ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Innalillahi wa”inna Alaihirraju’un,Kullu Nafsin za”ikatul Maut,kowani mai Rai sai ya dandani Dacin Mutuwa,yau dai ga Azeeza ta amsa kiran mahallincinmu Tatafi da duka burinkanta da mafarkanta Allahu akbar Shiyasa akace ka Shuka alheri kodon Watarana bakasan Yaushe zaka mutu ba,Inna Ramatu Kuwa tayi Tawakalli tare da Azeeza ta kwana har sai da Asuba ne ta kira mallam ta sanar dashi,cikin tashin hankali yake kiran sunan Allah,Gabadaya jikinsa yayi sanyi yakara tsorata da rayuwa Fadi yake Aransa Na yafemiki Azeeza Allah ya karbi bakuncinki.

 Sai da gari ya waye Mallam Lawal yazo akayi cike cike aka basu Gawan Azeeza suka zo da ita gida,Lokacin mutuwar ta Azeeza tagama zagaye gari kowa sai Fatan dacewa yake mata,Ba”a dauki wani lokaci ba Inna Ramatu da kanta tamata wanka ta Shiryata aka dauketa Akayi mata sallah,Aka tafi da ita zuwa gidanta na gaskiya,Allah sarki Rayuwa kenan komai yayi Farko yana da karshe gashi yau Azeeza an tafi an bar Duniya an kaita an Turbeneta daga ita sai Halinta,sai Fatan muma Allah sa mucika da imani AMEEN.

Mallam lawal ya kira Kawu Bala da kanshi ya sanar dashi Rasuwar Azeeza,salati ya dingayi Abun ya tabashi,haka daya sanar da Ummah itama ta shiga sallallami tana Fadin”Kaji Abun Allah ko,yanzu Duk Abunda tagamayi Ashema ba rayayya bace kai wanda bai bi Allah da manzonsa ba awannan Rayuwar wlh yaji takaichi Allah ya jikanta da Rahama”Kawu ya karba da Ameen da Ameen,Ummah ita takira su Madina ta sanar dasu Rasuwar Azeeza,su kansu Mutuwar ta dakesu,nan sukace in Su Ummahm zasu don Allahu su sanar dasu suma su bisu suma mallam lawal gaisuwa.

Kawu da kanshi ya kira Maimartaba Awaya ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,lokacin suna tare da goggo ya mikamata wayar Kawu bala ya sanar da ita Rasuwar Azeeza,mikewa goggo tayi tana Fadin”innalillahi wa’inna Alaihirraju’un Yaya Wata Azeezan? yace”Azeeza dai kanwar Azeema diyar mallam lawal”Dafe kai goggo tayi Tana Fadin”Allahu akbar kabirin ashe Ashe ganin karshe mukayi mata nida Azeema,kai Allah kabamu mutuwar Shahada,Allah ya karbi bakuncinki Azeeza”Kawu da Maimartaba dake zaune suna karbawa da Ameen,

 Dauke kwallar data zuboma Goggo maimartaba yayi bayan Kawu ya yanke kiran,Kanta ta dora bisa kafadansa tana Shesshekan kuka,babu shakka mutuwar Azeeza ta daketa,mutuwar matashiyar budurwa ko bakomai Yadda ta dauki Azeema ya’haka tadauki Azeeza,Allah yajikanta da Gafara,hannu maimartaba yasa ya Rumgumo goggo yana buga bayanta alaman lallashi yake Fadin”Shiii..Kibar mata kuka hakan nan,mutuwa fa dole ce gimbiyata,addu”an mu kadai take bukata yanzu plz wipe ur tears”Yafada yana dago Fuskarta,Tirr na kame gefe ina kallon Salon soyayyah manya bansan sanda na saki ihu ba ina Fadin Allah dai ya biya Ranka Shidade????

 Goggo ta dago tana riko hannuwan maimartaba tace”Yallabai na????????Bakowa nake Tunani ba sai Azeema kaga fa ga Halin data keci yanzu ya zataji in taji mutuwar kanwarta wacce ita kadai gareta”Ajiyar zuciya maimartaba yayi kafin yace”Hakane karki damu da wannan ki kiramin ita ni dakaina zan sanar da ita..”Yafada yana kallon kwayan idon goggo,wacce tawuce luu,zuwa kirjinsa tana share kwallarta Shiko yayi Saurin tarbanta yana Bubbuga bayanta alamar lallashi domin yakijinin yaga goggo cikin damuwa,Gimbiya Fasilatu data Shigo Turakar maimartaba yanzu,tun da zata Shigo Fadawan bakin Shashen suka sanar da ita Gimbiyar Mata fa tana ciki,saboda haushi ko sauraransu batayi ba,ta Shigo ciki kai tsaye,aiko tayi mugun gani,har tagama Tsayuwarta basu san da kafuwarta ba,kishi ne ya Rufemata ido yasa ta Fice da hanzari tana share kwallah,ahanya taci karo da gimbiya Razeenah ita da bayinta zata shashen Ummah mai babban daki,tana ganinta tayi Saurin daidata fuskarta,wanda ta riga ta makaro tuni ta gnta,sai da sukazo gota juna kana gimbiya Razeenah tace mata”wlh kina wahalar da kanki Fasilatu,kinfi kowa sanin yanzu baki da wani Fada gun maimartaba,dama fa arashin uwa ne akanyi uwar daki,in ma zaki kama kanki ki kama,in kuma zaki cigabane toh bismillah,iskane zai cigaba da Wahalar da mai kayan kara..” Tafada ahankali yadda babu mai jinta sai ita gimbiya Fasilatun,tana gama Fadin haka ta wuce ta barta nan tana cizon yatsa 

 Goggo da kanta taje har Shashen Azeema ta taho da ita har Turakar maimartaba,in kuka ga Azeema alokacin sai kun mata kuka,saboda yadda ta rame ga cikinta ya fara Fitowa azahirin batu tana Fama da kewar mijinta,gashi ko awaya ba”a samunsu,hakama suma Zafira ma take cikin damuwa,don Safaratu kadai ke waya da Haisam suko su biyun Shuru ne kawai,Maimartaba cikin lallashi da nasiha ya sanar da Azeema rasuwar Azeeza,Tashin hankali wanda ba”a sakamasa Rana,haka Azeema ta mike jikinta na Rawa Tana Fadin”Azeezar ce ta rasu? take Fada kamar ta fita daga hayyacinta goggo ce tayi Saurin mikewa ta rikota ta rumgumeta tana lallashinta,kuka sosai Azeema take tana Tuna Fuskar Azeeza data gani na karshe,Tayi kuka kamar Ranta zai Fita,kome Azeeza tayimata wlh bata taba jin tadaina sonta ba,jininta bata da wata yar”uwa data Fita,haka wuni kuka tana rarrashin kanta ita kadai,maraici ya lullubeta babu uwa babu uba akusa ga rashin miji ga Rashin yar”uwa Duk lokaci daya Haka dai ta rarrashi zuciyarta harta kira Babanta tayimai gaisuwa tace ya bama Inna Ramatu wayar tamata gaisuwa,inna Ramatu najin sallamar Azeema Tafashe da kuka,ai sai itama Azeema tacigaba da nata,saboda yadda suke koke koke ne yasa mallam lawal ya karbe wayan ya kashe saboda ya lura cikinsu ba wacce zata iya mgana alokacin.

*BAYAN WATA UKU*

 Lokaci yayi Ta tafiya ayayinda Abubuwa dadama suka Faru ciki harda samun Nasaran dawowar Tawagarsu Umar,tsakaninsu da Tawaagar su Jabir kwana goma ne,Kuma Alhamdulillah an samu nasorori dadama,ansamu Kashe kashen rayuwa wasu sun Raunata gaskiya ammh Tunda ansamu Abunda Ake nema Shikenan.

 Iyaye da yan”uwa da abokan arzuka sunyi murna da dawowar ya”yansu lafiya,Jabir da Umar sunyi Farinciki sake haduwa da juna abunda basuyi tsammani ba ballatana Fata,yanzu Fatansu suga dawowar tawagarsu Aliyu wanda ta kasance kusan itace ta karshe bata dawo ba.

Daga chan Masarauta kuwa murna sosai akayi tayi da shagulgula na Dawowar Yarima umar,ammh duka fa zuciyoyo suna cikin Fargaba na Rashin samun wani bayani game dasu Aliyu,ammh an dage da addu”an Allah ya dawo dasu lafiya,Abun da ke Faruwa shine tun watansu daya da tafiya aka daina jin lbrin su kwata kwata awaya balle aji lbrin hadin da suke ciki,an kuma sake Tura wasu sojoji suma dinma dai haryanzu Shuru kake ji Topha Abun fa yafara Zama Abun mgana saboda dai Abun yaci ace in lafiya lafiya Toh sun isa suma su dawo alokacin 

Lokacin da Azeema taji lbrin Dawowarsu Umar ammh babu Mijinta aciki sai fa hankali ya tashi rai ya dumguzuma,bata da aiki sai kuka ga cikinta lokacin yashiga watansa na bakwai takara girma da Cika gashi cikin yana da girma sosai,tuni ya Turo gaba kamar cikin wata Tara,sukansu maimartaba karfin hali ne ke tafe dasu ammh fa sun Fara sarewa,Su Umar suna Nageria haryanzu domin ana kokarin Shirya wata tawagan ne zuwa chan maidugurin aje adubo ko lafiya don Shurun yayi yawa.

Kwatsam sai ga wasu daga cikin Tawagansu Aliyun sun dawo ammh babu Aliyu aciki da wasu daga cikin tawagan sojojin su Tara kaf,Sojojinn nageria su hudu,hudun na Cameron ne,kuma kowannensu shugabannunsu suna alfahari dasu sakamakon dukkansu zarata ne kuma jarumai ne,koda suka dawo aka tambayesu ina Sauran yan Tawagansu nan suka bada lbrin cewa wata daya daya wuce yan boko haram sun Farmakesu a sansaninsu dake Sambisa,inda sukayi bata gashi dasu,toh Lokacin an samu rabuwar kan Sojojin,akwai wadanda aka kashe ckin dajin kuma su basuga gawarsu ba,bayan komai ya lafane suka nemi wadandan Sojojin suka rasa ciki kuma harda shugaban Tawagan Nasu Captain Aliyu Tambari buzu,to kuma tun lokacin suka rasa wayoyinsu na mgana zuwa headquater kai tsaye,lokacin da wasu tawagan suka sake zuwa ,sai suka sake sabon Shiri,shine dalilin yin nasaran Cafke yan boko haram har su goma sha bakwai,Sungama duba ko”,ina ammh babu gawarwasunsu toh suna kyautata zaton cewa kila sun kamasu ne,sun tafi dasu chan wani waje dabam kuma inda babu wanda ya sani sai su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button