ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

 Wannan labrin yatadama gwannatin Nageria hankali ba karami ba,Su Umar da sukaji lbrin kuka reras sukayitayi Shida Jabir,basu da karfin gwiwan zuwa da wannan lbrin gida saboda zuciyoyo sun Raunta Ainun,sukansu Karfin Addu”ane ke Tafe dasu,nan da nan Cheif of Staff,yabada sanarwan Shirya jiragen yaki masu dauke da Na”urori zuwa Dajin na Sambisa Domin Ceto Wadanan Sojojin don Kasa bazata barsu su salwanta ba,duk da suna kyautata zaton samun Araye.

*Janafty

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

    *Chapter 36*

  “Washegari Sojojin suka yima Dajin Sambisa tsinke,wannan karon harda manyansu atare, dasu bayan su Umar da Jabir da Sauran wasu jajiratattun Sojojin,Ta jirage ne wadanda ke da Na”irorin Daukan Hoto ta kasa,ma”aikatan dake cikin Helecopter din suna ganin duk wasu kananan Abubuwan dake cikin dajin,ta Na”urorinsu,cikin ikon Allah suka tarar da wani sansani na yan boko haram din acikin chan kuryan Daji,Umarnin yin kasa akabama Jiragen bayan kowani Soja ya saka rigar iska,sun Fara sulalo wa kasa,Mamaya suka yi musu ba Shiri kawai sai dai sukaji tashin harbi kokafin su Fito da Makamansu sunyi musu kwanya harbi kota ko”ina domin Sojojin suna dayawa Suma,nan Fa akaita bata kashi har na tsawon Mintina Talatim kafin sojojin su samu Nasarar kashe wasu ammh duk da haka akwai wadanda suka kara Nausawa dajin,suma acikin Sojojin an samu Wadanda suka Raunata,ammh ba!a samu rasuwar rai ba,nan da nan suka kafa sansani bayan an Fitar da masu Rauninka likitocin cikinsu na basu Taimakon gaggawa.

Cikin katon sansaninsu da Sojoji sukayi watsawatsa dashi aka gano Sauran Sojoji 8 daga cikin wadanda suka bace,suna daure dukkansu da kacha,duk sun rame sun lalace,dukkansu babu riga ajikinsu,ko”ina tabon bulalane da sara alamar dai Suna cikin wata rayuwa,cikin azama aka kwance su aka daukesu zuwa sansanin sojojin domin basu Taimakon gaggawa Major Sadeeq Amfani ne ke Fadin!where iz Captain Aliyu Naseer..’?yake Fada Ahankalinshi take,sai alokacin Sauran Sojojin suka Fahimci babu Aliyu aciki,nan fa hankalu suka Tashi nan da nan akace su Jabir su sake bazama cikin dajin domin sake dubawa kila a dace su ganshi.

Aikuwa hakane ta Faru basuyi nisa ba,suka iske wani sansanin ammh babu kowa aciki,koda suka Farma wajen sai suka tarar da wani mutum Daure daga saman hannayensa da kasa ma an Dauremai kafafu,Shibai kai tsakiya ba,shikuma bai sauko kasa ba,kansa na sunkuye ne jina na zuba ta hanci ta baki,bayan Kafarsa ta dama daure da wani kyalle,ammh haka jini ke zuba awajen,gashi ta kumbura,Tsaye sukayi cak suna bin Mutumin da kallo,Abu daya yasa su ka gane wannan nasu ne,wandon Sojan Nagerian dake jikinsa,wanda yachanza kala saboda jini,Jabir daje tsaye yayi kukan kura yana Fadin”Dude….”Yafada da duka muryansa bude,wanda harsaida Dajin ya amsa,hatta sauran Sojojin dake baya da suka ji suka Biyosu aguje dauke da makamai.

Umar najin haka ya karisa garesa suka rikosa baya Numfashi alamar ma Asume yake,wasu daga cikin Sojojin suka fara Zagaya wajen suna dube dube,wasu kuma suka isa wajen suna kokarin kwance Aliyu,awurin kwancensa ne suka Fahimci yana da karaya biyu Akafadansa ta

 dama,bayan kafarsa ta dama ta Dauke da harbin bindiga,ammh an cire harsashinsa,sai kafarsa ta hagu itama tana Dauke da karaya,sai wasu kananun gocewar kashi,kuka reras Su Umar keyi na tsausayin Halin da Aliyu ke ciki,haka suka Daukosa ko”ina na jikinsa ya saki kamar gawa,suna Fito dashi manya sojojin suka karisa garesu da hanzari Jabir ne yake sanar dasu irin Rauninka dake jikinshi,nan da nan Major Sadeeq  Amfani yasa su Jabir da Sauran Sojojin su cikon 8 din da kuma wadanda suka jiggata su shiga jirgi tare da Likitocin cikinsu su koma chan Asbitin Federal Ta Abuja,domin basu Taimakon gaggawa,su in sungama tararra komai zasu zo daga baya.

Cikin kankani lokaci aka sakasu cikin jirgin suka lula sararin samaniya,tun acikin jirgin Likitocin sojojin ke bama Aliyu taimakom gaggawa,ammh har zuwa lokacin bai farfado ba,sun dai samu daman warware kafar data keda harbi sukayimata dressing kafin su isa Abuja,shiko Chaif Amry of Staff tun suna chan lbrin ya sameshi cewa an ganosu,nan da nan suka sanar da kafafen yada labarai na Gano wadandan Sojojin dasuka bata ayayin kwantar da tarzoma agarin na maisuguri.

Suna isa Abuja direct asibiti aka wuce dasu,wanda yafi jin jiki Aliyu ne domin Shine baya cikin hayyacinsa,suko Sauran Tun acikin jirgi suka dawo hayyacinsu,Emagency aka shiga dashi domin bashi taimakon gaggawa da kuma daure karayan dake tare dashi,ga kuma harbin bindiga wanda ya dade ajikinsa don ma dai Allah yasa Tun lokacin da Abun Yafaru an cire harsashin.

Lokacin da lbrin kuboto da Sojojin dasuka bata ya zaga Duniya gabadaya Mutane nata murna,ciki harda Ni”ima wanda Tun sadda taji harda captain dinta awanda ake nema,ta Shiga tashin hankali,sai kuka ta addu”ar Allah ya dawo dashi lafiya,jin dawowarsu har saida tayi sujjudan godiya ga Allah,duk da ba”a Fadi Ahalin da suke ciki ba,an dai ce Sun samu Raunika ammh ba na tada hankali ba,suna babban Asibiti dake Abuja suna amsan Taimakon gaggawa.

  Kawu Shine kan gaba wajen samun lbrin wayar Umar yakira Shiyake labartamai halin da Aliyu ke ciki hankalinsa ya tashi nan take ya biyo jirgi zuwa Abuja,Shiko Umar suna gama waya da kawu ya kira Maimartaba ya Fadamai Halin da”ake cki..Wai Fadar irin tashin hankalin da Maimartaba ya Shiga Fade bata baki ne,salati kawai yake yana kiran Sunan Allah,lokacin dayake sanar da goggo zaman ya bori tayi hannu bisa kai tana kuka,maimartaba na bata baki,gimbiya Razeenah da Ummah mai babban daki da Baba Ade sai gimbiya Fasilatu kadai sukaji lbrin Abunda ke Faruwa,sai waziri da shamaki wanda maimartaba yabada Umanin ashirya musu Tafiya zuwa Nageria.

Goggo tayi kuka tana Fadin in Aliyu ya mutu ne asanar da ita,ammh maimartaba ya dagemata bai mutu ba da Ranshi,Azeema kuwa babu wanda yake da karfin halin Sanar da ita,saboda yaya lafiyarma kura balle tayi zawo,bata da aiki kullum sai kuka tana Fadin Yaya captain ya mutu ne ba”a san gayamata ne,ga cikinta daya shiga wata na Takwas,yayi girma sosai ta kumbura tako”ina gashi yana neman Rinjiyarta in ka ganta sai ka tsausayamata Saboda yadda ta rame ta lalace kamar ba Azeeman Kaduna ba,Su Zafira na iya bakin kokarinsu na kada Azeema ta damu ammh ina Ita bata su take,kewa tare da zafin ciwon mijinta kadai ya isheta,tayi kuka kamar zata mutu ammh kullum hakuri ake bata,akwai likitar datake duba matan maimartaba ita ke kula da Azeema,duk sati sai tazo ta dubata tare dayi mata Fadan,ta rage saka damuwa aranta don hatsari ne mai tsohon ciki tana da hawan jini,kuma baya kasa kullum saima karuwa dayake,Azeema kallonta kawai take aranta tana Fadin”kaji mata,wato na zauna nayita kwanciyar Hankali mijina ya tafi yaki bai dawo ba,lalle ma wannan kwakwalwarta tatabu toh jinin yayi ta hawa ai badai Ranar sauka sai Muradin Ranta yadawo,Ko Zafira da Jabir ya kira ya sanar da ita Gargadi yayimata na koda wasa karta gayama Azeema,saboda ba”a ce asanar da ita ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button