannan,Hakika mallam lawal yaga karamci,domin nan take maimartaba dake chan yace asanar da mallam lawal An biya musu kujeran makka,shida matarsa ai inna Ramatu harda Faduwa saboda taji Abun abazata ne,oh Duniya yau ga wanda ta wulakanta,sune gatansu Ashe,godiya sukayi ta zubawa kamar ba gobe,goggo ko tayi rabon kudi sosai,haka mutane suka cika bakin motarsu suna Fatan Allah ya kaddara saduwa gimbiya domin dai sun san,cewa kila sai dai kuma a lahira,koda suka bar anguwan haka goggo ke kuka babu wanda ya nemi hanata domin sabo yawuce komai,shikanshi Aliyu da bai cika zama ba, yau yaji Jikinsa yayi sanyi da barin gombe koba komai cibiyarsa ta haihu tana Gomben,ammh kafin sutafi saida ya biya mkrantarsu Azeema sukayi mgana da principal din,cewa Azeema zatayi tafiya,koza”a samu wacce zata cigaba da rubuta mata jarabawan kan tadawo,da hanzari ya amsa mai da za”a samu,kudi mai yawa Aliyu ya bashi sukayi sallama,bayan ya damka mishi Exam card din Azeema wanda yakarba Ahannunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button