ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Haka akatashi taro,kowa yakoma gidansa lafiya,shima Aliyun bai tsaya anan Abujan ba,kaduna yakoma saboda samun damar parking din wasu kayansa,dakuma sallamar Bakinsu,kwana biyun da karin girmansa yasamu ziyara daga Ni”ima da kawarta muneera Abun mamaki harda mami da Cp Ahmed Sidi na iya,saiga Kwamishina yana nemam Dukawa ma Gadanga wai yana rokonsa gafara saurin dago dashi yayi yana fadin”Haba Daddy taya zaka dukamin,nifa kamar dankane,ni wlh haryau a uba nake kallo ka, don Allah bari ni babu Abunda kamin,kuma wlh ban rike ba”Kwamishina yaji dadin kalaman Aliyu har cikin Ransa yana ta godiya,Aliyu har Gidan Jabir ya karisa dasu suka gaisa da kanwarsa zafira inda tarasa inzata kaisu saboda hidima,Ni”ima tatambayi Azeema nan Yake sanar da ita basu dawo ba tana masarauta ammh zasu dawo kwanan nan,Rokonsa tayi don Allah in yana da hoton Triple ya nunamata,nan take yafito dashi ya haskomata,Santinsu Ni”ima tahauyi tana nuna musu Daddy da mami tana fadin”Daddy ku kallesu,suna kama da captain dina'”Kowa yaji Abunda tace itako da iya gaskiyarta take,bata kula da Abunda tace ba haka ta mikama muneera sunata santinsu,Shiko Umar na gefe Shida Jabir,ammh duk motsin da Muneera zatayi a idonshi baisan dalili ba,tunda suka hada ido da yarinyar yaji faduwar gaba itama haka take abangarenta,duk sanda ta dago ido,sai sun hada ido da Umar,tsarguwa tayi da kallon nashi tatashi ta Fito waje shikuma ya biyota da hanzari yana Fadi aransa”oppourtniy comes one in life”Gwara yayi amfani da damarsa kafin ta kubcemai,yana Fita ya ganta jikin motarsu,nan fa ya karisa gareta da gaggawa ya isar ds sakon zuciyarsa muneera can belive itace wannan hadadden gayen ke cewa yana sonta,kuma ma Dan sarki wow..Gaskiya Abunda bata taba tsammani ba,nan da nan tabada kai bori ya hau,nan take sukayi Sharing nombar juna,suna cigaba da Hiransu,suna bama juna lbrin juna,kafin wani lokaci duka zuciyiyon sun yarda da juna,koda su Ni”ima suka Fito nan suka tarar dasu suna zuba hiransu,duk wanda ya gansu sai da ya fahimci wannan ankullah soyayyah mai karfi,Ni”ima Abun yayimata dadi,dama kullum addu”arta Allah yabama muneera miji nagari tayi aure,sai gashi Allah ya bata,kanin gadanga ta yarda ko batada rabon Auren gadanga toh Muneera zata auri kaninsa suyi zumunci na har Abada,Gadanga bai nuna bacin rai ba,saima kallon Ni”,imar dayake da tsausayawa,yana yaba halinta na bata hassada da kyashi,ko fada da wani Ni”ima mace ce so simple shidaya zauna da ita shi zai bada lbrinta,cikin mutumci da karramawa suka tafi bayan Ni”ima ta ciko wasu bakaken ledoji da kayan babys dana Azeema tabashi tace abaiwa mejego da Farko kin amsa yayi saida ta nuna bacin ranta kana ya karba,har suka bar haraban gidajen nasu tana dagamai hannu,wlh haka kurum yaji kwallah,yakuma tabbatarma kansa Ni”ima tanayimai So daya ne tak,babu Surki,gida ya Shige dauke da kayan yana mamakin irin Taurin kan Azeema ko Text batayi mai ba,kuma ya tabbatar da taji lbrin komai,umh wlh xata gane bata da wayau ne, don ya lura yanzu pretty bata shakkarsa.

  Achan masarauta kuwa Shirya shiryan dawowan Azeema ya kamkama domin wajen kwananta hamsin kenan da haihuwa ta warke tayi garas da ita,kamar ba ita bace mutane uku suka tsagata suka Fito ba,gyara kuwa tashashi kamar ba gobe ita da kanta takejin kewar mijninta yana tasomata ammh tana kokarin dannewa,Su Afiya kuwa sun kara wayau da girma gasu da jiki Tububu kamar ya”yan Turawa,duk wanda ya daukesu bayan son ya jiyesu saboda sha”awa,ana gobe zasu taho Goggo ta kira gadanga ta sanar dashi nan yake sanar da ita su sauka ta Abuja saboda yanzu ma haka yana Abujan ne tun shekaran jiya yabaro kaduna,jin haka yasa goggo kiran Ummah ta sanar da ita,itakuma Ranar da su Azeemar zasu iso Tun safe direba ya wuceta da ita Abujan,Aliyu yazo yayi musu jagora zuwa cikin barikin,wanda kamar ma ba”a Nageria yake ba,ashe na kaduna kauyene,????Akuma Aranar su Aliyu suka raka rundunar hadakan sojojin camero da chadi da niger,suka hau jirginsu domin komawa kasarsu,ciki kuwa harda Umar,wanda yakoma kasarsa domin cigaba da gudanar da ayyukansu,ammh yace Nigeria tazama gida garesa,Tunda yanzu ma Anan zai dauko mata.

*am srry for d typing error,ban samu damar tacewa ba*

  *Janafty*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_Special Day..!Special person,..!Special birthday..????????????..! *1/1/2020* May dis Day be d begining of Anoder beutifull year 4u…May there be pleasant,suprises…Loads of joy And infinite happiness…Wish u a very Happy birthday *HEARTBEATDADDY*_????????????❤????????

        *Chapter 39*

“”Azeema sun sauka A abuja lafiya,ita da gimbiya Razeenah sai Inna Ramatu kadai sukazo,sai wata baiwa mai Suna Lami,dattijuwace sosai wacce zata dinga taimakama Azeema da kula dasu Anwar,inna Ramatu kuma daga nan Abujan gombe zata wuce wajen mijinta.

    Gimbiya Razeenah ita takira gadanga awaya ta sanar dashi saukansu,bai dau lokaci ba sai gashi yazo Filin jirgin na Nnamdi Azikiwe international Airport,koda ya iso,wajen da Azeema yafara tozali ya kalleta ta kalleshi lokaci daya suka dauke kai,kowa naji da kansa,cewa shi aka batamawa saboda haka shiza”a bama hakuri,ko su Anwar hannu Baba lami ya karbesu kafin ya daukosu su rankayo zuwa cikin barikinsu dake Abuja,ko zaman motan baya ta Shige ta hade rai sosai,gimbiya Razeenah ne ta Shiga gidan gaba.

Suna isa suka tarar da kyau da tsari irin na gidajen wajen harsunfi na kaduna ma girma,domin na nan din 3bedroom ne,da kuma falo har guda biyu,bayan katon kichen mai hade da store,kuma ko”ina yaji kayan alfarma babu Abunda ake bukata dama sai kayan da mutum zai saka su kawai zai zo dashi koda suka iso Tuni Ummah tagama gyara ko”ina harta Abinci sai tayi musu,suna zuwa Sallah sukayi kafin su zauna suci Abinci ana hiran Duniya da tambayan Mutanen chan,itako Azeema tunda tayi wanka tashige dayan bedroom din ta kwanta ko kara lekewa batayi ba,su Afiya suna wajen Baba lami,suma sunyi barci Tunda sukaji Ruwan zafi,da kuma nono,shikenan aka daina jin motsinsu,shiko gadanga Tunda yakawo su ya fice bai kara waiwayan gidan ba,saboda bayaso su Raba hali Shida Azeema don yaga take takenta so take yau takureshi har yatankanta.

Basu samu tafiya ba sai washegari da safe Gimbiya Razeenah da Ummah sai inna Ramatu suka rankayo sai kaduna suka bar Azeema da Baba lami da kuma mijinta Aliyu gadanga,daga kaduna ko kwana inna Ramatu batayi ta matsa tana son komawa gombe aranar Shiyasa Kawu Bala yasaka Direba ya kaita dauke da sha tara na arziki data samo daga Masarauta,dakuma wanda Kawu yakara mata,Gimbiya Razeenah dai tanan nan sai ta kwana biyu inji Ummah.

Tunda Su Ummah suka Tafi Azeema tashige bedroom din data zaba amtsauyin nata,takarayin wanka ta Shirya cikin Riga da sikat na Atamfa,wanda suka dauketa sukamata cas dasu,Baba lami na Falo tana Fama dasu Anwar yan Rigima itako kichen tafada domin lokacin har 11 ta gota yakamata tadora musu lunch ko badon Shi ba,don cikinta dana Baba lami.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button