BARIKI NA FITO 1 & 2
Bariki u/kanawa tayi inda ta d’auki motar da Alh madu ya bata ta siyar wajan y’an motocin dake u/kanawa ta wajan NDA, bata amshi kud’in cash ba transfer tasa suka mata, sannan ta wuce gidan iyayenta na bariki,
inda abbanta na Bariki ya bata shawara akan ta dawo nan da zama domin d’an gidan sarauta zata aura Karta sami matsala dan inta sami matsala suma suna ciki tunda har dasu a cikin aikin…..
Bariki tace hakane nima nayi wannan tunanin amma tashi na daka can zaiba wasu dama su Fara bincike akan abunda nake shiryawa amma zan dinga kwana a nan camma ina kwana zan dinga diban kayana da kad’an Ina kawo su nan har lokacin bikin yayi a wuce wajan,
Ranan bariki a gidan ta wuni tana ta jiran kiran yarima amma shuru babu kira babu sa’ko, gaba d’aya jikinta yayi sanyi ta kasa sukuni dan tsaki taja tare da kiran Layin Yarima taji line busy alaman yana waya….. Ajiyan zuciya ta sauke tare da fad’in kenan da nice bazaiyi waya ba Hmmmm, babu damuwa ai gobe kace zaka zo wajan Abba zan gani in zaka zo, dan nasan baka karya alkawari saida wani dalili…… Bariki wajan 6 tabar gidan ta koma maraban jos akan cewa gobe zata zo da sassafe insha Allah dan Yarima tana tunanin zai zo……
Bariki koda ta koma ta kasa sukuni gaba d’aya, domin rashin jin muryan Yarima ya sata cikin wani hali, sai yanzu ta kara tabbatar ma kanta tana son Yarima Sosai, kuma zata iya aikata komai akan sonshi Indai Abun bai sabama Shari’a ba duk da tasan wannan auran da zatayi da Yarima bai dace tayi ta wannan hanyar ba, toh amma yata iya tunda haka tata kaddaran tazo Mata, yanzu inta koma Gida AI Yarima zai gane karya ta shirya mishi tun Farko, wani hawaye ne mai zafi ya silalo mata tabbas duk Wanda yabar Allah…… Allah shima ya barshi…… Ta fad’a wannan halin ne duk saboda aikata sabon Allah, gashi Allah ya jarabceta da son Yarima wanda bata son ta rasashi, saboda son da take mishi yasa tana kokarin kara jefa kanta cikin wani bala’in ta tabbata koda Yarima Aliyu ta bashi Labarin ta ya hakura ya amsheta a matsayin mata, toh iyayenshi fah? Ya zasu d’auketa da sauri ta tashi tsaye domin bata taba tunanin iyayenshi a duk cikin wannan abunda take shiryawa ba, ya iyayen Yarima zasu d’auki abun, gidan sarauta gidan Kima da daraja, gidan da babu wasa a cikinsa, kuka ta fashe dashi Mai sauti lallai ina kara jefa rayuwata cikin halaka……. Kuka take Sosai tana surutai ya iyayen Yarima zasu d’auki wannan abun, na tabbata bazasu hakura ba su, sai Sun hukunta ni akan wannan laifin da nake shirin aikatawa, bariki gidan sarauta ne gidan su Yarima ba gidan wasa bane, irin wannan auren bai kamata kiyi shi a gidan sarauta ba, lallai sarauta ba wasa bace, sarauta ba karya bane, ido ta lumshe tunawa da yanda Yarima yakeyi kana kallonshi kasan akwai jinin sarauta a tare dashi Sosai yanda yake abu…… Lallai Indai Ina son Yarima ya kamata in fad’a mishi koni wacece…… Da sauri kuma ta Fara girgiza kai tunawa da tayi yana fushi da ita akan ance ana son ganinta, jiba yanda ya nuna kishin shi akai inaga yaji tana bin maza kuka ta kuma saki na tabba bazaka aureni ba Yarima inma ka yarda Wlh iyayenka bazasu Bari ba, dan gidan sarauta baza’a Bari ya auri karuwa ba k’asa tayi tana kuka lokaci d’aya kanta ya fara mata wani irin azababban ciwon kai ga idonta daya kad’e yayi ja, Kun San farar mace ba wuya, in tayi kuka a gane, kwanciya tayi a k’asa tana kuka, wayarta keta kara amma ta kasa tashi ta d’auka dan bata jin zata iya tashi domin yanda take jin kanta………. Lallai rayuwar bariki ba komai bace face kaskanci da wulakanci Wanda ta tabbata bata ga komai ba sai ranan da Yarima yasan ko ita wacece…. Bugun kofar da ake mata ne yasa kanta yake ta kara mata ciwo dakyar taja jiki ta tashi ta bud’e…..
Habib yaja baya yana fad’in ya ilahi Mai zan gani haka?? Bariki baki da lafiya ne? Maiya sameki?
Bariki kanta ta nuna mishi da hannunta alaman kanta na ciwo
Habib cikin tausayin bariki yace sannu Allah ya baki lfya, Yarima yazo yana jiranki har yaje ya nemi izini wajan mahaifinki na Bariki,……
Da sauri bariki tace dagaske? amma gobe yace zai zo
Habib yace Toh gashi yazo yau, shima Nasan yayi kewarki sai yasa yazo dan haka maza kizo muje yana Bayan layi yana jiranki, yace ya kira baki d’auka ba shine ya kirani, shima abbanki na Bariki yaita kira baki d’auka ba yana son fad’a miki wai baki dad’e da tafiya ba Yarima yazo yasa akai sallama dashi…..
Bariki da sauri tayi toilet ta wanke fuska sannan ta kara feshe jikinta da turare ta yafa gyalen jallabiyan data cire sannan ta fita, suka jera Ita da habib.
Har wajan da motocin Yarima suke suka nufa, yau yazo da fadawa motoci har biyar kaman yanda Ya saba zuwa da, tun daka nesa Yarima ya gane Zainab ce ke tawo wa, amma ganin kayan jikinta jallabiya sai yasa shi jin kishi domin a ganinshi bai kamata tasa jallabiya ba duk da komai nata a rufe yake, ido ya lumshe tare da fad’in yanzu Nasan haka aketa kallon mun ita,
Usman dake zaune kusa da Yarima yace Yadai naga kana ta Jan tsaki??
Yarima yace plz bamu waje zan kiraka ku gaisa inna Gama magana da ita…..
Usman dariya yayi sannan ya fita
Koda bariki ta karaso habib ya bud’e Mata motar sannan ya juya…..
Bariki shiga tayi idonta nakan Yarima shima idonshi na kanta, bayan ta shiga ta rufe motar……
A hankali Yarima ya furta my princess maiya sameki?? Mai yasa kikai kuka tell me plz mai yake damunki? Duk a tare ya jefo mata wannan tambayoyin….. Idonshi na kanta yana jiran amsa daka gareta……
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta fashe da kuka Sosai….
Yarima cikin tashin hankali ya janyota jikinshi tare da rungume ta, yana sauke ajiyan zuciya tare da shafa mata baya, a hankali ya fara magana my princess plz stop it kin San bana son kukanki, plz tell me Mai yake damunki????
Tana manne a jikinshi ta Fara magana Yarima kasan ina Sonka bazan iya juran rashin kaba koda na awa biyu bane, yau inata kiranka kaki d’auka, jiya na kira baka d’auka ba, na kara kira naji wayarka a kashe yau tunda safe naita kira kaki d’auka… Kuka taci gaba dayi lokaci d’aya kuma taci gaba da fad’in Yarima kasan ko kad’an Ina tare dakai bazan kula wani ba, yakamata ka yarda dani ka yarda da irin son da nake maka, yarima dan Allah karka kara fushin da inna kiraka zaka ki d’aukan min waya, koda zaka d’auka ka zageni dan Allah ka d’auka rashin jinka yana sani cikin wani hali n…… Kuka ne yaci karfinta Sosai wanda yasa dole tayi shuru
Yarima kasa magana yayi sai bayanta da yake shafa mata, jin sautin kukan nata har cikin kanshi yasa ya d’ago ta tare da kallon fuskanta da ya baci da kuka Sosai, murmushi Yarima yayi tare da fad’in Kinga kina ta zubar min da hawayenki, my princess plz ki daina I trust you sai yasa na dawo gareki and naje na sami Abba ya yarda ya bani izinin zuwa zance har mu fahimci juna manya su shiga, ya kuma nunamin yaji dad’i yanda na Fara neman izini sabanin mazan yanzu basa haka, yace ya yaba dani ya yarda da irin tarbiya na, duk da na fito gidan sarauta ban nuna iko ko sarauta ba wajan zuwa wajanshi, my princess Abba mutumin kirki ne, lallai na yarda iyayenki Sun baki tarbiya domin Abba yayi min magana na dattaku……. My princess I really love you, Ina miki son da nida kaina ina mamaki, jiya nayi fushi dake amma gaba d’aya na kasa sukuni, saida nazo na ganki na samu nutsuwa…… Ganin ta lumshe ido yasa ya kura ma fuskanta ido, ji yake kaman ya tafi da ita, yana Mata son da bai taba tunanin Zaima kowa irinshi shiba,