DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Dan Allah ki shirya kadaki Bari asan abinda yake faruwa musamu Mana a watse lafiya basai kin nuna musu Abbas yafasa aurenki ba ki nuna ko babushi Zaki iya rayuwarki ta walwala da farinki.

Da gangan ta fada hakan Dan Naj din ta shirya da farko qin yadda tayi sai daga baya ta saka kayan ta zauna bakin gado sbd zuciyarta data fara harbawa da sauri da sauri Kamar zata Fado ta Dan dafe kirjinta tana sauraron bugun zuciyarta daya sanyata lumshe fararen idanuwanta ta rufe tanajin kamarma hadda faduwar gaba.

Miqewa tayi ahankali takoma Palo inda hayaniyar baqin gidan take Anata fira
Tana fitowa dukkanin idanuwansu suka sake dawowa Kanta suna Yana baiwar kyawu da Allah yayiwa Naj din qamshin wani irin fitinannan turaren da ummanta ke Mata gyara dashi daya Gama Kama jikinta Dana kayanta tareda kayanta da aka turara ya gauraya palon cikin nutsuwa da farin ciki a fili hajjo tace”

Masha Allah, Allah na gode maka da ganin wannan Rana Allah kasawa aurensu albarka da farin ciki me dorewa.

Amin Hanifa ta amsa idanuwanta akan Naj da ko itama dasuka taso tun yarinta tare sukai rayuwa tare koyaushe tana yabawa.

Qarasowa tayi gefen Hanifan ta zauna tana duba wayarta hankali kwance ba damuwar komai su Kuma suka cigaba da sha’anin gabansu.


An daura Auren JALALUDDEEN MARSHAL ALFA da NAJMA ABDULLAHI BELA akan sadaki naira dubu dari cif Wanda duban jama’a suka shaidar cikin mamakin sauyi da aka samu ciki harda jama’ar su Abbas da yawa sun halarta sbd basusan cewan an fasaba duk da hakan dai kowa tanata fatan Allah yasanya alkhairi Wanda aketa bawa Marshal hannu Ana tayasa murna shidai bin kowa yake da mayun idanuwansa sai hannu dayake bawa manyan mutanen dasuke miqa Masa hannu Dan tayasa murnar aurenda Saida ya iso gurin yasan nasane.
Isowarsa gurin yasa mahaifinsa daketa dakon jiran isowarsa ya qaraso gabansa Yana kallonsa Kai tsaye yace”

Za’a daura auren Najma dakaine Ina roqon alfarman ka amince da hakan sbd wancan ya fasa adaidai lokacinda Babu wani mafita shiyasa a matsayinsa na mahaifinka Kuma itama Ina matsayin uba gareta na hadaku ta hanyar nema maka aurenta Ina fatan zakamin biyayya.

Fararen mayun idanuwansa ya zubawa Dad din kafin ya Dan sauke Kai cikin miskilar murya yace”

Ok Dad.

Hakan dayace yasa Dad din Jin wani irin sanyi da nutsuwa sbd yanata nazarin yanda zai fahimtar da jalal din hukuncin dasuka yanke Kai tsaye akansa batareda Jin shawararsa ko raayinsaba tunda ba yaro bane yanada iko da yancin zabarwa rayuwarsa abokiyar rayuwarsa da kansa duk da yasan karba Masa Marshal din yayi sbd yariga yazo gurin bazai iya komawaba yasa Dad din kunya Amma yanayinsa kawai ko Bai fadaba Dad yasan anyi Masa shigar sauri Dan kuwa Babu tsarin aure agabansa yanxu musamman da wannan din da za’a daura da ita Dan kuwa a yanda suke dinnan ba lallaiba ta kwantar Masa da Kai shikuma bayasa ran macen dake qarqashin ikonsa zatana Masa kallon qani ko wani Abu Dan kuwa shi mijin macen dazata bisa ne Amma tunda su dad din suka zaba auren dama agurinsu zata zauna so ba damuwarsa bane sosai aciki tunda shi bataredasu zai zaunaba a taqaice ma yaji bazai iya dogon zamaba komawa zaiyi.

Dan Haka Ana gama daurin aure akai gagarumin reception da akai liyafar alfarma shidai ko ruwa Bai Sha ba aka fara watsewa ya zame yayo gida kansa na ‘dan sarawa Dan Haka Koda ya iso gida Kai tsaye flat dinsa ya wuce ya zare babbar rigar jikinsa da hula da komaima ya cire ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi ta shower Yana sauke ajiyar zuciya.

Sai dayayi wanka yafito yaji ya Dan samu nutsuwa da saukin ciwon kan ya saka guntayen qananun Kaya yaje fridge yasha ruwa kadan yadawo yashige daki ya kwanta Yana kashe wayarsa cikin nutsuwa bacci ya daukesa.

Saida ‘yan daurin aure suka dawo kowa yaji da Wanda aka daura auren zallan mamakin al’amarin yasake yayata gidansu Naj da hayaniya saidai Kuma tunda dai ansamu andaura Mata auren ba’a fasaba gabaki dayaba a watse a banza yasa aketa sabuwar murna Allah yayi lokaci yayi tayi aure duk da wasu da yawa sun manta da banbancin shekarun sbd matsayinsa da yanayinsa yasama har wainda suka kusan haihuwarsa suna basa tsananin girma sbd matsayi da kamewa shiyasama ake mantawa da wani banbancin shekaru sai murna sukewa umma Allah yabasu Wanda yafi abundama suke buri tako Ina.

Dadah kuwa Banda sadaka da godiyar Allah tana washe bakin babu abinda takeyi yau Jin takeyi wani irin sakat daga ita har Dattijo da sai baza babbar riga yakeyi Yana gaisawa da manyan mutanenda yasan Albarkacin auren Naj da jalal ne yakeci Dan kuwa ganinsu Koda appointment ne shi bazai samuba Dan Haka sai farin ciki yakeyi Yana baje babbar rigarsa ta tsadaddiyar shaddar da Alhaji Alfan ne yake dinka Masa daman.

Yana dawowa gidan yakira Naj a waya yace maza tadawo gida yanzu.

Da mamaki ta fito zuciyarta ba Dadi sbd dai ga dukkan alamun data gani agun mutane andaura auren kenan
Ta hadiye wani Abu me daci da nauyi daga maqogoranta Dan kuwa auren Abbas shine mafi mumman al’amari daya sameta a wannan rayuwar.

Ko data shiga gidansu sama sama takejin Ana mata adduar Allah yawa aure albarka Saikuma tafarajin Ana Kiran sunan Jalal da cewan mijinta
Kanta ne taji ya dauka ciwo sbd komaima ita yanzu a duhu yake Mata Kai tsaye dakin Dadah ta Isa sbd tasan Dattijo daya aika kiranta Yana can tana Isa tashiga da siriryar sallama ta nufi gefen Dadah daketa washe Baki cikin farin ciki ta zauna ahankali tareda bude Baki cikin taushin muryarta tace”

Barka da jumaa Dattijo.

Gaida Dadah tayi itama duk da dazun sun gaisa data shigo.

Kallonta Dattijo yayi dakyau yana Dan kame fuska yace”

To Najma Kamar dai yanda Kika sani yau ne ranar daurin aurenki da Abbas
Amma sbd rubutowa ta ubangiji Allah baiyi shine mijin ba Dan kuwa a jiya suka sanarda sun janye sbd abindaya faru a jiyan da safe.

‘dan shiru yayi kafin yacigaba da cewa”
Sakamakon hakan yasa Babanki Alhaji Alfa da hajjo suka bayyanarda buqatarsu tason nemawa JALAL aurenki muka amince atake sbd Babu wani zabin kokuma mafita Daman cigaban dayafi hakan Dan Haka dai a taqaice andaura Miki aure da JALAL yanzu ke matarsace halak malak saidai Hajjo ta nema alfarmar kada a takuraki da maganar tarewa gurinsa kokuma wani abun yanzu duba da yanda akai auren Dan Haka Zaki zauna gurinta kafin daga baya idan an natsa Kya koma sashen mijinki kokuma ki bisa can qasar dayake.

Akaro na farko a rayuwarta data kafe Dattijon da ido idanuwan nayi jajir ko qyaftawa batayi zuciyarta ta tsananta dokawa har batasan lokacinda ta bude bakiba tace”

JALAL qanin Hanifa?
An daura auren kokuwa dai za’a daurane yanzu??

Gano inda ta dosa da Aniyar bijirewa auren yasa ya tsuke fuska cikin bori yace”

Andaura Kuma wallahi kibar maganar Nan dakikeson fada acikinki Dan kuwa kisani kikaje Kika dagawa bayin Allahn Nan hankali akan banzan tunaninki na girman Kai suka raba auren Nan dake da mahaifiyarki zaku bar gidan Nan Dan kuwa Banga amfanin rashin godiyar Allah ba,
Dukkanin masu fasa aurenki Babu Wanda yakaisa bare yafisa ba’a ma hadawa ga qauna da mutunci da mahaifinsa da kakarsa dama ‘yar uwarsa dasuke Miki har kin Isa kice bakyason auren,
To kiji da kyau Dadah kizama shaida wlh taqi auren Nan bani ba ita Kuma Tak banyarda tasake cewaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button