DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Inada aikin Yi Zan tafi Anjima dai nasan zamuyi magana idan kayi lokacina.” Ta juya ta fice.

Baibita da kalloba sbd yawan kallo ba dabi’arsa bace ya Dan kalli dad da fararen idanuwansa shima dad din shi ya kalla kafin ya nuna Masa kayan dake ajen da hannu Yana cewa”

As you know yau akwai taron daurin aure So ansamu matsala anfasa daurawa da wancan din saidai za’a daura da Wanda na Isa dashi ga Kaya Nan su babban rigane kayi amfani dashi anjiman sbd mutane zasu taro akwai kuma media you’ll more comfortable in it tunda daurin aure ne na hausawa.

Kallon kayan yayi kafin ya kalli dad din Kai tsaye yace”

Thank you.

Gingina masa Kai Dad din yayi Yana cewa”

Ok then see you.

Tashi dad din yayi ya nufi kofa marshal din na bayansa har harabar gidan kafin ya juya zai wuce saiga Hannah Wanda ta fito daga sashensu hajjo data sakawa ranta zuwa gaishesu kowace safiya da Rana da yamma sbd sake samun damar kame zuciyar Marshal tana ganinsa ta qaraso gurinsa tana sake wani irin qayataccen murmushi jikinta sanye da wata doguwar straight English gown ta roba data Dan lafe a jikinta kyakkwan shape dinta a bayyane.

Good morning Marshal” tafada tana tsayuwa agabansa.

Dan kallonta yayi tareda dauke Kai Yana kallon hanyar sashen hajjo da Hanifa ta fito ta koma cikin sauri tana waya da alama dai gabaki daya tama manta da ita din ba wata lafiyayya bace take irin wannan kaida kawon sbd hidiman bikin Naj din.

Juyawa yayi ya wuce Yana cewa Hannah din”

I will talk to you later zankoma bacci yanzu.

Daukeda murmushi a fuskarta tace”

Ok love” tana bin bayansa da kallo Kamar zuciyarta zata narke gabaki daya akansa,
Tana yiwa marshal so me tsanani Dan ita ba Shirin aure gabanta a da Amma yanzu sbd shi aure takeso Kai tsaye ba Jan lokaci shiyasa zata dage da Binsu hajjo ko zata samu a saka ranar bikin nasu tunda ansan da maganar auren nasu.

Alhmdlh Koda Naj ta tashi safiyar lafiya kalau ta tashi kamar koyaushe data Saba tanada qarfin zuciya Kuma tasaba da hakan tunda ba yanzu ne hakan ta taba faruwa da itaba Dan Haka dataga Suma su Hanifa da hajjo dasuke damuwa koyaushe maganar aurenta ta fasu taga wannan karon Suma Basu nuna damuwaba saima farin ciki dasuke da hakan yasa ta qara cire abin a ranta tayi wankanta ta fito sanye da riga da skirt na atampa Maroon data yiwa kalar fatarta kyau tazo palo ta zauna gefen hajjo daketa faman waya tasha ruwan dumi da Zuma da Madara ta koshi ta tashi taje ta dauko qaramin gyale ta yafa kanta ta fito tareda wayarta a hannu tana kunnawa ta nufi gidansu bayan ta biya gurin mum Malika ta gaidata Dad baya Nan jama’arsa nata isowa so baya gida.

Ko data Shiga gidansu Haka ta ringa Dan gaggaisawa da mutane harta Isa dakin Dadah da yau farin cikin duniya tana cikinsa bakinta Sam baya rufuwa sbd farin ciki danma Dattijo ya kwabeta akan kada ta fadawa kowa komai sai sunsamu an daura auren lafiya sunga aure ya dauru tukuna Dan Haka Babu Wanda yasan da maganar bayan ummanta da Dattijon yafadawa yau bayan sallar asuba aikuwa gari na wayewa sadaka me yawa umman ta Tara almajirai tayi tareda duqufa da adduar auren ya dauru taga ya dauru itama Dan har lokacin daga ita har Dattijo gabansu Bai daina faduwaba sai sunga anshafa fatiha aure ya dauru.

Kodata Isa can cikin gida gurin ummanta dasu anty Amina sai hidima akeyi sai hakan yaso Bata mamakinsu saidai Tai musu uzurin basusan Babu maganar aurenba sai anjima idan lokacin daurawan yayi sunji ansanar anfasa Dan Haka batai wani yunqurin maganar da kowannensuba Dan dama ba halinta bane yawan maganganu musamman irin wannan Dan Haka dakinta ta shige tana hada sauran kayayyakin lefen Abbas dake dakin Dan tasan maida Masa za’ayi Allah yasa ko takarmi daya Bata sakaba a kayansa duk aurenta idan za’ayi hajjo ke hada Mata lefe na musamman sbd gudun irin Hakan.

Har qarfe daya da rabi tana gidan inda tana gamawa Kai tsaye ta fice Takoma bayan tabar musu kayan shirye tsaf a tsakar dakin ta fito tana waya da Sarah Dake sanar da ita gatanan a Hanya tana zuwa.

A waje Babu kowa maza tsit duk an tafi gurin daurin auren da za’ayi dama a babban masallacin juma’ar da Alhaji Alfan ya Gina acan farkon layinsu jami’an tsaro da securities kuwa koina cikin layin akwaisu
Sojojin Marshal ne a kofar gida tsatsaye jikin motarsu da alama jiran fitowarta sukeyi ta wuce Kai tsaye ta shige gate suna bude Mata da sauri
Ahankali tace” thank you” tana wucewa hankalinta a waya.
Tana saka Kai a palon hajjo Yana fitowa sanye cikin wata navyblue hilton filtex da rawar da yakeyi kawai zai bayyana kudi me yawa ya lashe
Sai hular daya saka wadda ke nuna Bai Saba sakawaba Dan yanda ya sakatan ta Dan Yi gefe Amma sai hakan yayi wani irin yiwa kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani irin qyalli na kwarjini da cika ido ta dauke idanuwanta akansa tana rabewa ya kalli Dan qaramin siririn gyalen dake kanta Wanda iyakacinsa kafadunta ya dauke kai Yana wucewa sbd lokacin daurin auren yayi saura mintuna basufi goma sha uku ba ita Kuma tana shigowa tsakiyar palon hajjo da wasu baqinta da Basu Dade da isowaba sukabi Naj din da idanuwa gabaki dayansu.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107
[1/14, 3:34 PM] +234 901 771 2720: DM 12
Ganin duka idanuwansu akanta yasa ta sauke idanuwanta tareda qarasowa a natsenta cikin taushin murya da rashin karauniya tace”

Ina wuninku Baabah barka da zuwa.

Sake Mata kyallon qiri qiri su baabar keyi wato yanne da qannen mahaifiyarsu Jalal dinne suka qaraso yau sbd tun a Daren jiyan hajjo da Alhaji Alfa suka sanar dasu auren jalal din daya Kama na gaggawa saidai Ba’a sanar dasu yanda akai auren ya yiyuba dakuma girmarsa datai sbd idan ba’a fadaba zakacema ta girmenta sosai Sosai sbd yanayin jikinta datake me kyau da burgewa da nasa jikin daya bude sosai sbd exercise dakuma tsayi daya fita sosai Dan Haka cikeda yabawa suke kallonta fatarta na daukan musu ido sbd zallan gyalan dilka da wasu abubuwan da akaita Bata tana Sha Dana mulkawa.
Baabah tace”

Lafiya kalau alhmdlh,ya hidimar kike ‘yar Nan? Ya hidimar jama’a?
Allah ya Sanya alkhairi kinji,
Allah yayiwa wannan auren naku albarka.

Da sauke Kai tayi shiru batareda tace Amin din ba tunda tasan abinda yake Nan ba aure.

Hanifa dake daki tagama shiryawa cikin Ado na shigar alfarma tana qamshi sbd mijinta da tuni ya iso suna gurin daurin auren
Fitowa tayi takama hannun Naj sukai dakin tana cewa”

Naj zo ki sauya shirinki inasa ran yanzu kowane lokaci za’a daura auren
Zo kiyi ado A ranar farko mijinki ya ganki da ado na musamman.

Zama kan sofa dake dakin Naj tayi tana aje wayarta da kallon Hanifa cikin Dan basarwa tace”

Nasan kinsan anfasa auren Nan just drop your drama.

Murmushi me girma Hanifa tasaki tana cirowa Naj din wani tsadadden navyblue lace me tsananin taushi da rashin ado na hayaniya Wanda yaja kudi sosai gurin siya tareda wani transparent emboidery veil ta aje gabanta tana cewa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button