BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dariya yayi yace “Me kikeci?”
Tace “Madara ce, ko zaka Sha?”
Daga d’ayan bangaren Huzaifa yace “banashan madara, idan Nasha wahala take Bani da daddare, Saide inzaki Bani da hannunki saina sha…”
Kunya ce takama Waheeda, tasaka hannu tarufe fuskarta kamar yana ganin ta 🙈
Uncle Usman ne yashigo falon yazo wajan Daddy, yaga yarinya Sai rufe fuska take ita kadai, ga Kuma waya a kunnan ta tanata murmushi
Qarasowa falon yayi cikin sigar tsokana yace “anata wayar ne Waheeda? Kode da sirikin nawa kike waya?”
Waheeda tayi sauri ta kashe wayar, sannan cikin kunya tace “Uncle Huzaifa ne…” tana fada masa haka, tashige dakinsu cikin kunya
Uncle Usman ya qarasa Dakin Daddy Bayan sun gama abinda zasuyi, Uncle Usman yace “Yaya yakamata fa Yaron Nan Huzaifa idan da gaske yake yaturo,inda zai iyu da anhada bikin Waheeda Dana Naufal”
Daddy yace “Eh da munji dadin hakan gaskiya, Bari zanyi magana da mahaifin sa, tunda Naga yanzu ta bashi Dama yana zuwa zance a koda yaushe nasan sun dedeta, zanyi magana da mahaifin sa, Saisuzo ayi magana kawai”
Kamar yanda suka yanke wannan shawarar kuwa, haka akayi, cikin satin iyayen Huzaifa suka zo neman aure, Daddy da Uncle Usman da baba Habu sukace sun basu 😥🤗
Waheeda dataji wannan labarin bata damu ba, asali ma murna taitayi cikin ranta, saboda har aqasan ranta tanajin soyaiyar Huzaifa, tana sonsa sosai, idan ta zauna ta dinga tunanin sa kenan, shiyasa tadauki zuciyarta gaba daya ta damqa ta ahannunsa
** *** **
A kwatuna ne a shirye daya kan daya guda goma Sha biyu masu launin brown
Minister ne a tsaye yana kokarin Kiran waya, tsaki yayi ya zauna tare da fadin “inaga babu network ne, tun dazu nake gwadawa Amma taqi tafiya, ai Gara afada musu lefe yahadu, yaushe suke ganin yadace akawo musu?”
Hajiya Babba mahaifiyar Huzaifa, tajuya ta kalli huzaifa dayake Sanye cikin kayan shan iska, yana danna laptop din gabansa, tasake juyawa ta kalli minister tace” yanzu Alhaji baka ganin wannan kayan sunyi yawa? Ina laifin ma a kwatuna hudu ko biyar? “
Kallan ta yayi yace” kinsan me kike fada kuwa? Kinsan matsayina awannan jihar kuwa? A kwatuna shabiyu ai sunyi kadan hajiya, ko bakisan gidan da za’a Kai bane? “
Cikin 6acin rai tace” nasani mana Alhaji, ba gidan buzayen Nan bane? Ni kwata kwata yarinyar Nan bata minba, kana ganinta daga ita har yan’uwan Nata kasan irin sadaka yallar Nan ne…, duk abi a rabaka da danka ta hanyar asiri “☹ï¸ðŸ˜”
Huzaifa ya kalleta yace” Momy…. Ni inason Waheeda, Kuma gaskiya bazan iya barinta ba “
Minister yayi Dariya yace”to kinji, Kuma nikaina nasan idan Huzaifa ya auri yarinyar Nan zan samu jikoki kyawawa… Kisawa yaro Albarka kawai acikin auren sa”
Hajiya Babba takama jijjiga kafarta, ranta in yayi dubu ta ya6abaci…. Daga Dan har uban haka suka qyaleta, minister yaci gaba da neman number Daddy
** *** **
Washe gari karfe Tara nasafe, a Nigerian tayi masa,Kai tsaye wajan shopping yaje yasiyo panties da Bra, lokacin dazai za6a tunani yake wanne size zai d’auka mata? Shide bai ta6a ganinta azahiri ba,bare yayi hasashe ya d’auka mata Kuma pant da Brezia babu size din wadda yasani saina Waheeda, danhaka batare da tunanin komai ba ya ‘Dauko mata daidai size din Waheeda 🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
kasancewar sa mutum
na mutane bai samu zuwa gidan Hajiya Anty ba, Sai karfe goma Sha shad’aya, Kai tsaye gidan yashiga, kasancewar tana takura masa da waya yazo yaga lefe, yasan cewa idan ya wuce gidansu baizo yaga lefe ba, to zata dinga yimasa Mita ne, shiyasa Kai tsaye ya wuce gidan Nata, maigadi Sai washe masa haqora yake yana kwasar gaisuwa, saida yayi masa yayyafin kudi sannan yabarshi yasamu ganawa da Antyn nasa.
Gabansa tacika da kayan break fast, Sai Nan Nan take dashi kamar zata saka shi ajikinta, waya yake amsa wa cikin farinciki, yau yana jin wannan zuwan nasa na musanman ne, tunda har yazo Nigeria dan rad’in Kansa ba fitinar Waheeda ce ta kawo shi ba 😃
Yana ajiye waya, wata wayar tasake shigo wa, Kuma gaba d’ayansu masoyansa ne, tun yana amsawa harya fara gajiya, Amma duk da haka bai fasa d’aukar wayar masoyan nasa ba, saida Hajiya Anty taga abin nasa Bana qare bane, kawai saita kwashe wayoyin ta kashe su, sannan tafara bashi break fast din da kanta, saida yaci yaqoshi sannan tajashi zuwa wani d’aki, photunan Waheeda ne birjik acikin Dakin, saikuma na Babban Yaya dasu Sa’eed, saikuma na dukansu yaran gidan dasuka had’u suka d’auka tace “toga kayan lefenka…”
A kwatunan ya kalla guda ashirin da hud’u, ya kawarda da Kansa yace “nagani, sunyi”
Cikin mamaki ta Kalle shi tace “tayaya kasan sunyi Bayan ko bud’ewa bakayi ka Gani ba?”
Kallan inners d’in daya kawo tayi tace “sannan wannan kayan daka siyo sunyi wa ummi yawa, na ganta ai rannan, wannan bra din tamata yawa, bansan de pant d’inba, kaida nace ka tambayeta size dinta meyasa zaka siyo?”
“ai itace tace haka ne size din Nata” ya qarasa maganar cikin d’aure fuska
Hajiya Anty tace “to shikkenan, zanyi magana da ummanku, Sai muji ranar daza’a saka akai musu kayan”
Yana jin ta d’auko hanyar maganar auren sa, ransa yaqara 6aci, babu shiri yayi mata sallama yabar gidan yanufi gidansu.
Tun abakin get mutane suka masa cincirundo, Sa’ad da Sa’eed suka tar6eshi suka qaraso gidan, Ummah bakinta Qin rufuwa yayi, babu Wanda yayi tunanin zuwansa, Sai gashi ya basu mamaki yazo, Ummah ta Kalle shi duk farinciki ya cikata, ganin yanda yasaki ransa tasan cewa may be ya yarda da auran ne tace ” ‘Dana,me zakaci? Me kakeso nayi ma?”
Kallan ta yayi,yayi murmushi dimple d’insa ya lotsa, su yanbiyu da Waheeda Sai dariya suke musu shida Ummah, ganin yanda duk ta rikice ganin Babban Yaya kamar sudin ba sauran yaranta bane, kafin Babban Yaya yayi magana Daddy ya kalleta yace”haba Hajiya,Naga alama yakamata nadinga tuna miki cewa Naufal bashine auta ba “
Waheeda ta turo Dan qaramin bakinta gaba tace”Bayan Ummah tafi sonshi Dani”
Ummah ta kalli Waheeda ta kalli Babban Yaya tace “rabu dasu Dana, me zakaci nadafa ma dakaina? Karka damu da surutun su Dama can kishi suke dakai”
Fuskarta yakama yariqe yace “Ummah tah ta kaina, inason ki Ummah, naci abinci a gidan Anty, can nafara zuwa Naga Kaya, karki damu kanki, banajin yunwa, anjima de keda kanki Zaki Bani abinci da wannan hannun naki” ya qarasa maganar yana kissing hannunta, Ummah ta kalli Daddy alamun bata gamsu da maganar da Babban Yaya yafad’a mata ba, Daddy yace “yace miki ya qoshi hajiya,ai yana Nan a gidan babu inda zaije, anjima saiki bashi abincin”
Sai a sannan Hankalinta ya kwanta, ta kalli Naufal dayake Kallan ta cikin murmushi tace “to shikkenan, kaje daki ka kwanta ka huta, Kuma ka kashe wayoyinka kajiko”
Yace “to Ummah nah” daga Nan yatashi yayi dakinsa, Waheeda ta kalli brief case dinsa daya manta bai tafi da’ita ba, tasan Kuma kudi ne aciki, idanuwanta Tajuya, tana fatan ace yabata ko 50k ne, cikin sauri ta dauki jakar tabi bayansa
Tana shiga ‘Dakin ta ganshi yana kokarin cire Kambos d’in kafarsa, Kallan ta yayi ba tare daya Dena abinda yake ba, cikin murna dajin dadin ganinsa tayi saurin qarasa wa wajan sa ta ajiye Brief case din akusa dashi tace “Babban Yaya ga kud’in ka” 😃
Murmushi yayi, ya kalleta yace “kud’i na kuma? Waya fad’a miki kud’i ne aciki?”